A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Binaif yace, “me kika zo yi mana? Kinzo kisa yarinya ta ta firgita ne ko?”

Kallan sa tayi da ranta da baci tace, “Dan zo Naga yarinyar da Baka fada min ba ko? Sai da ka fadawa duniya karewa ma sai da ta kwana sannan Ubanka ya fada min haushin da naji shine naki zuwa suna sai yau uban Ka ya kaga dama shima ya kawo ni”.

Inni ce ta sauko tace, “Umma kece kika zo ashe kuma shine suka barki a bakin kofa kina ta tsaye tun dazu aka ce gaki nan sai yanzu Kenan Kara so Umma”.

Umma tace, “Alhamdulillahi sai yanzu na samu sirika ‘yar arziki ai Bari na suka yi a tsaye ina ya rafka sallama amma a banza suna nan suna faman guje guje da danyen jego”.

Murmushi kawai Inni tayi ta amsa jakar hannun ta tare da kama hannun ta tama ta wuri ta zauna ita kuma ta zauna a dan nesa da ita.

Tace, “Amma Inni anan zaki kwana tunda Baki zo da wuri ba”.

Sude tashi sukayi Baya sun gaida ta suka hau Sama Binaif kuwa ko kallan ta be kara yi ba, Ummusalma ta kalli Ummu.

Tace, “wai ina su yusseer ne kusan Sati fa Kenan”.

Ummu da gowa tayi ta kalle ta sannan ta sunkuyar da kanta.

Tace, “imm sun tafi fa wannan Kaduna wurin shiyasa kika ji su shiru”.

Murmushin geden baki tayi tace, “ki Ramin su kice suzo nan dan 20 minutes”.

Binaif yace, “Baki me tace bane ba suna Kaduna”.

Bata kalle Shi bama bare yasa ran amsa ta ummu kawai take kallo ita kuma ummu taki kallan su tana kallan pretty.

Tace, “Kin Kira su ko kuwa?”

Wayar ta ta karba a hannun uncle sannan ta Kira su
Yusuf yace, “Hello ykk ya pretty”.

“Lafiya qalau take zaku zo yau?”

“Ehh zamu zo Insha Allah”.

“Kuzo yanzu”.

“To shikenan gamu nan zuwa”.

Kashe wayar tayi taki kallan kowa Ummusalma kuwa kallan ta kawai har ya Gama.

Tace, “meke faruwa”.

Cikin sanyin murya tace, “Abba ne beda lafiya kuma sunce Kar na fada wa kowa shiyasa kiyi hakuri”.

Bata ce komai ba ta kyale ta, Jin pretty ta fara kuka yasa ta dauko ta ta kawo mata ita Bata fara yi tana kallan ta.

Mas’ud yace, “saikin koya Mata kiwa ko? Kike wani kallan ta wai ke Uwar ta”.

Harara ta Galla masa tace, “ina ruwan ka tunda Kai ba dauka zaka yi ba sai kayi shiru”.

“Danna fada maki?”

“Bana so”.

“Masifaffiya”.

Banza tayi dashi ita kadai tasan halin da take ciki dan babu wata alama da ta nuna hakan. Basu wani Dade ba sai gasu nan sun zo da sallama suka shigo wani kallo da ta musu yasa su tsaya wa a bakin kofa Basu Kara ba sun rigada sun san halin ta tun kuwa suna yara sun jima basu ga wannan bacin ran dake tattare da ita ba, Binaif ta mikawa ‘yar ta tashi kowa kallan ta yake tana zuwa batayi aune ba ta kifa wa yusuf mari.

Yaseer yace, “ya…”

Shima nasan raban ya samu tana cigaba da kallan su, Dafe kunci sukayi suka sunkuyar da Kai”.

Cikin tsananin bata rai tace, “Abban ku Kenan ba Abban Ummun ne ita Daya ko? Baza Ku iya fadan cewan Abba beda lafiya ba ko? Sai kawar Ku da Zama dolen Ku ko? Okay ko Dan abun da ya min ne yasa aka ki fada min”.

dagowa Yusuf yayi yace, “dalilin Kenan yaya kiyi hakuri”.

“To najima da yafe masa abinda ya min Ida ma shine saime kuma?”

Yaseer dagowa yayi ya kalle ta yace, “Anya yaya kina da zuciya kuwa? Anya zuciyar ki tana aiki? Kinsan me kike kuwa? Kin ma jima wato da yafe masa”.

Wani banzan kallo ta wurga musu tayi tafiyar ta ya wuce daki tayi kwanciyar ta tana maida numfashi ta jima a haka Binaif ne ya shigo ya rufe kofar ya zauna a kusa da ita.

Yace, “meyasa kika yi haka?”

“To su abinda sukayi yayi daidai Kenan Yusuf fa yaseer? Me zamu boye wa juna? Just because of …”

Hade bakin su da yayi yasa ta tayi shiru bata Kara ba, Sai da ya nemi wuce gona da iri sannan suka sarara ya kwanta akan ta Yana sauke numfashi shafa kansa tayi ta fara yi sai da ya dawo normal.

Yace, “yaushe zamu koma ne wai nifa nagaji sati biyu fa ai ba wasa ba nayi kokari ko dan hug din nan ba min ba kike”.

“Hmmm”.

“Daya Kenan”.

“Uhm hum”.

“Biyu”.

“Wai meye kake wani kirga abu”.

“Babu komai kawai ina ga de rashin ki a kusa ni ya fara yasawa kin manta ni ne Amma bakomai karki damu Zan fanshe”.

“To kayi hakuri”.

“Meyasa aka Sawa pretty zulaihat”.

“Kawai insan suna nan ne sosai da sosai shiyasa tun ina karama kuwa”.

Murmushi kawai yayi ya rabo da ita badan ya gamsu ba sai Dan besan bata moment din su Yana Jin dadin haka.

Ana gobe bikin su ta shirya tsab suka fita ita dasu Neena da Ummu.

BY: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????

????A BAKIN WAWA????
Akanji magana

 60

Basu dauki mota ba haka suka tafi direct gidan Maman Sadiq suka nufa.

Tayi mamakin ganin su ba kadan musamman Neena da taje suna bata ganta bata ga Inni ba da yake Sunan yayi jama’a kuma da wuri ya dawo sosai suka sha hira, suna cikin hira Ummusalma ta dauki pretty tace tana zuwa.

Gidan kusa da Maman Sadiq ta kwankwasa shiru babu amsa kara Knocking tayi namma babu amsa sai da tayi da Dan karfi sannan taji anyi magana, ita kuwa matar gidan gani tayi tunda wannan din nan ya tafi shikenan babu Wanda ya kuma zuwa sai Shi kuma idan zaizo waya yake mata ta bude ya bata abinda zai bata ya tafi.
Shiru tayi har aka zo aka bude.

Tace, “sannu da zuwa shigo”.

Dan murmushi tayi sannan ta shigo a waje ta zauna ganin tabarma da kayan wanki da’alama wanki take itama Zama tayi suka gaisa sannan matar.

Tace, “kawo yarinyar muganta”.

Mika Mata ta ita tayi pretty kuwa idan ta ras a bude take kallan ta itama kallan ta take yi tare da sa Hannu cikin nata babu abinda take hango wa game da yarinyar sai kamar ta da Binaif sanda Yana jariri kwalla taji ta taru a idan ta tana kallan yarinyar tana Mata murmushi da gowa tayi ta kalli Ummusalma dake kallan su.

Tace, “ya sunan ta?”

Murmushi Ummusalma tayi tace, “zulaihat”.

Fadada murmushin tayi sosai tace, “kice itiyi nace”.

“Itiyi kuma?”

Murmushi tayi dakyau tace, “takwara ta nake nufi”.

Itama murmushi tayi tana cigaba da kallan yarinyar sai anan hawayen ya digo daga idan ta tasa hannu ta share tana maida sauran zubowa.

Ummusalma tace, “Mama lafiya?”

“Bakomai kawai ina tuna yaro na ne”.

“Ayyyaahhhh sorry, shima Karami ne?”

“Sanda na tafi na barshi Karami ne amma yanzu nasan ya girma dakyar ma idan beyi aure ba”.

“Kamar ya Kenan? Kin tafi kin barshi fa kika ce Yana karami mekenan?”

“Amma daga ina kike?”

“Gida nan makwabciyar ki nazo shine nake tambayar ta ta taba Shiga tace bata taba ba tana de Jin motsin mutum a ciki shine kawai nace Bari nazo”.

“Ya sunan ki?”

“Ummusalma tace”.

“Suna mai dadi”.

Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta irin kunyar nan sai kuma ta dago.

Tace, “amma Mama meyasa kika bar yaran ki Tou”.

“Labari ne Mai tsayi babu kuma Wanda yasan da wannan daga ni sai Hafsa sai kuma kawar ta”.

“Wacece Hafsa?”

“Kishiya ta ce”.

Irin mamakin nan tace, “kishiyar ki kuma? Shine zata raba ki da yaran ki tun yana Karami?”

“Kamar yarda nace maki labari mai tsayi”.

“Amma mama baza ki iya Mai dashi gajere ba? Ina San nasani ko Zan iya taima maki”.

“Salma kenan bansan taya Zan Baki labarin ba ban kuma san ya zaki dauki abin ba zurfi ciki na ne ko kuma San yaro na ne ya rufe min Ido bansani ba”.

Hawayen ne ya zubo mata ta goge shi, Ummusalma tace, “Mama kome zaki fada min Zan fahim ce ki sosai”.

Tsab ta kwashe komai ta fada duk da ta sani amma bata katse ta ba har barin cikin ta da tayi har samun wani cikin da komawan Rukayya gidan ta anan tayi shiru haweye na zuba a idan ta da’alama ta tuna abu mafi girma shiyasa ta zubar hawaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button