NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

ya juya mata baya ya sanya tayi saurin saka dunkule d’aya na turaran a cikin wutar ta tsuguna akai haya’kin na ratsa jikinta, kusan minti biyar tayi a haka sannan ta mike da sauri ta gyara towel din jikinta wanda yay dai-dai da mikewarsa zaune yana kallon inda take, da sauri ta bude wardrobe ta dauki riga da wando na bacci ta saka a jikinta ta gyara gashinta sosai ta saka hula mai wani irin ado a gabanta, turare ta fesa sosai a jikinta, ta nufi bed din,
Ta dan tsaya kansa, kamshin jikinta na fuzgarshi, kamar wani bugagge yake kallonta da lumsassun idanunsa, a hankali tace”Zan kwanta.” Cigaba yay da kallonta ya kasa cewa komai.” Ta sake maimaita maganarta nan ma be ce mata komai ba, sai kawai ta haye bed din tana dan turo bakinta, bargo taja ta rufe kafafunta dashi, Ya sauke ajiyar zuciya me zafin gaske, a hankali ya mi’ke ya fita daga dakin, ta’be bakinta tayi tace”Zaka gama salau! salau! d’in naka ka dawo ka bada kai, idan laifi ne ai bani kadai ce mai lefi har da kai dan haka duk sai mu taru mu bawa junanmu hakuri.”
Ta dauka, ba zai dawo dakin ba sai ta saki jikinta sosai bacci na kokarin daukarta taji alamun shigowarsa dakin yana kulle kofa, ta dan kalleshi ta ganshi cikin wasu pyjamas sky blue ‘kirjinsa a waje dan be daure igiyar gaban rigar ba
Tsigar jikinta ta mi’ke da sauri ta mai da idanunta ta rufe tana takure jikinta gabanta kuma na d’an fad’uwa kad’an!
Ya jima kafin taji ya hayo bed din yana jan bargon jikinta……Sai kawai ta sakar mishi bargon dik ya janye ya rufe jikinsa dashi har da kanshi, shuru dakin yay na tsayin minti goma, ta bude idanunta a hankali sai taga dakin yay duhu, alamun ya kashe fitila, ta dan juyo a hankali tana kallonshi taga yanda ya wani takure jikinsa cikin bargo har da rufe kanshi, yau bai bada tazara mai tsayi ba a tsakaninsu, juyawa tayi a hankali ta dan dora hannunta kan babynta dake gabanta tana sauke ajiyar zuciya, Can wayarshi ta soma ringing, firgigit ta mi’ke zaune tana kallonsa ko zai tashi ya dauki wayar, taga ko motsi yaki yi, gashi sai kiran wayar ake.
A hankali tace”Ana kiran wayarka.” Shuru yay mata sai da ta sake magana tukkuna yace.”Ki dauka ki kashe wayar wannan halin da nake ci yasa na manta ban kashe wayar ba.”
Murya a harhard’e yake magana.”
Ta dan rankwafa ta jikinsa ta dauki wayar tana dubawa taga Zeey ce.

Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262alliya:
‘Yr Bngr Sys
81
Wani matsiyacin tsaki taja me karfi ganin sunan Zeey kan screen din wayar, tuni ranta yay wani mugun ‘baci taji zuciyarta na wani irin tafarfasa tamkar zata tsaga kirjinta ta fito waje haka takeji, hannunta na karkarwa ta datse kiran tana kara jan wani tsaki!! idanunta har sun kada sunyi jawur ranta bai ta’ba ‘baci ba irin yau! Wai me matar nan take nufi ne? Jin tana ta jan tsaki ya sanya ya bud’e fuskarshi yana kallonta,tana rike da wayar tashi a hannunta sai dubawa takeyi.
Shuru yay mata dan shima jikinshi ya bashi Zeey din ce dama dai-dai wannan lokacin take kiran wayarsa shi abin ma mamaki yake bashi sam bata da zuciya ko kadan yana jin ko aure zaiyi ba zai aureta ba dan shi yafi son ya auri mace wacce tasan ciwon kanta ba me bibiyar maza da kanta ba.
Zeey Sarkin ‘yan naci aikuwa sai ta sake kira second guda bata ‘kara ba ta d’aga wayar a fusace! murya a sama tace”Ke! mahaukaciya idan kina cin ‘kasa to ki kiyayi ta shuri wallahi! saboda rashin kamun kai da iskanci da wulakanci zaki dinga kiran waya duk daran duniya kina damun mutane? wallahi to duk sanda kika sake kiran me wayar nan sai nazo har inda kike naci miki uwa! ni Wasilatu ‘Yar gaske! na wuce da tunaninki bana d’aukar rainin hankali! idan auranki zaiyi yaje ya aureki ban hanaba amma kada ki kuskura na sake ganin kin kirashi a waya lokacin da yake cikin gidanshi, duk sanda kika kuskura kika sake kiran wayarsa a dai-dai wannan lokacin sai na dauki tsatstsauran mataki a kanki wallahi.”! A fusace! take maganar tana wani irin huci jikinta na kyarma tamkar wacce tasha tsumin ‘yan bori sai faman hura hanci take…….Mi’kewa yay zaune da sauri yana ‘kokarin fizge wayarsa, ta mike da sauri ta bar gurin tana cigaba da sauraran maganar da Zeey ke mata.”
“Ke har wata abace da zaki ce zaki dauki mataki akaina to mu zuba ni dake shege kafasa aure kuma nida governor kamar anyi an gama sai dai ki mutu dan babban mutum mai ‘kima da mu’kami gami da mutunci bai cancanci! ya zama miji a gareki ba.” A fusace! tace”Da Uwarki ya cancanta.”! Zeey ta mike zaune da sauri tana mamaki! kafin ma ta dawo daga cikin mamakinta taji muryar Wasila na fad’in “Nace da Uwarki ya cancanta!? Shegiya dabba! wacce ta rasa mashinshini! tana bin mazan mutane a waje, zan nuna miki isa da mu’kamina a gurin shi wanda kike ganin ban isa na zama mata gareshi ba, zakiji da kyau wallahi zai za’ba a tsakaninmu ni ko ke! shashasha! mahaukaciya kawai.”! Tana karashe maganarta ta kashe wayar tare da fashewa da wani irin kukan ba’kin ciki da takaici.
Ya jima kanshi a ‘kasa ransa yayi masifar ‘baci! ashe dama yarinyar nan ba tayi hankali ba wannan ai shashanci da rashin hankali da zata tsaya tana gundume gudunmen ashar da wata ransa ya sake ‘baci sosai da abinda tayi dan duk a ganinsa laifin ba na kowa bane nata ne tunda be ce ta daga waya ba cewa yay ta kashe masa waya…….A d’an kausashe yace.” Kiyi min shuru kada ki tasar min da yarinya daga bacci.”! Cikin ‘kuluwa da tsabar bakin ciki ta kalleshi, tace”Sai me! idan ta tashi ai laifin ba na kowa bane naka ne ni wallahi tallahi nagaji nagaji! ana cutata kuma ace ba zanyi magana ba kawai ka za’ba ni ko wannan ‘yar iskar mahaukaciyar matar dake kiranka a waya.”
Cikin tsananin bacin rai yace.”Ranki zaiyi mutukar ‘baci idan kika sake yi min irin wannan maganar kece zaki tsara min abinda nayi niyya idan nace Zeey na za’ba me Za kiyi.!?
Aikuwa sai ta fusata sosai idanunta ya rufe shaf ta manta waye a gabanta ta dinga zazzaga masa rashin kunya da fad’in “To same? dan ka za’bi Zeey ka ajiyeni dama ai hausawa suna cewa duk wanda yaci moriyar ganga zai yada koranta dama ai nasan tuntuni bani kake so abinda ke jikina kake so, dan haka ko sakina ma kayi ni bazan damu ba dan nasan Allah yayi min baiwar da in na rabu da kai in auri wanda yafi ka komai da komai na rayuwa sai me? dama dole akayi min me zanyi da tsoho! (me saisayayyan kai Inji Nafeest Lol????) ta cigaba da cewa ” ai dama kai d’in kwata kwata ba’asan aurena bane dama da Zeey din kafi dacewa.” Kallonta yake wani irin gumi na tsiyaya a jikinsa, tunda yake ba’a ta’ba ci masa fuska irin y

au ba, wannan yarinyar shi takewa rashin mutunci da d’ibar albarka? wai shin ma duk me ya jawo hakane? tambayar kansa da kansa yake da yaga bashi da amsa ga wani irin ciwo da kansa ke masa sai kawai ya mike zai fita daga d’akin! tayi gaggawar tarar gabanta tana kuka da fad’in “Sai ka sakeni tunda kace ka za’bi Zeey dani wallahi na gama zama da kai dama baka cancanta dani ba.”! Cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da rud’ani! ya kifa mata mariku masu tsakanin shiga jiki, ta zube akasan dakin tana rirrike kafafunshi ihu! take sosai wanda ya tashi su Hajja daga bacci duk sukayo waje cikin tsananin tashin hankali da damuwa.
Kafarsa yake janyewa tana sake ri’kewa duk tabi ta cikwiye masa a jikinsa
Ga wani irin jiri da ciwon kai na nema su zautar dashi.
Hajja ta dinga buga kofar d’akin tana fad’in ” Innalilhi wa’ina ilaihi raji’un jama’a meke faruwa ne? Amadu Wasila ku bude kofar mana komai yayi tsanani maganinsa Allah.”
Jin muryar Hajja ya sanya Wasila tayi zumbur ta mike tsaye, saboda yanayin kwarin jikinsa har sai da ta tureshi ta bude kofa a guje ta fita daga dakin ta rungume Hajja tana wani irin kuka da shashsheka! “Hajja! nagaji da wannan zaman nagaji kullum sai ya dokeni ya sani kuka kullum cikin ‘kuntata min yake baya kulani baya sakar min fuska nayi masa lefi na bashi hakuri yaki hakura, kullum sai muna kwance budurwa zata kirashi a waya suyi ta hira kuma a gabana bashi da lokacina ko magana nake masa baya saurarata, yanzu da bakinsa yace” Ya za’bi budurwarsa a kaina, dama nasan haka zata iya faruwa tunda dani da iyayena duk be dauke mu da mahimanci ba sabida muna talakawa, dama budurwarsa tace ni bancancani da na zama matarsa ba dan haka ni kawai ya sauwa’ke min na huta da wannan zaman.”!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button