NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ya jima yana kiran sunan Allah kafin yayi gaggawar bud’e motar ya fito ruwa na dukanshi, Can ya hango motar su Mada! ta silalo gurin…….Ya tsaya yana kallon motar har tayi parking kafin ya ankara yaga sun fito su uku ko wanne fuskarshi rufe da ba’kin abu, dake namijin duniya ne bai wani razana ba sosai! suka durfafo inda yake! Mada ya fito da wata bindiga yana saita shi da fad’in”Kud’i ko kuma mu dauki ranka.”! Yace.”Ai babu mai daukar ran mutum sai wanda ya halliceshi! Lauje ya kai wa bakinshi duka da sauri ya rike hannunsa yana girgiza masa kai! Yace.”Kuce kawai na baku kudi sune bukatar ku amma kada ka kuskura ka ta’ba min lafiyata.”

Zuruf! ta bud’e motar ta fito, sai ta fashe da kuka tana wata makyarkyata sosai tsoro takeji gani takeyi anya su Mada! ne kuwa, ganin sun saita shi da bindiga yasa gabanta faduwa ta shiga kuka tana basu hakuri.”

Da sauri Lauje yaje ya bud’e motar ya hau dube dube a ciki a take ya bude wani gurin cikin motar ya fito da daurarrun kudi a hannushi, ya dinga jefewa ! ‘Kwage! yana cafewa! Wasila ta isa inda yake a hankali tace”Lauje.” Yace.’Yar gaske maxa ki fece daga nan.” Data tabbatar da sune sai kawai ta silala ta bayan motar zata gudu, tana waigowa ta hangi Ahamdu da Mada suna kokawa! saboda tsabar tsaurin ido irin na Mada so yake ya lalube jikin Ahmadu, ya dauke masa wayoyinsa shi kuma ya hanashi, Sai kawai taga Mada! ya daddage! ya sakar mishi duka a ‘kirji! Ihu! tayi da ‘karfin gaske! wanda ya sanya shi saurin juyowa, yana goge ruwan fuskarshi, dan har lokacin ruwa ake me ‘karfi! Can ya hangota tana ‘kwarma! ihu zata tsallaka titi! Yayi nufin binta, Mada! ya tad’e kafafunsa, santsin gurin ya sanya ya zube ‘Kas! cikin zafin nama ya rike kafafun shi shima ya makar dashi a gurin! a gaggauce! ya mike! da azama! ya murd’e? hannunsa ya ‘kwace! bindigar dake hannunsa! ya saita wuyanshi……
Mada! ya hau ‘kif’kifta ido! Yana kare fuskarsa da hannunsa!….A kausashe yace.”Waye! ya aiko ku.”? Mada! yayi shiru yana yi wa ‘Kwage! Inkiya da idanunshi, Kwage! ya lalla’bo ta bayan Ahamdu ya kir’ba mata wani irin duka! Ahamdu yayi taga taga zai fad’i! da sauri Mada ya tureshi ya mike a guje! sukayi inda motar su take suka shiga, Ahamdu ya saita bindigar hannunsa zai harbesu wayam! babu bullet sai da ya duba ta sosai sannan ya gane ashe ta gaibu ce! Can ya d’ago kanshi ya hangi motarsu ta fice daga layin……
Wata irin walkiya akayi mai hasken gaske! Walkiyar da ta zame masa madubi gurun hango Wasila tana kurd’awa wata hanya tanayi tana waiwayen bayanta, Da sauri ya nufi motarshi ya shige ya kunna da gudu yabi hanyar da bi, Ganin hasken mota yasa ta juya da saurin tana waigen bayanta, bata tantance cewar shine ko bashi bane, ta juyo da sauri tana cigaba da sauri aikuwa facal? ta fad’a cikin wata kwatuwar kwata mai zurfi! Kuka tasa tana kiran sunan Allah! ganin ruwa ya shanyeta har yuwanta shikkenan mutuwa tazo, sai kawai ta dinga kwarma ihu! tana fad’in”Azo acece ni! Azo! aceceni!” Jin wannan sautin ya sanya As dake cikin motarshi a can gaba ya fito a gaggauce! ya durfafi inda yake jiyo sautin muryartata, To shima Ahmadu hankalinshi ne yayi masifar tashi, dan gani yayi ma kamar motar bata guda ya bude ya fito ya soma gudu yana so ya cimma inda yake jin ihunta!
Had’uwa sukayi da As! d’in, sai suka shiga kallon kallon, Ga Wasila tsakiyar kwalbati ruwa na neman tafiya da ita dan ma ta rike wani karfe ne da tuni ruwan yayi gaba da ita!
Ahmadu na gane Waye baiyi wata-wata ba ya kir’ba! masa wani irin naushi a ‘kirji! As ya ri’ke kirjinsa yana tari! Ahamdu ya sake kir’ba mishi wani naushin da yafi na farko! As ya zube a gurin yana jawo numfashi da ‘kya!!! Facal! facal! d’in da yaji a cikin ruwan ne ya sanya ya dawo da hankanlinsa nan ya hangota tana d’ad’dago kanta sama! da hannunta guda! Da sauri ya afka cikin ruwan, dan har sai da yayi motsi saboda yawan ruwan da ya taru ! Daukota yayi a kafad’a ya daddafo ya fito yana kwantar da ita, ta sume a gurin……

A hankali a tashe ya ciro wayarshi da ruwa ya jika jagab! baiyi tunanin idan yay kira da wayar zatayi ba saboda yanda take digar ruwa, amma abin mamaki yana fara kiran yaga tana shiga ajiyar zuciya ya sauke, Stion ya kira yay musu bayanin komai da kuma kwatancan garun! Ya mai da wayar jikinshi bayan ya gama, inda take yazo ya tsuguna ya fara danna ‘kirjinta a hankali a hankali ruwa ya dinfa fita ta bakinta da hancinta kafin wani ruwa yayi fit ya fito ta hancinta ta bude idonta a razane! ta mike tana zazzare! idonta! Ganinshi tsugune gabanta ya sanya ta fashe da kuka jikinta ya soma karkarwa shikkenan kashinta ya bushe! Bai ce mata komai ba, Ya mike tsaye tare da goya hannuwansa a bayansa ya nufi inda As ke sheme!!! Yana tsaye a kanshi yana nazarin shi motar Police ta shigo gurin…..suka fito su kusan biyar suna haske gurin da torchlight din hannuwansu, Ganin Sananniyar fuskar Ahamdu ya sanya su mamaki! sosai gaisawa sukayi yace.”Yanzu babu lokacin bayani ku daukeshi kawai ku wuce dashi stion da safe zan shigo.” Suna haska fuskar As suka razana! Ganin sanannaniyar fuskarsa Ahamdu yace.”Kuyi abinda nace kawai.”Sanin halin Ahamdun da rashin wasa ya sanya suka bi umarinsa, bayan haka kuma dama sun gaji da mulkin Lawan Rabo baya basu albashi kan kari babu promotion da sauransu wasu daga cikin ma’aikatansu ma duk ya koresu daga aiki acewarsa wai basa aiki shiyasa ya sallamesu, dama suna ciki dashi da masu bashi shawara, irin su As din dan haka suka ga su baza su ‘ki bin Umarnin Ahmadun ba, suka fito da wani gadon karfe cikin motarsu suka dora As a kai suka haura dashi motar, kana sukayi wa Ahamdun sallama suka bar gurin.

Ya juyo inda take takure kanta tsakanin kafafunta tsananin razana da fargaba ya sanya jikinta maxari sai kace wacce aka kad’awa gangi tsoro nadama gami da dana sani duk sun baibayeta yanzu da badan Ahmadu ba da tuni ruwa ya cinyeta! hakika fadawarta cikin ramin kwatar yasa ta sare ta sadakar da cewa mutuwa zatayi sai gashi wanda take ‘kokarin gujewa shine ya ceceta, wata irin nadama takeyi sai kuka takeyi ma’kogwaronta ya bushe ‘kamas!!! Taga inuwarshi a kanta, Idanunta jage jage da hawaye ta d’ago tana kallonsa, ganin fuskarsa a daure ya sake fad’ar mata da gaba, kawai sai taji wani masifaffan fitsari ya matsota! Cikin ba’kin ciki da takaici ya buga mata tsawa “Tashi mu tafi.”!!! Gurin sai da ya amsa da sautin muryarahi, Ta mike jikinta sai kyarma! yake tana d’igar da ruwa duk tabi ta ‘kankame! hannuwanta a jikinta, ya nuna mata hanya da hannunsa,

Tana cire ‘kafa da niyar tafiya fitsarin dake cinta ya kufce! sakin sa tayi kawai ta cigaba da tafiya tana kyarma! Bayanta yabi hannuwansa goye a bayansa yana jajanta al’amarin.

Gaban mota ta bude za ta shiga yace.” Rufe min mota.” Da sauri ta rufe! ta bude murfin baya ta shiga ta zauna tana kuka da nadamar rayuwarta…. ya shiga a gaggauce ya Kunna motar suka bar gurin.

Gwajab! gwajab! din da motar takeyi ne yasa As dawowa hayyacinsa ya mike zaune a zabure! yana fad’in’ Karya kakeyi Ahmadu! Ba zan jima ina shuka ba ranar girbi tazo kace ban isa inyi ba, Wallahi sai ka saki yarinyar nan ko ni ko kai, a fad’in garin nan.””!! Daya daga cikin police din yace.”Yallabai yi a hankali shin wai meke faruwa ne tsakaninka da Ahmadu Musa.” As yayi saurin dawowa hayyacinsa yana bin motar da kallo sai ya ganshi tare da ‘yan sanda, gabanshi ya fad’i! Yace.”Kai ina zaku kaini.”!? “Yallabai Ahmadu ne ya kiramu a waya ya shaida mana muzo gurin nan domin mu dauke ka mu kai ka stion mu rufe.” Ya buga musu tsawa da fad’in”Ina ce dai bai fad’a muku abunda ke tsakaninmu ba.”? Dan sandan yace.”bai fada mana komai ba, amma kuma ga yanayin maganganun da kakeyi munso mu fahimci wani abun.” As yaji gabanshi ya yanke ya fad’i! A duniya ya tsani mutuncinsa ya zube gurin mutanan gari da kuma iyalinshi, yanzu idan Ahamdu ya sanar da Media cewar yayi nufin daukar matarshi me duniya da mutanan cikinta zasu daukeshi, sai kawai gumi ya soma yanko masa daga ko wace kusurwa ta jikinshi, Yace.”Maza ku saukeni a gida Ahmadu bai da hurumin daureni domin bai da wani mu’kami a siyance idan dauri ne ma nine zanyi masa.” Babban cikinsu yace.”Sam! ba haka dokar aiki take ba ku da kanku kuke fad’in cewar ba mayin aiki tsakani da Allah bama bin doka dan haka babu wani karin albashi da za’ayi mana, saboda haka daga yau zamu fara aiki tsakani da Allah a kanka.” As ya shiga rarraba ido yana kallonsu ma’kogwaronshi ya bushe kamas! yace.”Kunfi kowa sanin mukami na a siyasa me zai sanya kuyi min haka ku fad’i ko nawa kuke so zan baku ku kaini gidana kuma bana so kowa yaji wannan maganar.” Mai maganar cikinsu yace.”Yallabai alamu sun nuna mana kaine mara gaskiya tsakanin ka da Ahmadu, saboda haka dole ne muje stion dake domin yin aikinmu kamar dai yanda na fad’a maka da farko cewar kuna fad’in bama aiki kan ‘ka’ida shine zamu fara ta kanka.” As yayi kwata’kes! yana zazzare ido cikin motar………….
Tofaaa! Karshen tika tiki tik! ‘Karya fure take bata ‘yaya! Tsalle d’aya za kayi ka fad’a rijiya sai kayi dubu baka fito ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button