NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Kika futar min da book Ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whadap numbar
07084653262

BINTA UMAR ABBALE‘Yr Bngr Sys
24
Mikewa yayi cikin kasala da rashin kuzari ya nufi bedroom din, nan ya ganta tsaye gaban wardrobe dinsa tana masa bunkice, Tsawa ya buga mata “Me kika ajiye min a cikin kaya kike bunkita min.”!? Yanayin yanda taga fuskarsa a murtuke yasa tasha jinin jikinta, Yayi mata wani irin karjini a ido, ‘kas tayi da kanta tace” Kaya nake dubawa.” Yana hararata yace.”Ke kika ajiye a kayan a gurun da zaki hargitsa min.”? Shiru tayi masa, ya nufi wardorbe din sai tayi saurin matsawa daga gurin, a duk sanda zai tunkari inda take wata iriyar shakka ce take kamata, yana dubewa ya ciro mata wata jallabiyar sa mai faffadan wuya da hannu zurmemiya yace.”Karbi kisa wannan nayi wanka yanzu na fita domin sanin abinyi.” Yanda yayi maganar ba alamun wasa a tare dashi yasa ta karbi rigar….Ya juya ya nufi toilet… Rigar take bi da kallo tana tunanin yanda za’ayi ta saka rigar nan katuwa tsayin ta yayi mata yawa fad’inta ma haka ga wuyan kurmame, haka dai ta hakura tasa rigar duk domin tayi sallolin dake kanta….Lifayar ta ta nada a jikinta ta hau kan dadduma ta tayar da sallah.

Ya fito daure da towel iya kungunsa sai wani karami a hannunsa yana gogo kanshi…Kai tsaye mirror dinshi ya nufa ya fara shafa mai a jikinsa ya sanya turaran jiki kana ya gyara sajensa dama bai fiye barin suma ba a kanshi dai-dai misali ya taje ya gyara ta sannan ya shirya jikinsa cikin yadin kufta brawon d’inki hannu ne wanda aka bata lokaci gurin dinka shi yayi kyau mutuka mafi akasarin kayanshi ya dika ne masu kyau da tsada! Hula ya sanya ya daura agogo kana ya hau kan kafet din dake kusa da ita ya tayar da sallah.

Ganin ta idar da tata sallar ne yasa ta mike daga gurin can bakin bed ta zauna tana saka wasikar jaki! Har ya idar da sallahr shi yayi adduao insa bata sani ba sai alamun bude kofarsa ne ya dawo da ita hayyacinsa, Ga yanayin alamun da taga ni a tattare dashi ta gane futa zaiyi sai ta mike da azama tabi bayansa.

Yana tsaye tsakiyar palo suna magana da Garba, Ganin fitowarsa ya sanya ya sallami Garban ya kalleta babu cikakkiyar walwala a tare dashi…….”Don Allah ka bani waya ta da sim card dina kaji.”! Tafada tana marairaice fuska.

Tsaki yaja ya kama hanyar fita, Tace”To dan girman Allah ka bani aron wayarka na kira kanwata nasan gidanmu hankalinsu na atashe mussaman mamanmu.” Ya dan tsaya yana kallona na minti biyu karamar Wayar sa ya ciro daga aljihu Ta iske inda yake da sauri ta karba har tana hadawa da hannunsa,

Numbar Camas! ta fara kira wayar nata ringing bata dauka ba Yace.”Ke! bani wayata bana son ‘bata lokaci.” da sauri tace”Dan tsaya na kira daya layin na gani.” Tsaki yaja ya fice daga palon….Ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta zauna kan kujera ta sanya numbar Camas! test ta tura mata kamar haka.

Camas! Ina cikin masifa da tashin hankali da ukuba yanzu haka ina gidan Ahamadu Musa babu iya ka wai yaje can garin su mahaifina ya nemi aurena kawu malam mai allo ya bashi aurena da sadaki dubu biyar, Kiyi kokarin ki samo min mafita Camas! kaina ina cikin masifa Tana gama rubuta test din ta tura mata ta goge numbar da test din dan kar ya gani……Ta kira Rashida itama tana ringing bata dauka ba da sauri ta shiga kiran wayar Uwani is swich Up! Tsaki taja tayi shuru can ta yanke shawara Numbar As ta sanya a wayar ta soma kiran shi aikuwa kamar jira yake yi ya daga wayar, ta sauke ajiyar zuciya da sauri ta nufi dakin tana fad’in”As ‘Yar gaske ce! Daga daya bangaran As yace.”My love ina kika shiga munanan hankalinmu a tashe mahaifiyarki da kanwarki sun shiga damuwa yanzu haka ma duk muna tare dasu da Camas kawarki.

Kuka ta fashe masa dashi tace”As Ina gidan Ahamdu Musa a halin yanzu…….Tiryan tiryan! ta shiga warware masa abunda ke da akwai! As ya shiga tsananin tashin hankali da bakin kishi Ahamdu Musa ne yayi masa wannan wulakancin? ya za’ayi ya jima yana rainon abu ace lokaci guda wani yazo ya lalata masa shiri!! Yace.” Wallahi karya yake mu zaiyi wa wannan wulakancin wato ta in da ya bullo kenan to ki kwantar da hankali kuma ki tsaya kai da fata kan a’kidar ki duk rintsi kar ki sauka daga ra’ayin ki ni nasan saboda wata manufa tashi ya sanya ya aure ki ba wai dan sha’awa ko wani abu makamancin haka ba, domin tuntunin nasan wannan mutumin bashi da lafiya tamkar mata maza yake babu wani abu da zai iya a kanki, duk da haka dai ki kiyaye zamu dauki kwakkwaran mataki a kansa, sai ya sake ki komai abunsa wato ya gano kina da muhimanci a tafiyarmu shine zai dauke mana ke to daga nan government house zan nufa domin mu san abinyi.”

A hankali tace”Nima zargin da nake yi kenan ya aureni domin ya rusa tafiyarku ganin ina da muhimanci a tare daku shiyasa ya ‘bullo ta wannan hanyar As kuyi da gaske na lura da gaske yake dan Duk ya tara ma’aikatan gidansa a aikana yace su sanya idonsu a kaina gidanshi tamkar kurkuku yake ko ina a rufe babu ta inda zan taimaki kaina.” Jin wannan maganar tasa As ya sake zabura! Yace.”Aikuwa duk yanda zamuyi ki fito daga cikin gidanan zamuyi kar ki damu.”
“Shikkenan As ina saurare dan Allah ku taim…….! maganar ta katse lokacin da ta ganshi a gabanta, bakinta ne ya soma kyarma!! ” Ra….shi..d ki cewa…U….! Hannu ya mika mata alamun ta bashi wayar…..Dai-dai da lokacin da As yake cewa”My love kina ji na ko? ki kwantar da hankali ki saki jikinsa dashi ki nuna masa komai ba komai bane ta kanki zamu shirya plan dinmu a kansa ai ya janyowa kansa tabbas ajalinsa na kusa.”
Ahamadu najin muryar As din tar! dake saboda rashin dubara hands free ta bude ko kuma dai ta manta ne oho!!! Jajayen idonsa ya ware mata Hannu ya sake mika mata a karo na biyu!!! Ta mika masa wayar jikinta sanyi kalau….Wayar ya kara a kunnansa, Har yanzu As nata surutu da fad’in”My love kina jina kuwa kinyi shiru, karki wani damu da wannan abun zamu dauki ‘kwakkwaran mataki a kansa.” Kashe wayar yayi ya tsira mata rikirkitattun idanunsa…..”Waye kika ce min zaki kira.”!? Yafada yana kallonta cike da tuhuma…..”Rashida c…..! Kafin ta karasa ya bata wani lafiyayyan mari! Ihu! ta kurma! ta haye kan bed ta tsaya hannunta dafe da kuncinta……A zabure! yace.”Ni zaki rainawa hankali ko? Waye wannan da kika kira har yake kiran ki da masoyiyarsa.”!…..Cike da rashin gaskiya tace”Kanwata ce Rash…..Bed din ya haye! ta manne jikinta jikin bango tana kare fuskarta,Wuyanta ya dam’ka! da karfi ya shake mata magogwaro yana mata kamshin mutuwa! Ta dinga ‘kifta ido tana kakari idanunsa sun gwalalo sunyi jawur had’e da tara ruwa…..Lokacin duk wani tausayi da imani nasa babu so yake ya kashe ta, babu abunda idan ya tuna yake sake dugunzuma masa zuciya sai muryar gardin mutumin dake kiranta da Masoyiyarsa (My love) ba za’ayi haka dashi ba gwara kawai ya kasheta ya huta tun kafin ta tarwatsa masa zuciya…….Idanunta ne suka soma lumshewa jikinta ya soma shikawa luuuuuu! tayo jikinsa……Ya sake ta ta fadi kan bed din Ta suma! daukar ta yayi ya kai ta can bakin toilet ya ajiye ya bude firji ya dauko shegen ruwa mai sanyi kai tsaye ita ya nufa ya hau tuttula mata a fuska da jiki! Ta bude ido a zabure! tana a tishawa, cigaba yayi da zuba mata ruwan sanyin a jikinta, cikin rashin tausayi…….Saboda rashin kwarin jiki yasa ta koma ta kwanta jikinta yayi lakwas! sai makyarkyata takeyi tana jin saukar ruwan sanyin a jikinta amma ta kasa motsawa sai wasu irin hawaye ne masu zafi dake ziraro mata…..Sai da ya juye mata babban gora na ruwan swan kana ya jefe ta da goran ruwan ya sanya kai ya fice daga dakin ranshi ba’ki’kkirin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button