NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Suna zaune kan katuwar tabarma shida abokanansa gabansu katon farantin silba ne jere da kwanuka, da jug jug na ruwa da alama abinci suke shirin ci ya hangosu, Sai ya shiga wasiwasi da tunani to sai da suka iso inda suke ya tabbatar da cewa su d’in ne Yace.”Uwani ko ba ita bace.”? Tace.”Nice Kawu.”! Sai ya washe bakinsa yana fad’in “Kece kike tafe da ranar nan babu shakka yau an tuna damu kenan gaki ga zuriarki lallai yau patskum nada manya ‘baki sannuku da zuwa.” Mi’kewa yay yana ‘kwalawa yaran dake wasan langa langa a ‘kofar gidanshi kira…..Suka rugu a guje yace.”Maza ku kwashi kayan nan ku shida dasu gida…..Yaran suka dinga ihu! suna fad’in “Yeeee! munyi ‘baki daga birni da gudu suka runtuma cikin gidan suna jan akwatinan kayan nasu


Can ya hango yaron da aka tura gidan ya fito daga wata hanya yaji tamkar yaje ya tareshi ya tambayeshi, sai dai kawai ya daure ya bi yaron da kallo har ya isa inda mai allo yake ya tsuguna yana masa magana.” mai allo ya Umarceshi da ya koma gurin zamanshi kana ya mike daga kan kujerarshi Ya nufo inda yake tsaye babu yabo babu fallasa a tare dashi, tun kafin ya karasa inda Ahamdun yake ya hango damuwa da tashin hankali a tare dashi, sosai ya shiga mamaki yana tunanin to bayan rabuwarsu ya mayar da ita ne har ta samu cikin ko kuma bayan ta fito daga gidan cikin ya bayyana ? babu me bashi amsa sai su ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya karasa inda yake a nutse yace.”Alhaji mu shiga ciki sai muyi maganar.” Ga yanayin yanda mai allo ke masa magana yasa ya fahimci akwai damuwa, jikinsa babu kuzari ya juya yana tafiya me allo ya bi bayanshi.
Mai allo ya zauna kan tabarma yana kallon Ahamdu A nutse ya soma magana kamar haka
“Yau shekaru takwas kenan rabon da Wasila da ‘yar uwarta Rashida su tako ‘kafarsu garinan! shiyasa nayi mamaki mutuka! a lokacin da kuka zo min da wannan maganar, amma kuma banyi muku musu ba saboda nasan hakan zata iya kasancewa tunda muma kullum cikin tunanin zuwansu muke nasan duk tsiya yarinyar bata da wasu iyaye sai mu, kuma nasan dole watarana zata kawo kanta inda muke duk kuwa da tsananin ‘kiyayyar da suke mana ita da ‘yar uwarta……Ni da ‘Yan uwana da sauran dangi kullum cikin saurare muke da kallon hanya muna jiran tsammanin zuwansu garinan, tun bayan rabuwar auranka da ita muka yanke shawara kancewa mun dauke hannunmu da kansu gabakid’aya wanda har ‘Dan uwana Habibu da ya fusata yace. Duk ranar da suka shigo garinan to sai ya koresu ni ne na hanashi nace mutukar sunzo inda muke to zamu kar’be su hannu biyu amma idan basu nemi in da muke ba to zamu kyalesu da halinsu da kuma mahaifiyarsu, to a gaskiya ni nafi gazgata zaton cewar Yaran nan sun bi bayan mahaifiyarsu can garinsu.” Mai allo ya ‘karashe maganarshi yana so ya tabbatar musu da gaskiyar lamari……Khalifa ne kawai ya iya magana Yace. “Allah shi gafarta malam ko zamu iya sanin garin su mahaifiyar tasu.”? Mai allo yayi shiru yana d’an tunani kafin yace.” Wallahi sunan garin ya kwanta min a raina, tun da kasan can d’in ba nan ne inda cibiyar mahaifinta yake ba, shi kanshi ‘kanina Yahuza a hannun Kawunta ya aureta amma dai na ta’ba ji sau d’aya ‘kanin nawa ya ambaci sunan garin har yace watarana zai daukeni ya kaini mu gaisa da danginta to kuma sai Allah ya dauki abinshi.

Khalifa da gogan naku bakinsu ya mutu murus! Saboda dukaninsu sun rasa tudun dafawa sun ma rasa wane tunani zasuyi shin yanzu ina zasu samu yaran nan? Su dun tunaninsu babu inda suka dashi sai nan dan suna tunanin itama Uwanin a nan take ashe ba haka bane! Gashi gurin wanda suke tunanin samun cikkaken bayani shima yace bai ma sannan sunan garin da suka nufa ba……..Innalilihi wa’ina ilaihi raji’un!

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[14/08, 12:04 pm] Farida Books: ‘Yr Bngr Sys
58
Cike da farin ciki da walwala ya shiga gidan nashi yana kwalawa matarshi kira……….Kuluwa ta fito daga wani guri wanda alamu suka nuna cewar madafi ne (khicin) hannunta da wata katuwar mara da alama kwasar towo take, tace”Malam ganin nan Allah yasa lafiya irin wannan kira hak…..Kafin ta rufe bakinta sai idanunta ya sauka kansu Uwani da ‘yayanta, lokacin ‘kan’kani ta kirne fuska tana fad’in “A’a yau kuma Uwani ce a garin.”? Uwani dasu Wasila duk sunga sauyin fuska a tare da ita, lokacin da take maganar da alama dai batayi maraba da zuwan su garin ba…….Kawu Madu yana washe hakoransa yace.” Wallahi kau nima nayi mamaki sosai dan baki ji dadin da nakeji ba, abinci zamuci dasu malam tsalha na taso domun in shigo dasu gidan.” Kuluwa tace”To sannunku da zuwa ku shigo ciki.” Kawu Madu yace.”Uwani ku shiga ciki a baku abinci ku huta ai da alama ma kun kwaso rana.” Uwani tace”Aikuwa wallahi munsha zaman mota da gajiya.” Kawu Madu ya juya ya fita yana fad’in “Bari nasa Ayuba yaje can cikin kasuwa ya siyo muku ruwan sanyi.”

Uwani da Rashida suka shiga daukan jakkunansu dake yashe a tsakar gidan suka nufi dakin Kuluwa, suna shiga katuwar rumfa ce sai dai babu shinfida a cikinta sai guntattakin tabarmi da ledoji ko ina kaca kaci da kwari ka ‘kananin kyankyasai ga wani uban ‘kuda da yake tashi a rumfar da wani kafirin zarnin fitsarin yara……Tun lokacin da suka shiga rumfar Wasila ke yatsine ya tsinen fuska zuciya sai masifar tashi takeyi aikuwa kafin tayi wani yun’kuri amai ya kece mata! a guje! tayi waje ta nemi bakin rariya ta tsuguna ta dinga kelayashi tana kwallah……Rashida ce tsaye a kanta tana mata sannu duk ta shiga damuwa. Bayan ta gama aman ta bata ruwa ta wanke bakinta da fuskarta kana ta mike jiri na d’ibarta……Rashida ta rike hannunta wai su koma cikin d’akin girgiza kanta tayi da kyar tace”Rashida rabu dani don Allah zuciya tashi takeyi idan na koma gurin nan zan iya yin wani aman.” Aikuwa karaf a kunnan Kuluwa ta rike baki tana fad’in “Ke ja’ira yarinyar me kike nufi? daga zuwa zaki fara yiwa mutane sanabe da iyayi kina nufin kazama ce ni kome.” Rashida tayi saurin girgiza kanta tana fad’in “Ba haka take nufi ba baba.” Kuluwa tace”To me take nufi da har zata shiga dakina ta rugu waje da gudu tana kwara amai.” Rashida tace “bata da lafiya ne dama tun a mota cikin ta ke ciwo.” Kuluwa ta girgiza kanta tana fad’in “Maji ma gani dai idan tusa zata hura wuta, kome kuke tafe dashi dai-dai nake daku to kaji.”! Tana gama maganar ta ta shige madafi domin cigaba da aikinta.

Uwani na cikin dakin abin duniya yayi mata yawa, tunani takeyi yanzu wace irin rayuwa zasuyi cikin gidanan! tun da can baya tasan Kuluwa macace mara mutunci da muguwar kaxanta sam bata so kowa yazo inda take tabi ta asirce Kawu Madu sai abinda tace yayi yake ji shima wani lokacin tsoranta yake yi, Ta dinga tunanin irin wuyar da zasu sha ita da ‘yayanta a gidan dan ga dukanin alamu Kuluwa ba tayi maraba da zuwansu ba, tunani take ko su tafi gidan Kawu Isa ne? sai ta tuno shi kuma ai bai da gidan kanshi haya yake kuma daki guda ne suke gamutsuwa dashi da matarshi da ‘yayanshi…..Iya mai waina kuma ba ita kadai bace a gidanta tana da kishiyoyi kuma babu wadataccen gurin zama, dole dai gidan Kawu Madu din shine gurin zamansu, Kwallace ta taru a kwarmin idanunta tayi saurin gogewa, lokaci guda duniya ta juya musu baya, sun fara d’and’anar jin dadin rayuwa kuma sun koma gidan jiya…………Sai a lokacin nadama mara amfani ta kamata ta dinga tunanin abubuwan da suka dinga faruwa a baya da irin kud’ad’en da ‘yarta ta rike da samun nasarar auran Ahamdu tayi, Yanzu ne ta gane auran Ahamdu da ‘yarta shine rufin asirinsu tasan da Wasilan na gidanshi har yanzu da tuni basu shiga wannan gararanbar ba.
Kuluwa ta shigo dakin hannunta rike da wata katuwar langa tana kallon Uwani tace”Naga kamar kema kina cikin alhini da damuwa to Allah yasa dai ba abin kunya kukayi a can ba kuka gudo nan dan naga alamun ciki a tattare da waccan ‘yar taki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button