NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whsap numbar
07084653262alliya:
‘Yr Bngr Sys
62
Rashida ce ta shiga dakin ta tsaya kanta tana kiran sunanta, “Anti Wasila dan Allah ki daina kuka ni wallahi banga abin kuka da damuwa anan ba,Allah na yarda da nadamar mutumin nan yanzu kuma yana sonki dan da baya sonki ba zai tayar da hankalinshi a kanki ba, kawai ki hakura ki koma dakin ki shine mutuncinki damu gabakid’aya.” Idanunta jaga-jaga da hawaye ta dago tana kallon ‘yar uwar tata dake durkushe kusa da ita, “Rashida nifa bazan koma yanzu ba sai na haihu haka kurrum kai tsaye zaizi yace ya mai dani sai kuma na kwashi jiki na bishi babu wani shiri da da yanxu ba d’aya bane yanzu nasan ciwon kaina.” Rashida tace”Eh gaskiya kuma hakane to da zai bari ki haihu shikkenan yafi sauki hakan amma yanzu ku kin koma nasan hankalinsu mai allo ba zai kwanta ba.

To a can tsakar gida kuma sai fafatawa ake tsakanin mai allo da Ahamdu da kuma Hajjah inda mai allo ya kafe kai da fata yace Wasila ba zata koma ba sai ta haihu sannan Ahamdu da Hajjah sai rarrashinsa suke da kawo masa misalai wanda suke nuni da cewar in ta koma d’in ai babu matsala insha Allah zasu kula da ita da kyau dan har hajja tayi al’kawarin zama tare da ita har sai ta haihu tayi ar’bain tukkuna sannan ta tafi gidanta, Malam mai allo yayi shiru yana nazarin maganarsu, shi dai hankalinsa yafi kwanciya da zaman yarinyar a gabanshi to amma bashi da yanda zaiyi dole ya hakura ya basu tinda yanzu suke iko da ita, Yana mutukar ganin girman hajja sabida matar tasan abinda takeyi sosai…..Yace.”To shikkenan ai tunda kun rinjayeni na bar muku amma kuyi hakuri ku barmin rashida dan naji kana cewa tare zaku tafi da ita.” Ahmadu ya marairaice sosai yana rarrashin mai allo kan yay hakuri ya basu har rashidan zamanta tare da ‘yar uwarta zai d’ebe mata kewa sosai mai allo dai sun gama kashe mata jiki sai kawai ya amince musu amma kam zai sha kewa dan d’an zaman da sukayi dasu na watanni uku sun saba da juna sun sha’ku sosai.

Bitan na kicin ta kwalawa rashida kira ta fito da sauri ta nufi kicin……Bitan ta kammala abinci tsat tsaf ta jera kwanukan silba kan wani katon faranti shima na silba sai she’ki yake kwanuka uku ne akai d’aya lafiyayyan towon farar shinkafa ne tas dashi a nad’e cikin leda d’aya miyar taushe ce da taji gyada da alayyahu da yakuwa, d’aya kwanon kuma farfesun naman zabbi ne sai kamshi yake yayi shar shar dashi, tace”Dauki ki kai musu sai kizo ki dauki wancan jug din ki kai musu ruwa.” Rashida ta dauki abincin ta fita.
Mai allo ya mi’ke ya bar gurin domin su samu sakewa suci abincin a nutse Ahamdu ya saki jikinshi yaci abincin sosai irin wanda ya Jima baici irinshi ba, hakika ya yarda da kula da tsabtar matar shiyasa ya zage sosai ya cika cikinshi

Rashida kam na daki na rarrashin Wasila suci abinci ta’ki hawaye kawai take! tarasa abinda yake damunta, mai allo ya d’aga labulen dakin yana fad’in “Ina Wasila.”? Da sauri ta goge hawayen ta tace” Gani Kawu, Yace.”Kiyi hakuri kinji ko kiyi hakuri ki kyautata hakuri a karo na biyu na umarce ki da kiyi biyayya kibi abinda nace miki insha Allah zaki samu alkairi a gaba, bani na fad’a ba Allah ne ya hukunta hakan! duk macen da mijinta ya saketa saki d’aya kafin ta ‘kare iddah mijinta ya dawo yace ya janye sakin ma’ana ya mayar da ita ko bata so dole ta koma ta cigaba da zama dashi a matsayin mijinta, dan haka nake sake baki hakuri nake kuma ro’konki da kibi mijinki ki koma d’akin ki insha Allahu za kiji dad’i kuma kiyi alfahari anan gaba.” Mai allo ya gama kashe mata jikinta da maganganunsa shiru tayi tana tsiyayar da hawaye mai allo ya saki labulen dakin zai tafi tace”Kawu ina da magana.” Ya dawo da baya yana kallonta……Tace”Kafin na koma to ina so muje can pataskum gurin Uwani kaga tunda muka zo ba muje saboda yanayin rashin lafiyana ba kuma musan halin da take ciki ba.”

Mai allo yayi shiru yana nazarin maganarta ta Yace.”To babu laifi sai kuje domun ki shaida mata abinda yake faruwa, yana da kyau a fita hakkinta a matsayinta na mahaifiyarki tasan halin da ake ciki, bari na sanar da Alhajin abinda ke faruwa.” Labulen dakin ya saki ya nufi inda suke zaune Sun gama cin abinc

i suna hira mutumin ya saki jikinsa sosai dan har ya kira Khalifa a waya ya shaida masa abinda ke faruwa…..Mai allo ya dan jingina jikin bango a nutse yace.”Anya Alhaji tafiyar nan zata yiwu yau kuwa.”? Yayi saurin kallonshi yana so yaji dalilin da zai hana yiwuwar tafiyar……Mai allo yace.”Yarinyar nan na bukatar ganawa da mahaifiyarta hakan nada kyau sosai mahaifiyarta tasan halin da ake ciki ta kuma sanya mata albarka, a zamantakewar auranta, dan haka nace ko zamu bari rana ita yau! insha Allah sai kadawo ka d’aukesu kafin sannan sunje sun dawo ta sake nutsuwa tukkuna.

‘Dan ‘bata fuska yayi yace.”A’a malam ina ganin rana d’aya ma zamu iya zuwa mu dawo
Ba tare da anja dogon lokaci ba, ni da kaina zan kai su su dubata insha Allah gobe zamu dawo tare da khalifa sai su shirya muje daga can sai mu wuce kawai.” Mai allo yace.”Babu laifi hakan Allah ya kaimu lafiya.” Hajjah tace “Amin amin ya rabbi mungode malam Ubangiji Allah ya kara girma da dattako.” Mai allo yace.”Babu komai hajiya mudai fatan anan shine Allah yasa anyi kenan Allah ya d’orar da zaman lafiya.”

Ya d’an gyara zamanshi as’usel kamar ko da yaushe dai ya ciro kudi masu yawa a jikinshi ya dora saman buzun mai allo yace.”Malam zamu koma Allah ya saka da alkairi.” mai allo yace.”Alhaji Ahmadu baka gajiya kullum cikin hidima kudin nan sunyi yawa.” Yace.”Babu komai malam Allah ya bamu mu bayar meye amfaninsu in ba’a badasu ba.” Mai allo yace.” To maddalah mungode kwarai Allah ya kara arziki da wadata.” Ya amsa da “ameen.” yana gyara babbar rigarshi.

Hajja ta le’ka d’akin su Wasila tana gyara lullu’binta tace”To Ina kuke zamu tafi Wasila kina ina.”? Wasila dake kwance kan kafita ta fara kokarin mikewa zaune Hajja ta shiga dakin tana fad’in “A’a yi kwanciyarki kinji ko sannu! Dan Allah kiyi hakuri karki sa damuwa cikin ranki insha Allahu abinda ya faru a baya bazai faru ba yanzu ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kuma ki daina kuka.” Kanta a kasa tace”Insha Allah Hajja nagode ki gaida gida.” Tace”Gida zaiji insha Allahu gobe inanan ina jiran zuwanku.” Shiru tayi tana mayar da ‘kwallar dake kokarin zubo mata……Hajja ta fito daga d’akin kawai sai ta ganshi ya ‘kurawa kofar dakin ido kamar zai shiga, kai kana kallonsa kasan a dame yake daurewa kawai yake yana kokarin dauke abin daga ranshi duk dan kar girmanshi ya zube a idon yarinyar da mutanan gida…..Hajja tace”To ko zakuyi sallama ne naga kanata kallon dakin….Girgiza kanshi yace “Tunda kunyi sallama babu damuwa ai gobe zamu had’u insha Allah.” Tace”To babu lefi.” Bitan ce ta fito daga daki hannunta rike da wata roba mai murfi mai kamar kwanon sha robar da fulani ke zuba nono a ciki, daya hannun nata kuma ledar fura ce a cure tace”Hajjah ga wannan babu yawa, tun zuwanku naso in dama muku ayyuka sunyi yawa.” Hajja ta kar’ba da walwala a tare da ita tace”To godiya muke Bitan Ubangiji Allah ya saka da alkairi kwarai naji dadin yanda kika kar’bemu hannun biyu mungode sosai.” Bitan tayi murmushi kawai tana fad’in “Babu komai hajiya mune da godiya ai ku gaishe da gida Allah sauke ku lafiya.” Hajja ta amsa da ameen kana tabi bayan Ahmadu da ya riga yayi gaba.” Suna tsaye da mai allo suna sallama, Garba dake zaune cikin mota ya fito suka gaisa da mai allon kana ya koma ya jingina jikin motar yana ganin tawowarshi ya hude mishi mota ya shiga Hajja ma shiga ta zauna da sauri ya zauna a maxauninshi , Ahmadu ya shiga dagawa mai allo shima yana daga mishi hannu gami da yi musu fatan sauka lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button