NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

“Masha Allah.” Yafada yana dan gyara zaman sa a nutse yace.”A wannan watan nake tunanin yi muku karin albashi, Insha Allahu.” Sai duk suka saki fuska suna dariya godiya suka shiga yi yace.”Kowa yaje ya rike aikinsa Allah ya taimaka.” Suka amsa da “Ameen Allah ya kara maka suttura da tsawon kwana insha Allahu sai ka zama governor domin kaine muke saka ran za kayi adalci ga talakawa.” Yace.”Ku cigaba da addua dai Allah ya za’ba abunda yafi alkairi.” ‘Insha Allah kaine alkairi a jahar kano.” Abinda suke ta fada kenan har suka bar palon.

Rabe ne ya fito daga wata ‘kofa dake cikin palon, da alama kicin ne domin naga anyiwa kofar ado da wani irin labule mai baza da kyalli hannunsa rike da wani faffadan tire na silba cike da kayan marmari irinsu inibi dabino kankana abarba lemo gwanda da sauraru an shiryasu tsaf gwanin ban sha’awa, wani dogon daining mai kujeru kusan takwas naga ya nufa ya aje tiren ya koma kicin nan ya soma fito da kayan kalaci ya jere tsaf! a danining din ya iso inda yake zaune yana duba jarida Leadership ta wannan satin….”Sir an shirya daining.” ba tare da ya d’ago ba yace.”Okey.” Rabe yace.”A tashi lafiya.” Hankalinsa na kan jaridar har Rabe ya fita…..Ya kai minti talatin a haka kafin ya aje Jaridar ya mike ya nufi bedroom dinshi….Idanunsa ya sauka a kanta tana kwance a bed dinshi ta kifa cikinta ma’ana tayi irin kwanciyar da ba’a so. ya karasa inda take ya tsaya yana kallon bayanta mussaman bom!bom dinta yana mutukar daukar hankalinsa, zama yayi gefenta ya sanya a hannu a hankali ya burkitota kwanciya ya gyara mata ya kama gashinta daya wargaje ya had’e guri guda hannunsa yasa ya tufke mata ya zuba wa fuskarta ido gani yayi ta dan fad’a kwarmin idonta ya zurma ciki akwai alamun gajiya da yunwa a tattare da ita gashi bacci ya dauke ta ko da yake shima baccin rahama ne…..’Kirjinta ya zubawa ido yana kallo…Yaji tsigar jikinshi ta mike tsayin shekarun da yayi babu mace bai ta’ba shiga mawuyacin hali ba sai tsakanin jiya da yau da jikinsa ke gogayya da nata, Ya mika hannu a hankali ya dan shafi saman lebunanta! ajiyar zuciya ya sauke! runkufawa yayi dai-dai fuskarta ya dora bakinsa kan nata le’bunanta ya lasa da harshensa yaji wani irin santsi, da sil’bi! yanda take sauke nuffashi ya sake kid’ima shi bai san sanda ya sake lasar lebanunan ba…Motsi tayi yayi saurin mikewa a gaggauce ya fita daga dakin yana sauke zazzafar ajiyar zuciya.

Baiyi wani cikakken karin kummalo ba ya bar daining din, Jikinsa duk ya mutu yana jin wata iriyar kasala ta dabaibaye shi, can palo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera Fargabar komawa dakin yake saboda shi kansa bai yarda da kansa ba sam baya so zuciya ta jashi ya afka mata bayan bai shirya hakan ba….Rintse idonsa yayi yana hasaso yanayin tsarin hallitunta da manya manyan d’uwaiwakanta a duniya yana bala’in son mace mai wad’annan abubuwan nono da d’uwawuka!! mace ko mummana ce a fuska baya ganin muninta mutukar dai tana da wannan had’in!! Ya dora romat din dake a hannunsa saman kirjinsa yana lumshe ido….Oh! duniya kenan wai shine yau yake jin sha’awar ‘ya mace ashe dai zai ga zuwan wannan rana.?


Rashida da Uwani dai sun soma shan jinin jikinsu hankalinsu yayi masifar tashi sosai mussaman da suka kira Camas! a waya ta tabbatar musu da cewar tun a daran jiya suka rabu da Wasilar tace ta tawo gida, Ta shaida musu cewar itama tun jiya da daddaran take kiran wayarta bata dauka ba, dazu da safe ma ta kira akace wayar a kashe take.

To jin wannan magana ta Camas! ta sanya hankalinsu ya tashi Uwani sai matsar kwalla take tana fadin”Allah yasa dai ba Magauta bane suka sace mata ‘yarta, Rashida ma da taga abun dai ba na wasa bane sai ta hau kuka duk jikinsu yayi sanyi sun san Wasila nada makiya sosai suna zargin ko daga cikinsu ne suka sace ta Allah ma yasa kar su kasheta, adduar da sukeyi kenan kuma basu fasa neman wayarta ba.


Wajejan karfe uku da rabi na rana ta farka daga baccin da ya dauketa, ta j idonta a bude kafin ta yunkura ta tashi zaune ji take jikinta tamkar anyi mata dan karan duka sai nu’kurkusa yake mata ga wata iriyar masifaffiyar gajiya data dabaibaye ta…..Salau! salau! ta mike ta nufi toilet…Ta hada ruwa mai dumi tayi wanka ta dauro alwala ta fito. jikinta daure da towel mai girma, kwata kwata bata sha’awar mayar da kayan jikinta ta zauna gefan bed din ranta a ‘bace! kawai an kawo mutum an ajiye bashi da sutturar sawa Hatta da pant da breziya ka’idar ta ce bata maimaitasu kullum sai ta sanja haka ta cure kayan da ta cire da lifayar da jins din da shart din da undis din guru guda ta ajiye ta fita palon kirjinta d’amare! da towel! Nan ta ganshi yana bacci kan kujera ya mike sam’bal hannunsa guda a saman kirinsa sai daya hannun kuma ya dora saman kanshi.

Cikin sigar ‘kuntatawa ta tsaya kanshi……”Ka tashi ka bani suturar da zan saka.” Wannan kalma ta dinga nanatawa gatsal! “Ka tashi ka bani sutturar da zan saka zanyi sallah lokaci na ‘kurewa.”! Ya dinga jin maganar a cikin bacci tamkar mai mafarki, sai kuma ya bude idonsa da sauri!! ita ya gani a kanshi….Yaji kansa yayi bala’in sarawa! ya tsani yana bacci a tashe shi!!! Ya mike cikin yanayi na ‘bacin rai yake kallonta……” Wai ke me yasa kike abu irin na dabbobi ne? bacci fa nakeyi zaki tsaya min aka kamar doki.”! Kwarai taji zafin maganarshi wato itace ma dabba……Itama cikin bacin rai tace”Akan na tashe ka ka bani sutturar da zan saka nayi ibadah kake kirana dabbah! meye laifina anan? ka dauko ni ka ajiye babu suttura babu ci babu sha dan nayi magana a zageni wallahi ka daina kirana da dabbah ki tinkiya domin ni ba ita bace.”!

Bai ce koma komai ba ya mik’e tsaye ta d’an ja gefe tana masa wani irin kallo…..’Ka’ida idan yana bacci aka tashe shi sai yayi ciwon kai da jiri dalili kenan da ya sanya yana mikewa ya tafi luuuuuuu! kamar zai fad’i! tayi saurin kaucewa! amma inaaa! sai da ya same ta ta fadi kan kujerar da ya tashi ya afko jikinta!!! Kanshi da fuskarsa tsakankanin ‘kirjinta ya kwanta luf dashi sai kace yaro.

Nauyi ne ya isheta ta ture fuskarsa tana turje jikinsa da kafafunta “Daga ni dan Allah.”! Tafada tana kumbura baki…..Can ‘kasan ma’koshi taji yace.” Sai jiri ya sakeni zan mike daga jikin ki ai kece sila waye yace ki tashe ni ina bacci sai kiyi hakuri har sai lokacin da na tashi.”

Tabd’ijam! kana nufin kaina zaka kwanta har sai sanda ka ga dama! Ni wallahi nauyin ka ya isheni ba zan iya daukar ka ba ka d’aga ni jikina ya soma tsami.”!!!! Tafada tana ture shi da fuskarsa dake kwance kan kirjinta duk ya matse mata nono.

‘Kara sakin jikinsa yayi sosai yana sake mikewa sosai a kanta, Wasila taga abun nasa kamar da zalinci sai ta soma kuka tana masa magiya ya daga ta da gaske nauyi ne dashi…..Yana jinta yayi mata shiru, tuntuni ya daina jin hajijiyar kawai tsabar taushin jikinta ne ya sanya ya manta da komai yayi kwanciyarsa kamar wanda yake kan katifa.

“Dan girman Allah ka d’aga ni wallahi zaka kassarani bani da ‘kwari! wayyo ruwan cikina da gwiwata duk sunyi laushi shikkenan jama’a zai ‘karasa n………Kafin ta ‘karasa maganar ta ya mika hannunsa ya datse mata baki!! duk da haka ba ta daina magana ba….Mikewa yayi daga jikinta still hannunsa na damtse da bakinta, Ta mike zaune da sauri towel din tuni ya sunce daga jikinta yayi nasa guri cinyoyinta da lafiyayyun nonowanta suka wanke masa ido tar!!! yake kallonsu kamar wanda ta samu tv ana film din soyayya!! ta tattaro towel din da sauri ta kare kirjinta duk da haka cibiyarta da wasu gurare na jikinta a waje suke! Ta dinga janyo towel din dake ‘kasan sa tana so ta rufe, ya janye hannunta idananunsa kan mararta da cibiyarta…..Tsorata tayi kwarai daga nin yanda yake wani wulkita idonsa, sai tayi gaggawar doke hannunsa dake damtse da bakinta ta ture shi da karfin gaske taja towel din ta daure jikinta,Tsaki! taja da fad’in” Allah ya isa.”! Ya bita da kallo wanda ya rasa ko kallon menene Yayi masifar shiga rudani wai shin ina alwashin da yaci akan yarinyar nan ne? ina tanade tanaden da yayi mata suka tafi? karfa ace yarinyar nan ta rinjaye shi tun ba’aje ko ina ba, anya ba zaiyi wa kansa fada ba kuwa ya kama girmansa ‘kankanuwar yarinya na ganin dama a kansa tana fada masa ko wace irin kalma Anya kuwa.’!!!!!!?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button