NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ana ya gobe suna wata ‘kawar Hafsa tazo musu da lafiyayyan garin magani mai suna ‘kare kukanka maganin na wahalar samu itama yayarta ce take can Ghana acan suke hadashi, maganin na kyau sosai sai dai tsada amma amfani daya zakayi dashi ka gane amfaninsa a jikinka, Wasila bata ji nauyin kud’insa ba ta dauki roba biyu dubu dari uku kenan duk roba daya dubu dari da hamsin….Tace zata bawa Hafsa kudin insha Allah.
Ita yanzu mutukar magani ta tabbatar da kyansa da ingancinsa ko nawa ne zata iya sawa ta siya domin ta gyara kanta da mijinta.

Saboda yawan ‘Korafin da Matan Kawunsa Almu keyi masa na rashin zuwan Wasila gidansu ya sanya ya dauketa ya kaita gidan ta wuni tare dasu, sosai Wasila ta yaba da mutuncinsu gami da karamcinsu sun karbeta hannu biyu sun dauki Zahra sun rike wannan ya dauka wannan ya ajiye kamar zasu cinyeta wannan kadai ya sanya taji tana masifar kaunar su, basu tafi ba har sai da Kawu Almun ya dawo daga kasuwa suka gaisa ya dinga sa musu albarka gami da adduar samun zuria mai albarka, a gurguje sukaje gidan Hajja itama suka gaisheta, sai bayan goma na dare sannan
suka koma gida.


BAYAN SHEKARU HUDU

Abubuwa da yawa sun faru a cikin wad’annan shekarun da suka gabata masu dadi da marasa dad’i to masu dad’in dai sunfi yawa Inda Wasila da Rashida suka sauke al’kur’ani mai girma da sauran litattafan addini kana kuma suka samu gurbin karatu a jami’ar bayaro university Wasila na karantar harkokin kasuwanci wato business administration ita kuma Rashida tana so ta zama malam asibiti ne Wasila mijinta ne ya za’ba mata abinda yake so sai tabi ra’ayinsa domin a zauna lafiya, cikin shekara biyu da ta gabanta Amadu Musa Ya kar’bi mulki jahar kano daga hannun Lawan Rabo ya cigaba da tafiyar da mulki kan tsari babu cuta babu cutarwa yanzu al’ummar jahar kano hankalinsu ya kwanta basu da da wata fargaba tunda komai na rayuwa yay sauki! !!!!

a jahar duk wani al’kawari da Amadu ya dauka ya sauke musu tare da taimakon mataimakin shi Sunusi Alhasan Khalifa Su Wasila ana gidan gomnati ana cin duniya sosai tayi wani uban kyau! da k’iba da kwarjini ta zama babbar mace, shekarun Zahra biyar, Wasila ta soma sha’awar haihuwa sai dai ta riga ta sanya inplan duk saboda karatunta wanda takeyin basaja, gurin shiga makarantar duk da ko bata rufe fuskarta da niqab ba babu wanda zaice ita matar governor ne sai dai kawai idan an duba yanayin fatar jikinta da hutu da kuma irin manya manyan motocin da ake kawota makarantar dan wataran ma harda securities suke tafiya, idan taga jama’a naso su fahimci wani abun sai kawai ta hana securities din binsu, tasa Rashida tajasu a mota.
Senator Nura mai wakiltar kano ta tsakiya shine ya kwallafa ransa kan Rashida wanda tun tana janyewa har dai ta amince masa saboda ta lura da mutumin yana da kirki da mutunci kuma yana sonta tsakani da Allah, yanzu haka saura watanni Biyu daurin auransu.


Camas! Kuka wiwi takeyi gami da nadamar abinda ta shuka yanzu neman Wasila take ruwa a jallo ta nemi yafiyarta bata san yanzu ganin Wasila ma wani gagarimin aikine babba, kusan kullum sai taje government house din securities suka koreta dan babu wanda yake mata kallon mai hankali tana yawo da yaggagun kaya shaye shayen da ta dinga yi ya mai da ita shudu shudu! Ga mahaifinta ya dade da rasuwa, sai mahaifiyarta suke zaune a gida duniya gabakid’aya ta juya mata baya duk wanda suka buga harkar siyasa sun watse As da su Alhaji Ma’aruf suma takansu suke dan Amadu ya kama governor Lawan Rabo ya gar’kame! suma sai da yasa hukumar Efcc ta tuhumesu, duk wani satar kudi da sukayi da kadarorin da suka siya sai da suka fadi inda suke Amadu duk ya kwace komai yace kudi na talakawa ne……Dukaninsu da gidan da suke ciki suka dogara shima kawai ya bar musu ne albarkacin aure da Haihuwa.


BAYAN SHEKARU BIYU

Wasila ta kammala karatunta cikin nasarori da samun cigaba, a rayuwa yanzu Wasila tana da ilimin da zata iya gogayya da duk wani jinsin mutum ba’kar fata ko farar fata, tana jin turanci sosai dan watarana ma idan ba tayi ra’ayin yin hausawa ba da turanci take magana, a cikin shekaru biyun da suka gabata, akayi bikin auran Rashida ta tare a gidanta, Uwani kuma ta haifi tagwaye duk maza tare da malam mai allo, hakanan Hafsa ma ta sake haihuwa inda ya kasance tazararsu da kishiyarta Aysha babu yawa, dan tun bayan samun gomnatinsu Khalifa ya kara aure yanzu haka Khalifa nada yara hud’u inda Amadu keda ‘Daya……..Ganin ana barinsa a baya sai ya tashi hankalinsa, yace.”Tunda an gama karatun aje a cire inplan d’in.
To itama dama a dame take haihuwar take muradi, Rashida ce ta cire mata aikuwa aranar da aka cire yini tayi tana zubar da jini ga jikinta yay tayi mata ciwo, sai da ta kwanta jinyya na kwana biyu sannan ta dawo hayyancinta, Jini na daukewa Yallabai ya bud’e Wuta, kullum in bai fita ba yana aikin abu guda, Itama gwanar da yake kullum cikin gyara take bata damuwa, Cikin ikon Allah kuwa ciki ya bayyana a jikinta, sosai sukayi farin ciki ita dashi, ba tare da ‘bata lokaci ba ya shirya musu tafiya zuwa ‘kasa mai tsarki domin suje sununa farin cikinsu gurin Allah Subahanahu wata’alah!!!

ALHAMDULILLAHI

Jama'a nan na kawo 'karshen wannan littafi mai suna 'YAR BANGAR SIYASA! Ina ro'kon Ubangiji Allah ya yafe min zunubai na, Abinda na rubuta dai-dai Ubangiji Allah ka bani lada, abinda na rubuta na rashin dai-dai Allah ka yafe min???????? Ku d'auki abinda yake da amfani ku watsar da mara amfani Nagode Jama'ata Allah ya 'kara kauna❤️ Sai mun sake saduwa daku a cikin sabon littafina mai suna
A KWAI WATA A ‘KASA!!

Wannan littafin ba zance komai a kansa ba saboda ni nasan komai????amma kai/ke duk ina bukatar kusan meke 'kunshe cikin littafin! AKWAI WATA A 'KASA!! Kada ku sake a baku labari! yana nan zai zo bada jimawa ba.

GA MASU BUKATAR PAID BOOKS ‘DINA TO SAI KU TUNTU’BENI TA WANNAN NUMBARS D’IN.
????????

08089965176
07084653262
BINTA UMAR ABBALE

LITTATAFAN MARUBUCIYAR:

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
*GIMBIYA BAL

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button