NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Tunda Ahamad ya taso yaga yanda mahaifin shi ke taimakon al’umma sai ya dora a inda ya tsaya tun yana dan shekara ashirin a duniya sunanshi ya ‘bace a gari mutukar baka kira
(Ba iya ka) ba to babu in zaka kwana kana kiran Ahamad babu wanda zai gane wanda kake nufi….

Ahamad jama’ar gari ne suka kwadaita masa sha’awar mulki da sam ba tsarinsa bane ya fiso yayi harkokinsa to shima kuma da ya zauna yayi nazarin yanda al’amuran siyasar ya ta’bar’bare sai kawai yayi sha’awar fantsama kansa a harkar domin ya taimaki al’ummar da suke galabaita a jahar mussaman talakawa sune dama abun tausayi.

Kallo guda za kayi masa ka gane yana da fuskar Salihai! a zahirinsa kenan a bad’insa kuwa mutum ne shi mara hakuri kuma sam baya barin ta kwana kamar zawo yake mutukar kayi masa abu idan bai rama ba sam baya jin dad’i….bayan wannan halin nasa bai da wani mummunar hali dama ance adan adam tara yake bai cika goma ba Ahamad nada tausayi da taimako sai nace muku ma duk rabin neman kudinsa yanayi ne kan jama’ar gari marasa galihu da na kasassu gami da marayu…….Dalili kuwa bashi da nauyin kowa a kanshi tunda shi ba aurene dashi ba ballanta ayi maganar yara, Jama’ar gari duk sun dauka yana da aure da iyali shiyasa duk adduarsu a kan iyalinsa take ‘karewa sai dai kawai amsa da “ameeen”

Nasan zakuyi mamakin namiji kamar Ahamad mai jini a jika sannan uwa uba kudi! ga kyau da kwarjini da haiba da yake dasu amma me yasa bai aure ba? Yana zaune hakane ba wai dan bashi da lafiya ba ko kuma rashin matar aure akwai ‘yan mata bila adadin dan ba zasu lissafu ba, kawai duk cikinsu bai ga wacce ta kwanta masa a ransa bane ya ajiye maganar aure a gefe saboda yasan cewa lokaci ne idan Allah ya kawo masa matar lokaci guda za’ayi a gama.

‘Daya daga cikin masu tsaronshi ne ya shigo palon….Ya d’aga kanshi yana kallonshi A nutse yace.”Ya akayi.”? Garba yace.”Kana da bakuwa tana dakin ‘baki mun sauketa.”

Jim! yayi yana nazari wace ‘bakuwa yayi kuma yanzu karfe goma na dare! Ko da yake ai tunda ya fara wannan harkar kuma yayi ta ganin jama’a ya mike a nutse Garba ya bashi hanya ya wuce kana ya take bayanshi.

‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi

 *NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300   Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176  sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

 *Free Pege5*
Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya 'karaso inda yake tsaye.....Kai a 'kasa Garba yace."Sir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar." Ido ya sanya masa a nutse yace."Kamar name kenan." Garba ya 'kara risinar da kanshi a kasa yace."Anya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba."

Murmushi yayi yace."Garba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo sa'a."
Garba yace."Ka gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba." Ya amsa da "ameeen.'' Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza, Garba ya take masa baya.

Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Ma'aruf a can tsallake a fake.....ranta duk a bace ta karasa bakin motar.....'Dan kwankwasa jikin motar tayi Camas! da Alhaji Ma'aruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur! ya bude mata motar yana fad'in" Ya akayi *'Yar gaske* Allah yasa kin aiwatar da komai." Rai a 'bace tace" Wallahi ya'ki bada had'in kai d'an iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba."

Alhaji Ma'aruf yace."Kai! wannan d'an iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji sha'awarki ba? anya ma kuwa yana da lafiya? duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji sha'awa ta kamashi." Ya 'karashe maganar yana bin jikinta da kallo.

Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas! take kwance a kai! Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka she'ke! Allah ya kyauta.

Hijab dinta ta sanya tace"Alhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku.

Alhaji Ma'aruf ya kunna motarshi yana goge gumi yace."Maganar ki gaskiya ce *'Yar gaske*  shiyasa muke 'kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin."

Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Ma'aruf na fada musu yanda suke dauki ba dad'i a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kad'angare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai kar'beshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya.

Wasila tace"Ka rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kad'ai ya isheshi sai nayi fata-fata da rayuwarshi."

Alhaji Ma'aruf yaji dadi maganar ta yace.''Mu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya *Yar gaske* zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu."

Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa *(Ba iyak ka)* har sai taga abunda ya turewa buzu nadi.


'Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen........


'Yar 'kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana  dakon dawowar 'yar tata.

Wasila ta mayar da 'kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu! kamar ba dare ba.

Uwani da Rashida suka fito a guje! Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshi.....Uwani na ganin Sabbin 'yan dubu-dubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu! ta rungume! 'yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar gud'a ta dinga rangadawa tana sakarwa 'yar tata kirari......Ita kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya.


Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige ru'babbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu 'kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga had'ddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya, wai! yaushe rabon duniya da ayya raye."!! Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannunta........Wasila tace"Yanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa.

Uwani tace"Ki d'an gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh! duniya kenan."

Wasila tace"Uwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga."  Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fad'in"Ai dama ni nasan jari na haifa ke ba 'karamar mace bace idan ba'aso ki dan komai ba a so ki dan 'kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina."

Wasila tace"Uwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sana'a muka fita mukayi ko ba haka ba Camas!." Tafada tana kallon Camas! dake irga kudinta.

Camas tace"Kwarai kuwa sana'ar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba."

Uwani tace"Kai amma wannan sana'a ta karbeku wallahi Allah ya bada sa'a ya taimake ku."

Suka amsa da "ameen." Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada ha'karkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita *Sana'a*

_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/11, 9:41 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
   ???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE…….!
Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za’a tura kudin.0542382124…….Binta Umar gtbank….Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din….07084653262_08089965176 sai na fad’i yanda za’a biya kud’in…..Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars…….90899076_88137740 katin airtal ko orange

Free pege4
Cikin takun girma gami da ‘kasaita ya shiga d’akin, lokaci guda ‘kamshin turaransa ya karad’e hancinta, ta d’ago shanyayyun idananunta ta zubasu a kansa, tun kafin ya ‘karaso inda take zaune ya ‘kare mata kalau black beauty mara tsayi sosai da cikar kirji dauke kansa yayi daga kanta ya had’e fuska sosai wannan bakuwar tashi ba ta arziki bace duba da yanayin suturar dake cikinta.

Tana sanye da wata matsatstsiyar t_shart da dogon wandon jins wanda ya fitar mata da zahirin hallitarta ta sanya karamin hijab wanda ko kirjinta bai rufe ba tsakiyar kanta yayi tozo da tsayi da alama tana da gashi sosai tunda ga alamunsa nan ya nuna saman goshinta.

Hannunsa cikin aljuhu ya isa inda take, ta mike tsaye da sauri tana marmar da shegun idanunta masu rikita lissafin da namiji……Ya kura ma jikinta kallo tayi sosai dan bai hango makusa a tattare da ita ba ta cika har ta batse kuma tana da abubuwan da yake bala’in so a jikin ‘ya mace sai dai kash! ba wannan ne a gabansa ba abunda ke gabansa a halin yanzu shine ya za’ayi talakawa su samu walwala da farin ciki.

Fuskarshi ya sake tamkewa tamau! yace.”Baiwar Allah daga ina? ance dani nayi bakuwa na dauka ta arziki ce sai a ka samu akasi.”

Wasila taji ciwon maganarshi kasancewar ta macen da bata daukar raini mussaman ga da namiji basarwa tayi ta matsa kusa dashi cikin salon janye hankali tace”Daga duniya na fito nazo ne in d’ebe maka kewa nasan namiji lafiyayye kamar ka na bukatar lafiyayyar mace ka mata.

Tsawa ya buga mata yana nuna ta da hannu”Ke! cikin gidana kika shigo kina min wannan maganar? ashe dama zargin da nake miki gaske ne okey get out from my house. “! Maimakon ta fita sai ta durfafeshi tana so ta rungumeshi, ya kai mata wani wawan mari! yana ya tsine fuska sai karkad’e jikinsa yake kamar wanda ya ra’bi motar daukar kashi…..Ya mutsa fuska yake yana korar shaid’an, yace.” Za kici Ubanki yanzu yanzu zan sanya a xane miki jiki har gida zaki shigo ki kawo min iskanci ni ba’irinku bane.” Fita yayi yana ‘kwalawa Garba kira.

Wasila ta dauke hannunta dake fuskarta gaskiya yana da taurin kai ta lura ba zai bari ha’kansu ya cimma ba ruwa ba d’an iska kawai tayi irin wannan shigar ya dinga kauda kai yana ya tsine fuska anya ma kuwa lafiyayye ne? bata da mai bata amsa sai tayi maxa ta dauki jakarta zata futa suka buga karo dashi yazo zai shigo kirjinta ya daki kirjinsa yayi saurin ja gefe guda yana kallonta sai wani gumi yake kamar wanda yayi tsere.

A ya tsine ta kalleshi tace”Na d’auka ai lafiyayyan namiji ne ashe hotiho ne har kana zagina ‘kato da kai baka kunyar zagi anzo a jiyar da kai dad’i kana gudu Allah ya kyauta kaje ka nemi magani.”

Wata sha’ka ya kai mata ya matse ta a jikin bango (garo) ta dinga kakari idanunta sunyi jajawur!!! Cikin kaushin murya yace.”Idan za’a had’a min iri-irin irinki guda dari duk zan gama musu aiki ba tare da nagaji ba, ‘karyar iskanci kike yarinya da ina da bukatar mace a yanzu dana fatattaka ki kuma in kwana lafiya ‘yar iska mara galihu.”

Hannu tasa tana ‘kokarin ‘bam’bare hannunsa dake sha’ke da wuyanta duk ta muzanta sai kyarmar jiki take tana cizan le’banta…..Sai da ya gama galabaitar da isa sannan ya saketa aikuwa ba tayi wata-wata ba ta kai hanni gabanshi zata d’amka! yayi gaggawar ri’ke hannunta yana kallonta da mamaki a tare dashi.

Sun jima suna kallon juna ita dashi mugun mamakin ‘karfin halin yarinyar yake wato shammatarsa take so tayi ta nakasta shi….Ido jawur! tace”Sake min hannuna.”! Ya ‘kara rike hannun tamau! yana sakin wani killer smile yace”Kina so ki ta’ba ne.”? Wasila tayi tsuru-tsuru tana kallonsa sam ba tayi tsammanin guy zai samu galaba a kanta ba.

“Wannan kayan aikin da kike gani yafi ‘karfin irinku ‘yan iska! na kamilar mace ne mai addani ba irinki mai yawon ta zubar ba.” A fusace! ta fuzge! hannunta ta watsa masa kallon raini fuuuuu!! ta kama hanyar fita……Taku uku yayi ya cimmata tare kofa yayi yana me bin jikinta da wani shu’umin kallo.

“Sosai kikayi babu wata makusa a jikinki duk inda ‘yan mace ta kai kin kai yarinya sai dai sam baki burgeni ba idan ma turo ki akayi to sai kije ki sake sabon shiri ki sani Ahamad ya wuce tunaninki.” Yana ‘kare maganarshi ya ‘kwalawa Garba kira.

Ya shigo da sauri yana fadin “Yalla’bai! gani.” Yace.” Maza rakata da bulala idan tayi gardama ka zane ‘kafafunta.” Garba Ya kalleta, “Wuce muje.” Yafada cikin bin umarnin Ubangidansa.

Wasila kamar ta hadiye zuciya ta mace tunda take a rayuwa ba’a ta’ba tozarta irin yau ba lallai guy bashi da mutunci amma babu komai sun d’aura idan kere na yawo zabo na yawo watarana za’a had’u.
Kallon uku shaura kwata tayi masa kana ta gyada kai ta wuce shi…..Garba ya bita a baya da zabgegiyar bulalarsa….Harbar gidan ya fito ya tsanya tare da zuba hannuwansa cikin aljuhu yana kallo Garba ya tasa ‘keyarta har bakin gate yanayi yana caud’a bulala a ‘kasa kamar zai daketa hakan ya sake kular da ita ta sake ‘kullatar guy girgiza kai kurrum take tabbas maganar da chamas! tayi gaskiya ne babu abunda yake cikin harkar Siyasa sai tozarci da wulakanci, Garba na ganin tayi nisa da layin sai ya juya ya koma cikin gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button