NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wasila ta juyo tana dariya da fad’in “Kai Hajja! idan kin tafi ai ba Kishiyarki ce kadai zatayi kewa ba har damu dan Allah ki zauna kada ki tafi wallahi ba zamuji dadi ba.” Hajja tace”Tafiya kuwa ta zama dole gobe i war haka na sauka a gida.” Tana tafiya domin isa dainnig din take”Gaskiya Hajja ba zaki tafi ba zamu shiga cikin wani hali na kew…….Kasa ‘karasa maganar tayi ganin ya zuba mata ido yana mata wani irin masifaffan kallo tamkar zai cinyeta, a take ta dai-daita nutsuwarta ta dan rage walwalar fuskarta, ta dan gyara kujera ta zauna tana ya mutse fuska, ita sam bata lura ma dashi a palon ba, haba wannan kallo kamar mawuyanci.”
Tea take kokarin had’awa hannunta ya shiga kyarma! sakamakon idanunsa masu mugun dafi da ya zuba mata, ta dan kalleshi a sace sai taga hankalinsa gabadaya nakan jikinta yana kallon brest dinta da suka fito ta saman riga……..Taji dad’in hakan dama yaushe zai iya daurewa tasan halinsa sarai! sai ta dinga d’an gantsaro ‘kirjinta tana d’an motsa jikinta da sunan tana gyara zamanta…….Wayarshi tayi ta ringing yana ji ya kasa dauka.
Ta dago a hankali tace”Ana kiranka a waya.” Dan dauke kansa yay yace.”Rabu da ita.” Shuru tayi tana ta’be bakinta, ta had’a tea din zata fara sha yace.”Bani wannan ki had’a wani.”
Mi’ka masa tayi ba tace komai ba ta had’a wani ta fara sha tana had’awa da bread, tana kallonshi ya kasa shan tea din sai auki tsaki da yake saki yana latsa wayarsa, ba tace masa komai ta gama break dinta ta mike ta bar masa gurin………..Tashinta da kamar minti biyar shima ya mike a maimakon ya fita kamar yansa ya niyyata sai ya shige dakinsa ya kwanta, zazzabi zazzabi na nema ya rufeshi.

Ita kam Wasila taji dad’in yanda taga tarkonta ya kamashi, murmushi take saki lokaci da lokacin tana jin sanyi cikin zuciyarta, tasan ko bata kai masa kanta ba to tana da tabbacin shi da kansa xai kawo kanshi……….Tunda ya shiga dakinshi bai fito ba sai lokacin sallar la’asar Hajja na kokarin shiga ta dauro alwala taga fitowarshi shima da shirin zuwa masjid tace”A’a dama kana ciki baka fita ba.”?
A dan kasalance yace.”Hajja ban fita ba wallahi zazzabi zazzabi nakeji a jikina.”Tace.”Ashsha! yana da kyau kasha magani.” Yace.”Yanzu idan na dawo daga massalaci zanci abinci nasha magani.” Tace”Allah ya sawa’ke.” Ameen yace ya fice daga gidan.

Wasila kam bayan tayi sallah wani wankan ta sakeyi ta cancad’a kwalliyarta cikin kananun kaya, riga da sket ta gyara gashinta da mayuka sai sheki yake ta daure da katon ri

bbon dankwalin abaya tayi rolling dashi, ta fito palo tana zabga kamshin turaranta mai dadi……..Tana zama Hajja tace”Kinga kuwa mijinki bai da lafiya ashe bai fita yau kwata kwata yana daki a kwance sai yanzu da ya fito zai tafi massalaci yake min bayani.”

Ta danji gabanta ya fad’i kadan anya kuwa wannan rashin lafiyar ta gaskiya ce? maji ma magani dai.” Abinda tafada kenan cikin zuciyarta…..Ya shigo palon gabakidaya jikinsa babu kwari ko ga yanayin tafiyarshi ma zaka fahinta har yayi nufi zama a gurin cin abincin sai kuma ya fasa ya nufi dakinsa.
Hajja tace”A’a ya zaka shige kuma kaci abinci kasha magani dan Allah kada ka bari zazza’bin nan yay ‘karfi a jikinka…..Ya dan Juyo yana kallon Hajjan dan ko da wasa baiyi kuskuran kallon Inda Wasila ke zaune dalili be san halin da zai shiga ba idan ya kalleta yace.”Hajja bana jin zan iya zaman gurin nan Ke! Ki kawo min abincin daki.” Yafad’a yana d’an hararar inda take zaune.” Hajja tace”Allah y sawa’ke Wasila tashi maza ki kai masa abincin ki tsaya yaci sosai yasha magani.”
Wasila ta mike ta nufi dainnig bata da wata damuwa dan ta tabbatar da cewar cutar ‘karya ce ya ‘kir’kirarwa kansa.

Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
80
Yana kwance rigingine idanunsa na kallon rufin dakin ta shiga dakin hannunta rike da karamin tire dauke da kayan abinci a kai, sallama tayi a nutse ta shiga dakin, ya amsa sallamar ba tare da ya kalleta ba, a hankali ta dan jawo wani karamin teble ta ajiye tire din abincin ta dan tsaya tana kallonshi, har yanzu guri guda yake kallo……Kamar za tayi magana kuma sai ta girgiza kanta a hankali ta juya zata tafi, Gyaran murya yay yana kokarin mikewa zaune yace.”Dawo ki had’a min abincin.”
Ta dawo fuskarta babu wata cikakkiyar walwala….Kasan kafet ya sauka ya tankwashe kafafunsa, yana kallonta ta dan sunkuya tana hada mishi abincin Brest dinta duk sunyo waje tamkar ma batasa breziya ba, ajiyar zuciya ya sauke idanunsa kurrr akai yana shafa gemunsa, ta hada mishi abincin ta aje gabanshi, yace.” dauko min ruwa me sanyi da lemo.” Ta wuce can inda fridge yake nan ma ya bita da kallo,
tana juyowa ya dauke kansa yana dan juya abincin da cokali da kyar ya kai loma guda bakinsa ya ajiye cokalin yana fad’an “Anya zan iya cin abincin nan zazzabin nan ya sanya bana jin dadin bakina.”
Ta lura magana yake nema da ita a takaice tace”Ka daure kaci kasha magani zakaji sassauci.”
Yace.”Zan gwada ci yanzu.”
Ta ajiye masa lemon da ruwa ta kama hanya tayi ficewarta tana wata irin tafiya sassan jikinta na wani irin motsawa.
Jingina jikinsa yay jikin katakon gadon ya langwabe kansa tare da lumshe idanunsa tamkar wani maraya yana sake jin wani irin feeling na taso masa.
Da kyar ya iya cin loma biyar na abincin ya mike daga gurin
Wayarsa ya dauka ya kirata lokacin suna palo suna hira, mamaki ne ya kamata ganin kiran wayarshi,
Cikin wata ‘yar iskar murya tayi mishi magana, ya sake shiga tashin hankali da damuwa, murya a sanyaye yace.”Kizo ki kwashe kayan abincin.” A hankali tace “To.” Takashe wayar, minti biyu ta mike ta nufi dakin….Idanunsa tsaye a kofar shigowa so yake kawai ta shigo ya cigaba da kallon albarkatun jikinta masu rikirkitashi, ta shigo dakin, yabi fuskarta da kallo kamar tsohon maye, dan gyara bakinta tayi ta isa inda yake zaune ya wani mi’ke kafafunshi, abincin dake gabanshi ta kalla ta ganshi da yawa dan ko rabi be ciki ba…..A hankali tace”Ai baka ci abincin ba.” Ya wani lumshe jajayen idanunsa ya budesu a kanta yace.”Waye ya fad’a miki.!? Ta girgiza kanta da dan ya mutsa fuska tace.”Ba kowa.” Daga haka bata sake cewa komai ba dan ta lura neman shiri yake da ita ita kuma bata shirya ba tukkuna.
Tana kokarin harhada kayan abincin yace.”Idan zaki zauna ki bani a baki zanci kasala ce take damuna da rashin kwarin jiki shiyasa na kasa cin abincin.”
Tace.”Allah ya sawa’ke!.” Daga haka bata sake magana ba ta dauki tiren abincin ta futa daga dakin cikin zuciyarta tana fad’in “Nasan wayo kawai ka shirya idan waya da budurwa ne ai ba zakace kasala kake ba.
Tana aje kayan abincin a cikin ta samu wani madaidaicin bokitin roba ta zuba ruwa me kyau, kaninfari ta zuba a cikin ruwan me d’an dama ta mayar ta rufe, sannan ta bud’e freezer mai dauke da kayan miya ta dauko wata madaidaiciyar kabewa ta feraye ta ta yanka dai dai misali ta zuba ruwa ta dora a wuta, tana tsaye ta dawu ta sauke ta samu ludayi ta murjeta tare da ruwanta, fridge ta bude ta sanya a ciki ta fita daga cikin din dai dai lokacin Rabe ya shigo domin ya fara aikinshi na abincin dare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button