NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

wani bane kawai dai kinsan wasu masu kudin kuma ranar da mukaje ai bai san cewar mune ba shiyasa, ni daina zan cigaba da tayaki addua kan Allah ya karkato da hankalinsa kanki gaki dauke da cikinsa ai dole ma nayi sha’awar ki koma hannunshi kuji dadin rainon danku.” Tsaki taja tana fad’in “Ranki zai ‘baci mutukar kika sake yi min wannan banzar maganar.”! Rashida tayi shiru tana kallonta…..Mikewa tayi taje ta kwanta tare da rufe kafafunta, maganar rashida tasa duk wani bakin cikin dake damunta ya dawo sabo, dal! ta dinga jan tsaki tana juye juye, hawaye ta share tana sake tuno lokacin da take birgima da ihu a gidanshi tana rirrikeshi ya taimaketa ya hakura ya mai da ita yanayi mata wulakanci, ai wallahi ta bar auranshi mutukar ta cika ita d’in ‘yar halak ce……..Da kyar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai marasa dad’i.

Washe gari da safe da rubutu ta fara karyawa malam mai allo ya fara rubuta mata a’lkur’ani ya Umarceta tayi bisimillah tasha kana ta shafe cikinta dashi, sai da ya tabbatar tayi yanda yace din sannan hankalinshi ya kwanta………..Bayan sun karya ne, sai sukayi wanka, rashida ta taya Bitan gyaran gidan ita kuwa Wasila dama tana yin wanka ta kwanta bacci mai nauyi ya dauketa.


Ya tashi cike da rashin walwala da rashin kuzari gabakid’aya duniya tayi mishi zafi ya rasa abinda zaiyi ya samu sassauci, da kyar ya samu ya kur’bi tea kofi daya, yayi kwance kan kuje daga shi sai singlet da wando iya gwiwa, wayarshi yake dubawa, ya bude ma’adanar hotonanshi, ya lalube pictures dinsu yana kallo, ji yayi hankalinsa ya tashi ya mike zaune yana rawar jiki, dan wayar har sai da ta kusa faduwa ya riketa da kyau, ya kurawa fuskar wayar……Da sauri ya mike ya nufi dakinshi, drowars ya shiga budewa nan naga ya fito da Pose dinta da sababbin wayoyin da ya siya mata, zama yayi gefan bed ya kunna wayar yana dubawa, numbobin mutum uku ya gani tashi data As sai kuma wacce yaga ansa Hdz Camas! da sauri ya dauki numbar awayarshi dan yana zargin itace numbar yarinyar da yake nema tayi mishi karin bayani……sai da ya kira sau uku kafin A daga wayar, Camas na kokarin shiga sabuwar motarta kira ya shigo wayarta koda ta duba taga sabuwar numbar bata damu ba saboda tasan tana hurd’a da mutane sosai Ta daga wayar da sallama a bakinta.

Ya amsa a nutse yana fad’in “Ina magana da Hadiza ko.”? Tace ” Eh ko kace Camas! dan haka jamaa ke kirana.” Ajiyar zuciya ya sauke, wanda har sai da taji a kunnanta, ya mike ya kunnanshi makale da wayar ya fito palo ya zauna kan kujera a Yace ” Nasan Zakiyi mamakin me magana dake, Ni ne Ahamdu Mijin kawarki Wasila.”
Camas taji gabanta ya yanke ya fadi har sai da wayar ta kusa faduwa, baki na rawa tace”Yallabai ina wuni.” ya amsa a nutse yace.”Tambayarki zanyi.’ Tace.”Allah yasa na sani.” jikinta duk yayi sanyi dan tayi tunanin ko zai tambayeta kan kud’adan wasila ne wanda ta riga tayi fata fata dasu mussaman da taji labarin sun bar gari gabad’aya sai ta sake sakin jikinta tana facakarta da kudi.

Yace.”Ko kin san ina ‘kawarki suka koma da zama.”? Shiru tayi tana tunani, Yace.”Ke nake sauraro.” Tace”Yallabai ban sani ba wallahi dan nima sai labari naji a gari wai sunyi tafiya amma dai nafi tunanin ko can kyauyensu suka nufa Garko.”

Yace.”Basu nufi can ba domun kawun su ya tabbatar min da cewar basu je mishi ba ya dai ce yana tunanin sunbi mahaifiyarsu, shin ko kin san inane garin su mahaifiyar tasu.” Tayi shiru tana tunani kafin tace”Wallahi na san sunan garin amma ya kwanta min bari yanzu in kira mahaifiyata a waya nasan ita bazata rasa sani ba, insha Allah zan kira ka sai na fada maka.”

Yace.”Okey to ina sauraranki.”! Camas! ta kashe waya tana tunani cikin mota, shin me yasa guy nan yake son sanin inda Wasila take, ko dai zai mayar da ita ne a matsayin matarshi, tabdijam idan hakane kuwa wallahi ba zata fad’a mishi ba, key tasa zata tashi mota, kiranshi ya shigo tayi banza da wayar har ta katse….Ta tashi motar ta tanaji wayarta nata famar ringnig amma taki dauka, har sai da ya gaji ya hakura.

Yana zauna rike da waya ya rasa ya zaiyi amma yarinyar nan ta shammace shi gabakidaya ya d’o

ra buri da tunani a kanta yana tunanin koda sunanan garin da suke ya ji ya san mutukar sun shiga garin tunda ba’ki ne nemansu ba zaiyi wuya ba, bai hakura ba ya cigaba da kiran wayar yana ta adduar Allah yasa ta dauka kawai sai yaji ta kashe wayar ma gabad’aya, ya dinga bin wayar tashi da kallo tamkar wani zautacce.


Yau kwanansu hud’u a Garko hankalinsu ya kwanta sosai Wasila ta mirmure ta samu lafiya sai abun da ba’a rasa ba, kuma laulayin ya danyi sauki sai dai jefi jefi take amai shima da safe takeyi kafin ta karya……Bata aikin komai Bitan da Rashida suke aikin gidan kullum malam mai allo cikin siyo mata kayan gon yake irinsu d’ata da goba mangwaro da sauransu, sannan kullum sai tasha rubutu da tofi safe da dare, ita kanta yanzu ta soma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya mussaman in ta juya gabas yamma kudu da arewa tana ganin ‘yan uwanta da danginta na shige da fice a gidan…..Ita kanta Hajara kullum a tafe take idan bata zo yau ba to gobe zaka ganta tazo kuma bata zuwa gidan hannunta haka kawai sai ta tazo musu da tsarabar kayan kwadayi……………..

Malam mai allo da kanshi ya shiga kasuwar garin ya siyo musu abubuwan bukata dai-dai karfinshi yanzu babu wani abun da zasu nema su rasa a gidan dai-dai silafas na yawo a tsakar gida mai allo ya siyo musu ko wanne da nashi.


‘Bangaran Ahamdu kuwa jinya ya kwanta ta tsayin sati uku har sai da Hajjah tazo gidan tayi jinyarshi wanda sai a lokacin ma ita ta san abinda ke faruwa, aikuwa ta shiga yi mishi fada tamkar ta ari baki, taji ciwon abinda ya aikata shi ba yaro karami ba, an samu yayi auran kuma baije ko ina ba ya fara saki, ai mutane ma sai su daukeshi karamin mutum……Ahamdu baya so ya fada mata dalilin da ya sanya hakan ta faru kawai dai yace mata tsautsayi ne da kaddara, ita kuma tace lallai sai ya kaita gidansu yarinyar tayi bikonta, nan yake shaida mata shima yanzu halin da ake ciki bai san inda yarinyar take ba, Hajjah ta dinga mamaki Yace.”Naje can garin nasu gurun waliyyinta shine ya tabbatar min da cewar bata gurinshi amma yafi tunanin tabi mahaifiyarta garinsu, to inda aka samu matsala shine shima bai san wane gari ne ba.”Hajja dai ta dauki laifin kacokan ta dora a kanshi ta kuma ce idan haka zai dinga auran yaran mutane yana saki to babu ubanda zai bashi auran ‘yarshi mutukar ba kwad’ayayyan abin duniya bane……Tace kuma lallai idan ya samu sauki ya dauketa ya kaita can gurin mai allon a bashi hakuri a bisa abinda akayi mishi, bai musa mata ya amince da maganarta saboda dama can baya tsallake umarinta


Bayan Sati biyar…….Cikin Wasila ya fito sosai dan har ya hud’a zani yayi kurcici dashi kamar an kifa ‘kwarya yanzu yana matakin wata biyar da kwanaki, tayi kyau sosai ta murje ta daina laulayi yanzu komai tana ci ta zauna lafiya ta daina amai da sauransu, sai dai kuma yanda cikin ke mata motsi a cikinta ne yake damunta, ga wani uban cin abinci da takeyi mutakar tana jin yunwa idan bataci abinci ba sai jikinta yay ta kyarma shiyasa kullum bitan cikin d’orawa da saukewa takeyi bata bari abinci ya yanke mata, sabida Wasila ta zama rumbu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button