NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘YAR BANGAR SIYASA!!
END????

ALHAMDULILLAHI

85
Gurin ne ya sake hargitsewa da hayaniya dalilin zuwan Securities din, kafin kice kwabo jama’ar da sukayi dafifi a kan titin sun soma gudu saboda gabakidaya harbin bindigar da Police din keyi yayi masifar razanasu, sai kowa ya soma kokarin ceton ransa, amma dai duk da haka sai da harbin ya samu wasu daga cikinsu suna kwance a gurin suna ihu jini tamkar yay magana kan titin yayi kaca kaca sai hayaki ne yake tashi a gurin gashi gari ya soma duhu magariba ta gabato…..Governor na ganin abinda ke faruwa ya kira d’aya daga cikin mutanan da ya tura yace.”Maza a kwashi wa’inda suka jikkata akai su asibiti, Allah sarki mutum kusan bakwai sun mutu ‘yan uwansu sai kuka suke suna d’ora hannu aka hade da tsinewa Lawan Rabo albarka suna tur da wannan mulki nashi….Amadu na katsina tare da Abokinshi Alh Muktari labari ya samesu dan sai da suka ga abinda ke faruwa a labarai, hankali a tashe sukayi sallama da abokinshi ya dauko hanyar dawowa gida…..Koda ya iso bai nufi gida ba kai tsaye gidan redio na Salama ya umarci Garba ya saukeshi, abinda bai ta’ba faruwa ba kenan wai ya shiga gidan redio dan ya yad’a manufarshi,
Tashar redion Salama taji dad’i sosai da zuwanshi, kafin kice me sun fara sanarwa yanzu yanzu d’an takarar governor kano mai girma Amadu Musa zaiyi magana dangane da abubuwan dake faruwa a wannan jahar.
Jama’a duk suka maida hankalinsu gurin sauraran jawabinsa…..Ya fara da bisimillah had’e da addua kamar yanda annabi ya koya mana kana yace.”
Hak’ika banji dad’in wannan abunda ya faru ba a yau! hankalina ya tashi matuka! ganin yanda jama’a suka jikkata wasu har suka rasa ransu, Duk abinda wannan gomnati tayi muku bai kamata ku dauki irin wannan mataki ba, don yin hakan ba zai amfanar daku komai ba sai ‘bacin rai gami da nadama da dana sani, na tabbata yau wasu daga cikinku suna nan cikin bakin ciki da damuwa rashin Iyaye da ‘yan uwa mata na gida suna kuka saboda wannan tashin hankalin Wata mijinta ya mutu wata mijinta ya ‘kone ko ya karya, duk saboda wannan hatsaniyar data afku, wannan abun da jama’ar wannan jaha sukayi bai dace ba shi wanda kukeyi dominsa din baza ku ganshi ba ballanta ku cimma burinku akansa, duk abinda hakuri bai baku ba rashin sa ba zai baku ba, kuyi hakuri ku barshi da Allah bisa ga zalintarku da yayi sannan kuma cigaba da yi mana addua kan Allah ya cika mana burinmu a cikin wannan tafiya, mutukar Ubangiji Allah ya dam’ka min mulki wannan jahar zan share muku hawaye zakuyi mamaki sannan dukanin wanda yay asarar gidanshi ko masana’antar sa wannan gomnatin insha Allahu Ni Amadu! na kar’bi wannan mulki nayi muku alkawarin biyanku hakkinku, wannan titin kuma da suka d’auko gadan! gadan! sunayi ni dama nasan ba iyawa zasuyi ba ku zuba musu ido, mu idan muzo namu salon daban yake da nasu, babu wani abu nasu da suka bari wanda zamu d’ora aikinmu akai komai sabo zamu ‘kir’kira! babu algus babu almundahana a ciki, zamuyi mulki bisa amana da tsoron Allah Insha Allah! Daga karshe nake muku fatan alkairi al’ummar wannan jaha mai albarka ku cigaba da addua kan Allah ya kawo mana sauyi mafi alkairi sannan kuma na umarce ku da kada ku kara tada wata tarzoma, saboda yin hakan bashi ne mafita ba, mafita shine ku bamu had’in kai aranar za’be! kowa ya fito ya za’bi Jam’iyyar mu mai albarka tun daga sama har ‘kasa, ku za’bi Jam’iyyar CPC Sa’a! Wasalamu alaikum.”

Amadu na gama Jawabinsa gari ya dauka anata hayaniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, haka can ma gidan gomnatin Governor Lawan Rabo da mataimakinsa da kuma mabiya bayansu hankalinsu yay bala’in tashi, governor Lawan Rabo ya dinga da ya sanin hukuncin da ya yanke na tura securities da yayi suka dinga harbi, yasan har duniya ta nad’e jama’a ba zasu ta’ba mantawa da zamaninsa, ba, aikuwa yana jikin wannan jimamin kiran mai girma shugaban ‘kasa ya sameshi, lallai yau yake so ya nufi Abuja domin yana so ya zauna dashi.
Lawan Rabo ya shiga rudani mutuka yayin da mataimakinsa yayi nasa guri dama shi d’an ba ruwa na ne tunda duk shawarar da zai bashi baya dauka yanzu data kwa’be masa sai y

aje yaji da matsalarsa.
As da sauran jama’arsa ne suka rakashi can fadar shugaban ‘kasar.

Duk da suna cikin karkara sai da labari ya samesu, dan Wasila har jawabin mijinta sai data saurara, hankalinta a tashe ta dinga kiran wayarshi domin taji lafiyarsa, wayar bata shiga da alama dai gidan Malam bai da network me kyau.

Sai misalin goma shaura na dare ya shiga gidanshi, yay wanka ya fito palo wanda yay dai-dai da shigowar Khalifa suka zauna suna sake tattauna maganar………A dai-dai lokacin ta sake gwada kiransa a waya a kaci sa’a wayar ta shiga, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace”Habibi sannu da hanya ina fatan ka dawo lafiya.”
Yace.”Na dawo lafiya lou har yanzu ban samu sukunin kiran wayarki ba.”
Tace.”Nima tun dazu nake ta neman wayarka network yana hanawa, na saurari Jawabinka dazu kano babu lafiya ashe.” Yace.”Eh gashinan jama’a nata fama wai sai sun halaka governorn ku Lawan Rabo.”
Tace”Dan Allah daina cewa governor mu wallahi na tsaneshi mugu ne.” Yace.”A haba dai yanzu kin fita daga jam’iyyarsu kenan.”? Kamar zatayi kuka tace”Ka bari bana so dan Allah.”
Ya dan shafa saisayayyar sumarshi yace.”To na bari ina Mommyna.” Tace”Tana goye a bayan Bitan.” Yace.”Wai ita wannan Bitan din bata gajiya da hidima ne.”?
Murmushi tayi tace.”Mutuniyar kirki kenan.” Yace.”Ina kaunar matar sosai saboda tana kaunarki gashi yanzu tana gwadawa kan Mommyna.” Mirmushi kawai tayi, yace.”Kin san wani abu.”? Girgiza kanta tayi tana lumshe ido yace.”Gabad’ayansu Malam Kawu Habibu Inna Hajara Momynmu da ita Bitan! Dukaninsu zasuje Umara insha Allah sati biyu masu yawa.” Wani irin farin ciki ne ya lullubeta kamar tayi masa ihu a wayar sai dai ta daure ta dinga zabga masa godiya da addua muryarta sai rawa takeyi……Yace.”Babu komai ai dangina nayiwa meye abin godiya.” Tace”Eh duk da haka nagode.” Yace.”Idan sun dawo zamuje namu umarar.” Tace”Tom shikkenan yanzu kuwa zanje na fadawa Kawu wannan albishir din.” Murmushi yay yace.”Sai Allah ya kaimu gobe ko.”? Tace”Tom Allah ya kawo ku lafiya.”
Kashe wayar yay yana murmushi, suka hada ido da Khalifa dake zaune ya zuba masa ido, hummm! Wai Amadu ne ke hirar soyayya wanda da idan ance zaiyi sai yace shi bashi da lokacin yin haka.
Murmushi yay yace.”Dama kana nan a zaune.”? Khalifa ya murmushin takaici yana jan ‘karamin tsaki yace.”Ai baza ka gane ina gurin ko bana gurin ba tunda idanunka sun rufe.”
Ya dan shafa kanshi As’usel da murmushi a fuskarsa yace.”Khalifa ina son yarinyar nan wallahi.” Khalifa ya mike yana fad’in “Ai ba sai ka fada ba duk ga alamu nan sun nuna.” Mikewa yay ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare suka fita daga palon.

Wasila ta sanar da Malam alherin da Amadu yay musu, malam ya shiga tsananin farin ciki mara misaltuwa ya aika aka kira masa Kawu Habibu shima ya dawo gida saboda daurin auran ya tarasu ya shaida musu abinda ke faruwa, Inna Hajara ta dinga rangwada ‘buda a gidan tana fad’in “Haihuwa mai rana Yau ni Hajara nice zanje wannan guri sai ta fashe da kuka tana fyatar hanci tace” Allah ya ji’kanka dan uwana insha Allahu kana aljannar furdausi, Bitan tace ta dinga rarrashinta da ta daina kuka domin yin hakan zai sanya su Wasilan hankalinsu ya tashi, da kyar Inna Hajara tayi shiru ta kama Wasila ta rungume a jikinta tana mata addua gami da hud’uba kan zamantakewar aure.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button