NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Kashe gari da safe suka nufi makarantar Lokacin Mahaifin Camas har ya mai da ita suka ganshi yana kokarin fitowa, sama sama sika gaisa kana suka wuce ofis din headmaster,

Uwani na shiga ta fashe da kuka, duk malaman dake zazzaune suka zuba mata ido, sai ta kama hannun Wasila tace”Malam wannan yarinyar marainiya ce ubanta ya mutu jiya tazo tana kuka tare da shaida min cewar wai ance ta daina zuwa sai Ubanta yazo tukkuna, Wasila bata da Uba ya mutu nice gatansu ita da kanwarta.”

Headmaster yace.”Baiwar Allah daina kuka zauna kiji dalilin da ya sanya na koresu daga makaranta ita da kawarta. Uwani ta zauna tana share hawaye Headmaster ya fara yiwa Uwani bayani kan shirme da shiriritar da sukeyi a makarantar sam! basa gane karatu sai auki tallah da kula kulan maza.” Uwani tace”Insha Allah xasu gyara ai nayi mata fada sosai a gida nace ta tsaya tayi karatu shine gatanta.” headmaster yace.”Ashe kin gane, yanzu shikkenan tunda kin kawo mana uzurinki, yarinyar zata cigaba da zuwa makaranta amma na soke zuwa da kayan tallah! duk sanda ta sake zuwa da kayan tallah to sai na koreta.” Uwani tace.”Insha Allahu zamu kiyaye.” Headmaster ya kalli Wasila da tayi fi’ki-fi’ki da ido tab! bata jin zata daina tallah a makarantar wallahi jinsu kawai takeyi. Yace.” Wuce maxa ki shiga aji saura in kuma ganin ki a zaune a filin makaranta kina siye da siyarwa, Simi simi ta wuce ciki Uwani tayi musu sallama ta tafi.

To tana komawa gida Uwani tace”Kinga Wasila dokar da headmaster dinku ya kafa ba mai yiwuba bace, zaki sanja tsari ne idan kinje da kayan sana’ar ki to ki dinga zama a aji kina siyarwa kar ki fito harabar makarantar nasan yau da gobe mutane suka gane zasu shigo su siya.” Wasila tace”Wannan shawara tayi, To haka dai ta cigaba da zuwa da kayan sana’ar ta, ‘yan matan ajinsu na siya na wasu ajin ma na shigowa su siya, tsayin shekara biyu headmaster bai san abinda ke faruwa ba..

Salimat itace suke ajiya daya da Wasila, Suhairat tana aji shida, su kuma suna aji biyar, ranar Suhairat ta shigo ajinsu bayan an fito break tana neman Salimat! kawai sai taga an kewaye Wasila ana ta siyan alawar madara da kantu!!! Suhairat dake tana da mukami a makarantar, sai ta nufi gurin, tana wani cin kunu ita gata mai yalon dankwali tace”Ke Wasila ashe bakiji gargadin da headmaster yayi wa masu kawo tallah ba a gurin Assamble ba shine dake ke mai taurin kai ce kike sauya salo kike tara mutane a aji suna siya to yau asirin ki ya tono.” ! Sai kawai ta hau watsi da botikayen kayan siyarwa duk suka watse a ajin…..Wasila ta kurma wani uban ihu!!! ta cakumi Wuyan Suhairat ta hau jibgarta cizo da yakushi Camas! na taya ta Suhairat ta dinga kuka tana neman dauki, Wasila ta haye ruwan cikinta sai da ta sumar da ita sannan taji dad’i……Aikuwa yan aji suka dinga ihu! da gudu Rashida ta nufi ofis din malamai ta sanar musu….A take suka shigo, aka yayyafawa Suhairat ruwa ta farfado tana kuka fuskarta duk tabon cizo da yakushi….
Headmaster ya tarkatasu gabadaya suka nufi ofis……..Suhairat na kuka take bayanin abinda ya faru Wasila da Camas! suna ‘karyatawa da fadin sharri tayi musu…..Headmaster ya kalli Wasila bayan ya gama jin bayanin Suhairat yace.”Kin nuna min ke d’in ‘yar halak ce kuma ke ‘Yar gaske! (Wannan sunan na ‘Yar gaske daga bakin headmaster ya fito shine asalin fara kiranta da sunan) to tunda sannan ta ara ta yafa takewa kanta kirari da cewar ita d’in ‘Yar gaske ce har jama’ar gari suka dauka.

Headmaster ya cigaba da cewa” Baki da wani amfani a cikin makarantar nan tunda dai ba karatu kika zo kasuwanci kika shigo gashi har kin sumar da yarinyar mutane kina nema kiyi kisan akai a makaranta ki jaza mana masifa to daga yau na sallame ki daga wannan makarantar har abadah.”!!! Wasila ta dinga kuka tana bashi hakuri! amma yaki sauraranta, yasa aka daukowa Suhairat! paracetomal tasha da ruwa kana yace ta tafi gida ta huta, dama kuma tsakanin makarantar da gidansu babu nisa tsallaka titi za’ayi kawai su Wasila ne suke hawa mota.

Wasila da Camas! suka fita ransu idan yayi dubu ya ‘baci! Camas! tace”Wallahi nima nabar makarantar har abada shege dan iska kawai dama ya tsanemu.” Wasila tace”Camas! zuciyata kamar ta fashe haka nakeji tsinanniyar nan tayi min asara ta kusan dari hudu gashi tasa an koreni.” Hawaye ta share tana jin wata irin tsanar Suhairat cikin ranta…..Uwani najin labarin abinda ya faru tayi ta kutuntumawa! Suhairat ashar! tana tsine mata har da cewa sai taje gidansu ta ci mata mutunci.” Wasila ce ta tausheta tace kawai ta bari ai taci ubanta tunda har sumar da ita tayi, to jin haka yasa zuciyar Uwani tayi sanyi…….To ashe tsugune bata ‘kare ba, suna zaune da daddare sunyi tagumi babu abinci yunwa duk ta ishesu, sai ga sallamar dan sanda a bakin kofa……Itace ta le’ka sai kawai taga Suhairat a tsaye ita da wani saurayi da alama Yayan tane. Suhairat tayi saurin nuna ta tana fad’in “Itace yallabai.” Kafin tayi aune! ya fito da ankwa ya kama hannunta ya daure! kallonsu tayi bakinta na motsi ta rasa me za tace! Yayan Suhairat yace.”Sir me ake jira da itane.” Dan sandan yace.”Maza muje division sai kiyi bayani.” Uwani da rashida suka fito suna ihu! da tambayar abinda ya faru, cikin rashin kunya Suhairat tace”Ki tambayi ‘yarki.” Wasila ta kalli Uwani tace”Ku daina kuka! Babu matsala kuzo muje.” Uwani da rashida suka bi bayansu sai share hawaye sukeyi jama’ar unguwa na binsu da kallo.

Lokacin da suka shiga stion din D.P.O nan yana dube dube! ganin kyakyawan mata Uwani da yaranta sai ya dauki hankalinsa, yace.”Maza kwanci mata wannan abun me yake faruwa ne.” ? Dan sandan ya kwancewa Wasila Hannunta, sai kawai ta fashe da kuka tana fadin”Shikkenan D.P.0 daga anga mutum bai da gata a duniya sai ay ta tozartashi, Wallahi duk wanda ya cutar damu Allah zai saka mana.” D.P.0 yace.”Daina kuka kiyi min bayani.” Zama tayi kan banci tace”Ai bani ce zanyi bayani ba gatanan a tsaye ita da yayanta.” D.P 0 ya kalli suhairat da ita da yayanta yace.”Kuyi min bayanin abinda ke faruwa, Suharait ta soma inda inda! D.P.0 yace.”Daka gani kece baki da gaskiya ina ruwanki dan tana zuwa da kayan tallah ko kuma kece shugabar makarantar.”? Suhairat tayi fiki fiki da ido! yace.”Idan da hali ma sai nace ki bata tara tunda kin tozarta kin zubar mata da kayan sana’arta kuma kin sa an koreta daga makaranta, to amma a bayanin da kikayi min kince ta sumar dake to ai kece kikaja haka ina ruwanki da ita? Kije babu wani hukunci da za’ayi mata ke ya kamata ayiwa hukunci.” Suhairat da yayanta jikinsu yayi sanyi simi-simi suka fita daga gurin….D.P.O ya kalli Wasila yana murmushi yace.”Yan mata meye sunanki ne? saboda mutuncin da yayi musu yasa tace sunana Wasila nan ta bashi takaitaccen tarihinsu, ya tausaya musu sosai yace.”Kada ki damu kinji ko, ni da kaina zan mayar daku makarantar ku zana jarrabawa tunda lokaci ya kusa, komai zai wuce.” Ya dauki dari biyar ya basu suyi kudin mota…..Sai murmushi yake mata nan Uwani da ita kanta Wasilan su gane akwai alamun tambaya gurin D.P.O Yace.”Gobe da wuruwri ku shiryo keda kawar taku kuzo nan ku sameni zan mai daku makarantar.” Tace”To yallabai mungode.” Sallama sukayi masa kana suka fito daga gurin hankalinsu ya kwanta su zuwa division din ma yayi musu dadi tunda sun samu kudin da zasu siyi garin kwaki suci dama yunwa suke ji.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button