NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

“Eh din bani dashi! tafada tana mikewa tsaye ya kalleta cike da mamaki! Ta cigaba da cewa ” Me yasa tunda kasan halina kake ta’bani bana so bana son zama da kai dole ne, ni a sake ni naje na cigaba da harkokina bana son auran.” Ranshi ya baci sosai ya fitar da hannu a fusace! ya bata lafiyayyar mari! “Ashe baki da kunya Ni zaki tsaya kina fadawa wannan maganar? zagina zaki ko me? Kukanta ya sake yin ‘karfi tace” Ni ba zan zage ka ba amma nace bana sonka kawai ka sakeni dole ne.”!? Yaji wani bala’in takaici ya rufe shi, bai sake ce mata komai ba, ya fara hada ruwan wanka rashi idan yayi dubu ya baci tunda yake babu wanda ke iya kallon kwayar idonshi ya fada masa maganar da ya gadama kamar yarinyar, ‘Yar karama da ita ta iya yi mishi rashin kunya ya kuma ya kasa daukar mataki, Yana jin yanda take kuka da ‘kunkuni ya dinga ya’ki da zuciyarsa a kanta, ko kusa ko alama baya so yake dukanta, tausayi take bashi sosai yasan kuma ‘kuruciya ce ke damunta da tana da hankali da duk ba zatayi mishi wannan rashin kunyar ba….Ya gama wankan shi ya fice ya barta a toliet din…….

Littafin na kudi ne….!
Kika futar min da book ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
39
Da kyar ta samu tayi wanka ta fito daga toilet din idanunta jawur zuciyarta ba’kikirin wani irin haushin kanta da kanta takeji tana ganin da ta jajurce da dik haka bata faru ba, amma daga yau ta dauki alkawari ba zata sake bari ya kusance ba dole ne tayi taka tsantsan dashi……Har ya kwanta sai ya mike da hanzari ya fita, Garba na can zaune cikin wata rumfa dake harabar gidan ya hangi fitowarsa, da sauri ya mike ya iske inda yake, yana isa yace.”Garba ka dauki waccan motar da na fita da ita jiya ka kaita car wash yanzu.” Garba yace.”Okey sir.” Key din motar ya mika mishi ya koma ciki Garba ya nufi parking area din domin daukar motar…..Yana shiga dakin tana fitowa daga toilet din ko kallonta baiyi ba ya nemi guri ya kwanta dan bacci yake jo sosai, Ta zumbura baki tana watsa masa harara ta wuce….Wardorbe ta bude ta dauko riga da siket na kanti dake kusan kullum sai ya shigo mata da sabbin kaya shiyasa kullum cikin ‘bata su take yi, ba tare da tasa breziyya ba ta sanya rigar kana tasa pant ta zura siket din ta gyara gashinta ko mai bata shafa ba ta fice daga dakin tana me buga kofar da karfi! Bude idanunsa yayi yabi kofar da kallo, Ya maida idon ya rufe yana girgiza kanshi.

Dainig ta zauna ta hada break fast tanayi tana nazari itafa ta dauka fita zaiyi kuma ya nemi guri ya kwanta ga Camas! tace za tazo…..Bayan ta gama break fast din sai ta koma dakin. nan ta tarar baccinsa yayi nisa sosai ta lallaba a hankali ta dauki wayarshi kan stool ta zauna da sauri ta turawa Camas test!

Camas! Ya za’ayi ne guy nan fa bai fita ba gashi a kwance yana bacci

Camas na driving tana duba test din sai ta bata amsa kamar haka.

Aikuwa ganinan ma akan hanya dan na kusa zuwa

Amsa ta bata kamar haka.

Okey shikkenan bari nasan yanda za’ayi yanzu zan fita gurin masu gadin tunda bacci yake

Tana tura mata ta goge numbar ta ajiye masa wayarsa hijab din da take sallah ta zura ta kama hanya ta fita…..

Suna hango zuwanta duk sai suka sha jinin jikinsu, mussaman Wanda ta ta’ba mari kwanaki kas yayi da kanshi….Ita kuwa tayi bala’in shan kunnu ta karasa inda suke….Rige rigen gaisheta sukeyi ta amsa a ya tsine kana tace”Ina da bakuwa yanzu zata zo saboda haka tana zuwa ku bude mata kofa ta shigo.

Duk sukayi kas da kansu sanin da sukayi cewar abunda ta fad’a ba mai yiwuwa bane dalili yallabai din nan bai fita ba kuma bai jima da sake yanka musu winning ba, Ganin duk sun sunkuyar da kansu kasa ne yasa ta buga musu tsawa tana kallon Sunduki tace”Yana ga duk kunyi shiru ne, nace muku bakuwa ta zata zo ko baza ku bude mata bane.”?

Garba yace.”Madam! bamu ji daga bakin Mai gidan ba.” Hannu ta daga masa,”Kai Garba ka fita daga idona na rufe na lura duk kafi kowa za’kewa a gidan….Shi mai gidan ne ni kuma matar gidan ce ni wakiliyarsa ce saboda haka ba dole bane sai kaji daga bakinsa.”

Yace.”Madam! kiyi hakuri bari mu fara kiranshi a waya tukkuna.” Ranta yayi masifar baci! a hasale tace.”kar ka ma wahalar da kanka bacci yake yi.” Yace.”Okey to idan ya tashi sai muyi maganar.” Ji tayi kamar ta gaura masa mari….Camas ! tayi parking din motar ta ta firo tana dan kwankwansa gate din, Garba ya bude karamar kofa, Yana lekenta ya ganeta sarai babbar kawarta ce, Camas ta tawo gadan gadan zata shiga, Garba ya mai da kofa ya rufe, sai ta tsaya turus! Wayar ta ta fito da ita tana kiran numbar da Wasilan ta kirata da ita domin ta shai mata……Wanda yayi dai-dai da shiga Wasila dakin a fusace! zata tashe shi daga baccin sai kiran wayar ya shigo ta dauka, da sauri ta fita palor…..”Camas! ‘Wannan dan iskan Garban ya kafe kai da fata sai da izinin mai gidan zaki shigo karki damu yanzu kome za’ayi za’ayi zan tashe sa a bacci ki dan jira minti biyu.” Camas! tace.”Okey to shikkenan.” Kashe wayar tayi ta koma dakin….Bacci yake sosai da alama kuma yana jin dadin baccin ta tsaya kanshi as’useul “Ka tashi ina da magana da kai.”! ka tashi ina da magana da kai! kalmar da take ta faman nanatawa kenan…..Ya bude idanunsa da sukeyi masa mugun nauyi, ya ganta tsaye ‘kerere a kanshi, ranshi idan yayi dubu ya ‘baci! har yaushe yarinyar nan zata daina yi masa kutse ne!? ya sha fad’a mata yana da matsala idan yana bacci ba’a tashin sa amma ta’ki ji! Hannu bibbiyu ya dora saman kanshi yana jin wani irin jiri da hajijiya, bakinsa ya shiga motsawa da alama salati yake yi da kiran sunan Allah, Sai taji ya dan bata tausayi, kadan, ta dan tsira masa ido tana kallon yanda bakinsa ke motsi yana sake rintse idonsa, kafin ya bude idon akanta

Saurin sunkuyar da kanta tayi saboda ganin yanda kwayar idonsa ta wani burkice kamar ma ba ita yake kallo ba, mikewa yayi tsaye! tace” Ina so in magana da kai ‘kawata ta kawo min ziyara sun hanata shigowa wai sai ka basu umarni.”

Ba tare da yace mata komai ba ya kama hanya domin barin dakin, so yake ya bar mata dakin tun kafin ta kashe hi. Da sauri ta tari gabanshi……..Aikuwa ya wanke fuskarta da mari mai shiga jiki, tayi saurin dafe kumatunta ba tare da tsammani ba! Tureta yayi ya bude kofa ya fita, Hawaye ya wanke mata fuska a fusace! tabi bayanshi, ” Sai dai kuma me? Bakin kofar daya bedroom din taga ya yanke jiki ya fad’i!! A gigice ta nufi inda yake tana tatta’ba jikinsa, Ya rike hannunta guda yana kokarin aro jarumta ya mike, tsaye, sabida yanayin karfin nasu ba daya bane yasa ta afka kansa, sai ya koma ya kwanta kasan ties tayi kwance a jikinsa, tana jin yanda numfashinsa ke fita da sauri da sauri….
Kimanin minti goma suna a haka, kafin taji ya dauketa cak! daga jikinsa ya ajiye ‘kasan gurin ya mike kallo ta bishi dashi har ya bude bedroom din ya shige tare da mai da kofar ya rufe…..Ta jima zaune a gurin kafin ta yanke shawarar binsa….Yana kwance rigingine ta same shi yana lumshe ido so yake ya koma baccin amma yaki zuwa, Simi-simi taje ta tsaya kanshi….Ya bude idonsa yana watsa mata harara, Da sauri tace”Don Allah ka taimaka kace su barta ta shigo kaji.”! idanunsa ya mayar ya rufe, yana jinta sai magiya take masa harda kuka, idanunsa a rufe yace “Je ki dauki min wayata.” Da sauri ta tafi….Ta shigo hannunta rike da wayar….Yana dubawa yaga miss call har guda uku kuma bai san numbar ba bai damu ba, ya nemi numbar Garba ya bashi umarnin budewa Camas! kofa….Yana gama wayar ko godiya ba tayi ba ta buge sikit dinta ta fuce daga dakin……Ko kalli bai bita dashi ba saboda tsabar yanda yake jin haushinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button