NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

‘Bata rai yayi yace.”Tashi kije ki gyara min daki.” Ta kalleshi cikin wani irin yanayi Yace.”Ban son kazanta bana shiri da kazamin mutum ina amfanin kin gyara jikinki baki gyara makwancin ki ba to daga yau kar ki sake kwanciyar min a daki ki dauki daya cikin dakunan dake palon nan bana son kazanta.”

Ranta ya ‘baci dajin irin bakaken maganganun da yake ya’ba mata sai dai ta daure kawai saboda tana neman biyan bukatarta, ba tace masa komai ba ta mike a hankali ta nufi dakin….Bayanta yabi da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta kwana biyu yaga ta soma yin sanyi Allah yasa ta d’ore…..Yana kokarin shiga sukayi karo ta dauko plate din dazu zata fita dashi……Dauke kansa yayi ya wuce Lokacin kirjinsa ya gogi nata yaji wani irin yanayi a jikinsa sam! baya so yanayin da yake ji a jikinsa yayi tasiri kan yarinyar shiyasa yanzu ko kallonta bai fiye yayi dan yaji haushin Allah ya isan da tayi masa,

Tana shiga dakin ta ganshi ya sunce kayan jikinsa yana kokarin daura towel tayi saurin dauke kanta ta nufi toilet da sauri gabanta na wani irin faduwa! Manta abinda ya shigo da ita toilet din tayi sai ta hau duru-duru!!! can taji alamun zai shigo tayi saurin Kwance pampo tana wanke fuskarta sai sannan ta tuna abinda ya shigo da ita, can wani guri ta nufa cikin toilet din dai ta dauki tsinsiyar laushi da makwashin shara, kanta a ‘kasa zata fita suka buga karo yana daure da towel iyakacin sa ku’gunsa kirjinsa a waje! gigicewa tayi har sai da yaso ya fahimci hakan! tayi saurin ra’bewa tayi zata wuce ya matse hanyar yana yi mata wani malalacin kallo….Kas da tayi da kanta kamar munafuka duk ta muxanta mutukar za taganshi a haka! babu suttura wata irin shakkarsa takeji da tsoronsa, “Yau waye yazo gidanan.”!? Ya fadi maganar yana tsareta da idananunsa dake mutukar saukar mata da kasala da mutuwar jiki.

‘Yar uwa ga shawara: Idan kina dauraye gabanki da ruwan sanyi bayan kun gama mu’amula ta aure da mijinki (sex) to ki daina domin yin hakan yakan iya janyo miki matsala babba, duk sanda kuka gama mu,amula ta auratayya da mijinki to ki samu ruwa mai dumi ki wanke gabanki tsaf! kana ki daura wankan janaba! kar ki saba kwanciya da janaba a jikinki komai rintsi idan kina da toilet a daki ki tanadi ruwanki idan baki da toilet a daki to kiyi addua dai-dai gwarwado Allah zai kare ki da kariyarsa ki fito ki tsarkake jikinki…..Ke kanki sai kinfi jin dadin hakan, Barin janaba a jiki na haifar da matsala babba na farko nan da nan idan an shiryo miki wani sharrin ya same ki a take saboda rashin tsarki, Na biyu shaidanu zasu dameki wannan najasar dake jikinki suma zasu zo su dora miki tasu ki tashi da ciwo ko dai wani abu makamancin haka……Allah yasa mu dace.

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book ke da Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
30
Kasa hada ido tayi dashi ballanta ta bashi amsar tambayar da yake mata gabanta faduwa kawai yake yi tana adduar Allah yasa ba wani ne ya fada masa cewar Camas! tazo gidan ba, Hannunsa yasa ya dago fuskarta dake sunkuye ya kura mata idanunsa, duk sai yaga alamun rashin gaskiya a tare da ita,Yace.”Dazu Kawunki wanda ya bani auranki ya kira ni a waya ya fada min wata magana, Idan kin san maganar gaskiya ce cewar mahaifiyarki tazo gidanan domin ta lalata miki aure to tun wuri ki hanata zuwa gidana, idan ba hakaba zan dauki mataki a kanta a da na aureki ne domin in wulakantaki kana kuma na karya alkadarinki na sake ki, to sai daga baya kuma na janye wannan ‘kudirin nawa saboda darajar wannan dattijon mutumin wato Mai allo, yafi gaban na watsa masa ‘kasa a ido ki godewa Allah Kawunki na sonki da alkairi duk wannan abun da yake nunawa a kanku kauna ce ba tsana ba, kinci albarkacin masu albarka zaki zauna tare da Ahamdu babu saki a tsakaninmu mahaifiyar ki karta ‘kara zuwar min gida da manufa mara kyau! zan sanya su Garba su dauki mataki a kanta.”

Fuskarta ta fuxge dake tafin hannunsa tana watsa masa harara kwalla ta cika kwarmin idonta, bakinta na rawa tace”Mahaifiya ta kake kokarin ciwa mutunci a gabana.”!? Yace.”Meye abin cin mutunci anan gaskiya ce na fada.”
Girgixa kanta tayi tana kokarin had’iye wani ‘kululun ba’kin ciki da yazo ya tokare mata a ma’kushi! Tace.” To kaje ka fad’awa wanda ya fada maka cewar mahaifiyata tazo gidanka cewar Shi din azzalimi ne kuma ni banga gatan da yayi min ya zalince ni da ya had’ani aure da kai mugu mai ba’kar aniya.”!

Cike da d’umbin mamaki yake kallonta, ashe rashin kunyar yarinyar har ta kai haka kamar wannan mutumin take kira da azzalimi me yayi mata na zalinci ta kira malam mai allo azalimi shi ta kirashi da mugu mai ba’kar aniya…..Al’amarin ma dariya ya bashi ya fahimci taji ciwon maganarshi kan mahaifiyarta, ya girgiza kai kurum yana kokarin shiga toilet din ba tare da ya tanka mata ba, taso yace wani abu daga nan ta zazzageshi in yaso ko mai zai yi mata sai da yayi mata, Duk lalacewar Uwa uwace tana masifar kishin iyayenta mussaman Uwani da duk wahalarta a kansu ta kare shiyasa suke fad’a da mai allo mutukar zai zagi Uwani a gabanta sai tayi masa rashin kunya sam basa shiri dashi ta gane kuma munafiki ne shine ya tunzura Ahamdu yazo yana kokarin zagar mata uwa.” Hawayen da take ta kokarin dannewa sunki dannuwa dole suka fara zuba, Ta juya yayin da yake kokarin hada ruwa miyau! ta tofa masa a bayanshi, Yayi saurin juyowa yana kallonta, shi ya d’auka ma tuntuni ta fita ashe tana tsaye, hawaye ya gani na karakaina a fuskarta, shifa bai ga abin kuka da damuwa anan ba, ai bai fadi wata mummunar magana kan mahaifiyarta taba, Had’a ido sukayi tace”Allah ya isa na Allah ya bimin hakkina.” Ya shiga mamakin Allah ya isan da take masa, Nufar ta yayi tayi kamar ta gudu sai kuma ta yanke shawarar tsayawa wallahi ya daketa sai ta murd’e masa mazakuta! ta kasheshi kowa ya huta shawarar data yanke kenan….Koda ya ‘karaso inda take sai taga akasin haka, dankwalin kanta ya fuzge ya mika mata fuska a hade yace.”Goge min kazamin Yawun ki da kika tofa min.” A hargitse tace.”Wallahi rantsuwar dan musulmi ba zan goge ba ko kasheni za kayi sai dai ka kashe.”! Ya girgixa kai tare da fadin”Ni dai na fad’a miki dan na lura kin ji zafi kan maganata okey Yanzu dai bani da lokacin ki amma ki kiyaye shiga hannuna zaki gane baki da wayo.” dankwalin yasa ya goge miyau din ya jefa mata a fuska, taja tsaki mai karfi ta futa daga toilet din, rashin a ‘bace yayi wanka ya fito……Still kuka ya tada ta tanayi sosai idanunta sunyi jage jage da hawaye, sai ya dan ji tausayinta ya kamashi, babu shakka tana da kishi kuma duk rashin kunyarta tana martaba iyayenta, shi dai yasan bai fadi mummunar kalmar da zata tada mata da hankali ba amma ta zauna tana kuka, hakane shima nada kishin iyayensa yana gani aka taba martabarsu sai inda karfinsa ya kare, Kaya ya sauya ya fesa turare hade da daura agogo ya dora hula saman kanshi ya kama hanya ya fita daga dakin yana jin shashshekar kukanta har cikin dodon kunnansa.

Ta jima xaune a dakin tana wannan kuka tana kuma tunanin yanayi na rayuwa, a duniya dai babu wanda yafi saurin ‘kaskanta sai talaka idan baka da kudi sai a zage ka a tozarta ka a gabanka yaushe Uwani tazo gidansa da har zai tasa ta a gaba yana cin mutuncinta, Tunda suke ‘yar tsama dashi bai ta’ba ‘kuntata mata irin yau ba ta dinga jin wata iriyar tsanarsa na d’arsuwa a cikin zuciyarta shi kanshi malam mai allon mugun haushinsa takeji a ganinta duk shine yake ‘kara rura wutar al’amarin……..Da kyar ta tashi tayi sallah magariba ta zauna har aka tayar da isha’i ta gabatar da sallahr sai ta kwanta kan daddumar bakin ciki duniya ya taru yayi mata yawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button