NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Tsaf malam Mai allo ya shirya cikin manya kaya yayi wa matarsa Bitan sallama dama duk abinda ke faruwa ya shaida mata saboda ya yarda da ita da nutsuwarta Bitan macace mai hankali da sanin ya kamata, fatan alkairi tayi masa gami da dawowa gida lafiya.

Mai allo bai sha wahala ba gurin zuwa gidan Kawu Madu dake Pataskum dan Wasila tayi masa kwance sosai kuma sai da ya tambayi Madu mai itace ya sake tabbatar da cewa shi d’in ba ‘boyayye bane.

Allah ya taimaka Kawu Madu nan bai fita ba yaro ya shiga gidan ya shaida masa yayi ba’ko……Kawu Madu na fitowa yaga fuska irin ta Yahuza me rasuwa.
Yace.”Hala dai kaine Yayan Yahuza mijin Uwani mahaifiyarsu Wasila ko.”
Mai allo ya washe baki

nsa yana mi’ka masa sannu yace.”E kwarai nine malam ashe ka shaida ni.”
Kawu yace.”Haba malam ai duk wanda yaga fuskarka yasan kai dan uwan Yahuza ne ai kuna kama sosai.
Mai allo yace.” Masha Allah masha Allah! Kawu madu yace.”Bisimillahi malam shigo ciki.” Mai mai allo yace”Da mun zauna ma a zaure magana ce mai muhimanci nake tafe da ita.
Kawu yace.”To babu damuwa bari na dauko abun zama.” Yay saurin shiga cikin gidan yana washe bakinsa,
Mai allo ya shiga soron gidan ya tsaya yana jiran fitowarsa.

Sai da suka sake gaisawa suka nutsu tukkuna kafin Mai allo yay gyaran murya yana fuskantar Kawun yace.”Magana ce nake tafe da ita Malam Adamu ina fatan kuma zaka dauki maganar tawa da mahimanci.” Kawu Yace.”Ina sauraranka Malam Mai allo yace.”Nazo nan ne da niyyar auran Uwani ina fatan amincewarka.”.

Kawu madu yace.”Alhamdullhi! kai amma naji dad’i wannan magana da kake tafe da ita dama ko jiya sai da mukayi magana da ita dake nan d’in ma tana samun zawarawa sai nace to ta futar da miji tayi aure sai ta nuna min duk cikin zawarawan dake sonta babu wanda yay mata a cikinsu, amma jikina na bani kai ba zata watsa maka kasa a ido ba ko banza tasan “yayanta sun samu Uba nagartacce.”

Mai allo yace.”Nayi istahara dangane da al’marin kuma alhmdullhi Jikina na bani akwai alkairi shiyasa nayi gaggawar zuwa domin na sameta mu tattauna kuma ku sani insha Allah gobe zanje in samu Kawunta na can kano idan mun tsaida magana da ita.”
Kawu Madu yace.”Hakan yayi kyau malam babu shakka idan Al’amarin ya ‘kullu ni zanfi kowa farin cikin hakan.
Mikewa yay ya nufi cikin gidan yana fadin'”Bari na kira maka ita ku tattauna.

Koda Kawu madu ya shaidawa Uwani zuwan Mai allo sai ta shiga mamaki sosai jikinta yay sanyi tun bataji abinda yake tafe dashi ba, hakika yanzu take nadama gami da dana sanin abinda ta dinga yi masa a baya.

Ta dauki mayafi kalar atamfar dake jikinta ta yafa a jikinta ta fita zauran…..Cikin nutsuwa take masa barka da zuwa tana sunkuyar da kanta kasa, sosai Mai allo yayi mamakin nutsuwarta, zauran yay shuru na minti biyar kafin mai allo yay gyaran murya a hankali yace.”Ina fatan Kawu Madu ya fada miki abinda yake tafe dani.”
Uwani ta dago kanta tana kallonsa, haiba da kwarjininsa ya sanya ta sunkuyar da kanta kasa a hankali tace”Bai fada min ba.”
Mai allo ya sakeyin gyaran murya a karo na biyu yace.”Wata magana ce mai muhimanci nake tafe da ita ina fatan idan kikaji zaki aminci da ita.”.
Tace.”Malam ka fad’i ko wace irin magana ce ina sauraranka.”
Mai allo yace.”Nazo nan ne da bukatar auranki.” Uwani gabanta ya yanke ya fadi sai ta kasa dago ido ta kalleshi.
Mai allo yace.”Nasan zakiyi mamaki ko? to ki sani ba’a mamaki da ikon ubangiji tabbas wannan auran namu akwai albarka a cikinsa a yanzu babu abinda nake bukata daga gareki sai amincewarki.”

Uwani ta jima kanta a kasa ta kasa cewa komai dan har Malam din ya cire tsammanin za tayi magana, sai kuma yaji tace”Babu komai malam na amince Ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkairi a ciki, sannan don Allah ka gafarce ni kan abubuwan dana dunga yi maka a baya.
Mai allo yay murmushi farin ciki ya cika masa zuciya yace.”Alhamdullhi Naji dadi sosai da kika aminci kai tsaye ba tare da mun kai ruwa rana ba, ni kuma nayi miki al’kawarin rike ki tsakani da Allah da manzon Allah dik wani abu da kikayi min a baya na yafe miki Allah ya yafe mana baki daya.”
Uwani ta amsa da ameen Yace.”Sati biyu kacal nake so a daura aure ko ya kika ce.”?
Murmushi tayi cike da kunya gami da jin nauyinsa tace”To shikkenan Allah ya nuna mana.”
To kafin malam ya tafi sai da suka tsayar da magana shi da Kawu Madu kan cewa kafin cikar kwanakin da suka d’iba zai kawo sadaki da duk abinda ya sawwa’ka.” Kawu Madu yace.”Kada ka takura kanta malam kawai ka kawo sadaki a daura aure.”
Malam yace.”A’a dole sai yayi mata suttura da sauran abubuwan amfani.” Cike da girmama juna sukayi sallama Malam ya wuce ya tafi zuciyarsa wasai yana jin wani irin so da kaunar Uwanin na ratsa jikinsa.


Masha Allah Addua bata bar komai ba kuma hausawa nacewa duk abinda hakuri bai baka ba to babu shakka rashinsa ba zai baka ba

, alhmdullhi gidan Amadu yayi kyau komai na tafiya dai-dai dukaninsu sun kwantar da hankalinsu suna kula da junansu kamar zasu cinye kansu, mutukar na gida suna daki a kulle suna soyyaya baby Zahra kam har ta saba da Rashida in ba nono zata sha ba baka ganinta gurin Wasila, al’amarin Zeey kuwa tun ranar data kira waya ta haddasa musu rigima bata sake kira ba saboda sosai taji zafin zagin da Wasila tayi mata, tayi ta tsammanin ko Amadun zai kirata taji shuru bai kirata ba, nan ta gane ashe itace take haukanta dole tilas ta sanyawa zuciyarta dangana ta rubuta masa text wanda lokacin da ya karanta test din sai da ya tausaya mata so masifa ne, shi kam yana ganin ko ya aureta wuya zata sha ko bakin ciki ya kasheta dan ba zai iya kwantata da Wasila ba, kwata kwata yanzu babu wacce take gabansa sai Wasila da babynta.

Yana tsaye tsakiyar daki yana fesa turare ta shigo dakin tana zum’bura bakinta, taki kallonsa ta wuce taje ta kwanta kan bed tana hawaye, tun jiya suke ta tafka rigima tana so taje su gaisa da Mai allo kana su wuce pataskum amma yayi biris da maganarta idan ta dameshi yace zasuje sai an kwana biyu har yanzu kwana biyun ba tayi ba.

Ganin tana kuka sai yaji babu dadi yazo ya tsaya kanta yana tambayarta menene? cikin kuka da shagwaba tace”Lokacin da Hajja take nan naji tace maka ka dinga bari muna zuwa gaishe da mahaifanmu amma yanzu nayi nayi da kai ka’ki barinmu, ni wallahi gurinta zan kai ‘kararka.”
Ya zauna gefan bed din yana dariya dan maganarta dariya ta bashi yace.”Ke! ni zaki kai ‘kara.”? Tana goge fuska da turo baki tace”To ai kana jin maganarta watakila ita idan tayi maka magana ka amince.” Ya sasauta fuskarsa yace.”Ba hanaku zuwa nayi ba, kinga Rashida jarrabawa zasu fara ranar Monday kuma tare zakuyi keda ita shine dalilin da ya sanya na dakata tukkuna kuyi jarrabawar sai muje tare nima ai ina so mu gaisa da Malam d’in.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta rike hannunsa tana shafawa tace”Shikkenan Allah muna gama jarrabawar nan ko kwana daya baza mu kara ba zamu tafi.”
Ya d’age mata gira yana dan kashe idonsa yace.”Wai idan kin tafi ni ya zakiyi dani kin san dai kin saba min da abubuwa da yawa.” dariya tayi mishi tace”Kayi zamanka ka huta dama ai wataran cewa kake na dameka.”
Yace.”Ba wannan ba, kwana nawa zakiyi.” Da hannunwanta tayi masa alama wai kwana ashirin zatayi.”
Yace.”Bana jin zan bari ki kwana Madam muje mu dawo a rana daya……Rungumeshi tayi tana cikwikwiya masa shaddar jikinsa tana kuka tace.”A’a wallahi ni kwana daya be isheni ba.”
Cikin mutuwar jiki da kasala ya cireta daga jikinsa yana duba jikinsa yace.”Duba saboda sangarta nayi adona kin ‘bata min jiki, ni dai na gama magana ba zaki kwana ba.”
Da gudu ta d’ane jikinsa tana kuka “Wallahi sai ka amince nayi sati daya.” Abinda take fada kenan tana cusa fuskarta a kirjinsa.
Jikinsa ne ya mace suka zube ita dashi kan bed din tayi kwance a saman kirjinsa tana masa dukan wasa sai kuka takeyi, rungumeta yay jikinsa na rawa ya shiga sumbatarta ta ko’ina…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button