NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Uwani tace”Kuma fa hakane maganarki Wasila duk ranar da governor ya gane baki da a’kida to kashinmu ya bushe gwara ki tsaya a bigire guda mussaman yanzu sune ludayin su yake kan dawo zamu kwashi roman da mukarad’iya gwara mu tsaya da kafafunmu kafin ya sauka.

Wasila tace”Ashe kin gane abunda nake nufi dan haka bani kudin na ajiyesu taimakon da yayi mana kuwa shine yayi niyya ‘yan kudinsa baza su sanya ni na sauka daga a’kida ta ba.” Uwani ta mika mata kudin ba dan ranta yaso ba sai dan ba yarda zatayi da ‘yar tata.


Tunda suka doso layin suke ganin cincirindon mutane wasu na shiga wasu na fita ga ‘katon gate din da ya zama security ga estate din a bude jama’a sunja dogon layi sai kar’bar tallafi sukeyi layin mata daban na maza daban…..Camas! tace”Kawata me yake faruwa ne naga mutane sunja layi.” Wasila ta gyara ni’kab din dake sakeye da fuskarta tace”Zai wuce kamfen yake domin yaudarar al’umma amma dai bari mu tambayi wannan matar.”

“Baiwar Allah dan Allah me akeyi anan gurin.”? Matar ta tsaya tana washe baki tace” Tallafi mai girma Governor mu na gobe yake raba mana mata dubu goma maza dubu ashirin.”

Wasila tace”Ke kin samu kenan.”? Cike da farin ciki matar tace”Na samu mana gasu ma nasa a cikin jakata, zuwa zanyi na siyo gyada buhu biyu mu dinga soyawa da yara na kafin muga abunda Allah Zaiyi.”

Wasila tayi murmushi tana jan tsaki tace”Kin san wani abu.”? matar ta girgiza kai….”Zan baki baki dubu ashirin yanzu kije ki watsa masa kudinsa kice baki so kudinsa basu isa su siyi ‘kuri’arki ba mulki kuma sai dai yaga anayi.” Matar tabi Wasila da kallon mamaki.! Wasila tace”Ko dai kudin da na fada sunyi miki kadan ne to na kara miki talatin akai sun zama hamsin nasan dai zasu isheki kija jarin ko wace sana’a ce.”

Matar tace”Bana son roman baka yarinya in fara gani a’kas! tukkuna.” Wasila ta zaro jakarta dake rataye a kafada ta lissafa kudi dubu hamsin cif tace kin gansu a hannuna kina aiwatar da aikin dana saki zan baki su.

Laraba na ganin kudi dumus a hannun Wasila sai ta gigice! tace”To yanzu ya za’ayi na shiga gurinan akwai ‘yan sanda sosai a gurin kuma suna ganin shige da ficen jama’a kana suna gane wanda ya fita da wanda ya shiga kuma kina ganin idan na aikata hakan ba za’ayi min komai ba.”

Wasila tace”Karki damu malama muje tare zamu sanyaki a tsakiya ba zasu gane ki ba.” Laraba tace.”To ku muje.” Kai tsaye suka durfafi kofar shiga gurin jami’an tsaron dake tsaye a gurin sukace su tsaya wani abu suka kara a jikinsu minti biyu sukace su wuce ciki…….Wasila da Camas! suka kama layi kamar gaske! Laraba kuma ta mike hanya dan isa inda yake tsaye……….Tana zuwa ta watsa masa kudinsa a jikinsa da karfi tace.” Bama so bama yi! wa ‘yan nan ‘yan kud’in naka basu isa su siyi kuri’armu bamu ba!. Ai sai gurin ya kaure da hayaniya Garba da Hadi sukayo kan laraba Ahamad dake tsaye cikin dumbun mamaki ya hanasu dukanta, su kansu Police din dake tsaye a gurin Sunyi mamakin matar amma ya hana a ta’bata komeye dalili oho.”

Ya Kalli Garba a nutse yace.”Zo ka tsaya ka cigaba da raba musu.” Garba ya tsaya inda yake shi kuma ya kalli Laraba dake tsaye jikinta yayi sanyi kalau yace.”Baiwar Allah bance dole ki za’be ni a matsayin d’antakarar ki ba wannan kudin da nake raba muku duk karshen wata inayi ne saboda Allah ba da wata manufa fa ra’ayinki ne ki za’be ni ko ki za’bi abokin gamayya ta ni nasan ba zai iya siyan ‘yanci ki ba nafi so duk wanda zai za’beni ya za’beni saboda Allah da kishin kansa da kuma ‘kasarsa….”

Laraba ta fashe da kuka tana fad’in”Kagafarce ni yallabai! wallahi bayin kaina bane roman baka akayi min wata yarinya ce yanzu tayi min alkawarin zata bani dubu hamsin idan na aikata maka haka yanzu kuma wad’annan maganganun da kayi sunyi bala’in kashe min jiki don girman Allah ka gafarce ni.”

Ahamd ya sauke ajiyar zuciya shi sam baiji zafin matar ta saboda yasan irinsu siyansu ake da ‘yan kud’i kad’an! saboda an san shi talaka bukatarshi kudi ko ta halilin kakane zai iya siyar da ‘yanci akan sabulu ko omo ko sukari.

Yace.”Yanzu zaki iya nuna min inda yarinyar take.”? tace”Kwarai kuwa Yallabai ai gatacan ma ta kama layi.” Ahamd ya goya hannunsa a baya suka mike dogon layin dake jere da mata har suka inda su Wasila suke…..”Gata nan Yallabai.”! Laraba ta nuna Wasila dake tsaye fuskarta da ni’kabi…..Zatin ta kawai ya kalla ya gane ta ya d’an tsirawa idanunta kallo dake ni’kab itama ta sama ido suna kallon juna…..Ya d’an juya a nutse ya kira police yana karaso yace.”Zura mata ankwa ka kai min ita cikin gida.”

Camas! tace”Innallihi wa’ina ilahi raji’un! Jama’a me mukayi baiwar Allah me tayi miki zakice itace haka kawai dan sharri! Yalla’bai wallahi ba ita bace hasali ma mu yanzu muka shigo gurin kuma ai ba ita kadai ce mai niqab ba a gurin.” Ahamdu ko sauraranta baiyi ba ya bar gurin.

Camas! ta dinga ihu! tana zagin Laraba Wasila ta dinga turjewa tana fad’in”Me nayi muku wannan sharri tayi min bani bace wallahi Police din yace.”Wallahi idan bakiyi shiru ba zan fuxge wannan niqab din dake fuskarki in yaso kowa ya ganki munafuka kawai.”

Jin abinda Police din yace ne sai ta daina turjewa saboda bata so ya cire mata niqab jama’a su ganta akwai tozarci sai kawai ta hau fuffukar ‘karya da fad’in”Ai gaskiya daya ce kuma wanda ya zalinci wani Allah yana gani haka kawai saboda rashin adalci za’a sanya min ankwa sai kace ‘barauniya ko kuma wacce tayi kisan kai!! kuma a haka ake cewa za’ a iya mulki wannan ba adalci bane wallahi duk wanda ya shiga hurima na barshi da Allah.”!!!

Dan sanda kuwa ya tasa ‘keyar ta tana tafiya tana surutai da farfad’ar bakake maganganu masu harshen damo wanda wanda ake dominsa ya sani masu hankali ma a gurin sun gane da wanda takeyi….Angizata yayi cikin gate din yayi ya mayar da ‘kofa ya rufe……Ta waiwaya bayanta babu kowa har masu gadi duk suna waje gefen bainci masu gadi ta zauna gabanta na fad’uwa sai yanzu jikinta yayi sanyi da al’amarin, dole ta cire tsoro da shakku a kan abunda zai faru ita dashi tayi al’kawarin ba zai ta’ba samun nasara a kanta ba…….Can ta hango shi ya fito daga wata iriyar kofa ta gilas ya durfafo inda take zaune gabanta ya dinga duka yana daka! mussaman ganin yanda fuskarsa take had’e tamkar hadarin da ya daf da zubar da ruwa.

‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi

 *NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300   Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176  sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

 _*Babu mahalu'kin da ya isa yayiwa mutum abunda Allah bai masa ba, bama nema gurin kowa! gurin Allah muke nema Allah ka yi mana ba dan mu ba*????????_

~~
Page d’in naku ne
HAUWA S ZARIA
(Mmn Uswan)????
MAMAN MAMY
(Shalele)????

Free Pege11
Ganin ya kusa isowa inda takene ya sanya tayi maza ta yi ‘kasa da kanta gani tayi ya kara wani kwarjini da kamala adduar neman rinjaye ta soma sai dai duk wacce ta dauka sai ta subce ta kamo waccen ma ta subce duk sakamakon tsayuwarshi a kanta ga masifar kamshinsa ya rikirkita mata lissafi.

“Cire wannan ba’kin abun na fuskarki.” Yafad’a cikin wata iriyar murya…..Ta dago kanta tana kallonshi, “Kamar yaya na cir…..Kafin ta ‘karasa ya fuzge niqab! din ya jefar, tayi saurin kauda kanta gefe.

Hannu ya mika yayi kamar zai juyo da fuskarta sai ya fasa yace.” Juyo ki kalleni ina son muyi magana dake.” Sai da ta dai-dai ta nutsuwarta tukkuna ta juyo tana kallonshi……..Sun kai kimanin minti uku suna kallon juna kafin ta dauke kanta tana wani ya mutse fuska.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button