NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wasila kuka take sosai tana ‘kara kulatar malam mai allo a ganinta duk shine silar fadawarta cikin wannan halin da take ciki, haka kawai zai kama ya daura mata aure da wanda bata so alhalin bashi ke ciyar da ita ba kuma bashi ke shayar da ita ba asali ma kullum cikin aibatasu yake ita da mahaifiyarta ta tabbata kudi Ahamdu ya sakar masa shiyasa ya rude ya yanke mata wannan hukuncin tayi al’kawarin insha Allahu daga shi har Ahamadun sai ta basu kunya auran da suka daura dashi da babu duk daya domin tananan a kan bakanta, sai ta kufce daga gidan.

A jikin d’an yan zogale akwai Wani abu kamar fure zaku ganshi saman zogale to wannan abin ba karamin sirri bane a tattare da ‘ya mace yana mutukar saukar da ni’ima nan take! duk bushewar ki da rashin ni’imar ki idan kina tauna wannan abun na jikin zogale kina matsi dashi sai kin zama ‘korama! ‘yar uwa ki gwada ki gani zaki bani labari! Ki cire ki sa a bakin ki ki tauna yayi laushi sai ki cusa a gabanki kina zaune a inda kike zakiji wandonki ya jik’e yini zakiyi kina tsarki, amma kuma ‘yar uwa ki yawaita tsarki da ruwan d’umi domin in kina da ni’ima! kuma a bude kike kinga anyi biyu babu namiji naso yaji gam!gam! sannan yaji ruwa na gudana a jikinki inda yana sanya jijiyarsa a jikinki zai shi tamkar a cikin teku…..Wannan sirri na baku saboda kauna, ki gwada ‘Yar Uwata????????‍♀️

Kika futar min da book! Na barki da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
07084653262[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
28
Da sassafe Uwani ta shirya tsaf lokacin ma Rashida bata tashi ba ta kama hanyar Garin garko….lokacin da ta isa garim Malam mai allo na tsangayarsa, ta iske matarsa bitan tana aikace aikace kamar yanda ta saba, Bitan ta shimfida mata tabarma tana mata barka da zuwa Uwani sai cika take tana batsewa tana fadin”Ni fa ba zama nazo ba nazo gurin mai gidanki.” Bitan tace.”Ayya aikuwa yana tsangaya tare da almajirai sai bayan sallahr azuhur zai shigo! Uwani tayi shiru tana dan tunani, Bitan ta kawo mata ruwa cikin kwanan silva ko kallon ruwan ba tayi ba ta mike tana fadin”Ni zanje tsangayar tashi domin inyi abinda zanyi in tafi.” Bitan! tace”Haba Uwani idan hankali ya ‘bata nutsuwa aka sawa ta dubu shi kiyi hakuri ki zauna mana har ya shigo gidan sai kuyi maganar ni nasan abinda yake tafe dake.
Da fadin wannan magana ta Bitan Sai Uwani ta hau masifa dama ‘kiris take jira tace”Ashe kin san abinda ke tafe dani amma kike cewa na zauna wato tare dake aka hada baki aka daurawa ‘yata aure ba tare da na sani ba ko? kunga kudi kun rud’e daka ke har Mijin naki gashinan lokacin kankani har naman wuya kinyi to wallahi da sake kamar yanda malam ya tozartani ya wulakantani ya nunawa duniya ni ban isa ba to nima sai na kunyata shi gaban almajiransa.

Bitan tace”Ki daina wannan maganar Uwani itafa rayuwa da kike ganinta ‘yar sannu ce wannan balo’kokon da kikeyi duk a banza tunda dai aure an riga an daura ai magana ta kare kuma kina maganar munga kudi karya kikeyi mu ba makwadaita bane abin wani bai dame mu kije ki tambaya kiji yanda al’amari ya faru.”

“Babu wanda zan tambaya aini ba yarinya bace da zaki zaunar dani kina min wannan maganar na dauka wallahi idan nice na haifi Wasila sai nasa ta kunyata mijinki tunda bai san ya kamata ba.”

Bitan! tace”Ai sai kije kiyi tayi mai dora ‘yayanta kan turba mara kyau kece zakiyi nadama mara amfani.” Uwani ta zura takalmata tana fadin” Ke da mijinki ne zakuyi nadama amma bamu ba aure kun daura saboda kuna samu kwabo da dari to ba zaiyu ba sai na kwance wannan auran wallahi.”

Bitan! ta bita da kallo cikin tsananin mamaki! tabbas babu abinda yake damun Uwani sai jahilci a irin wannan zamani ‘yarki ta auri mutum mai hankali kamar Ahamdu amma kice sai kin warware auran tabbas gaba tana tare da nadama.

Uwani na fita kai tsaye tsangayar malam mai allo ta nufa, tun kafin ta ‘karasa ya hangota domun uwani ba bakuwa bace a gurinsa, Sai ya gyara zaman sa kan kujerar karfen da yake zaune yana sauraran isowarta,

Ganin ta iso inda yake tayi masa ‘kerere a ka tare da fadin”Gurun ka nazo.” sai ya fara kokarin mikewa daga kujerar ta daga hannunta “Dakata malam yi zamanka ba sai ka tashi ba.” Ido ya zuba mata suma almajiran tun sanda ta fara magana suka dakata da karatun da takeyi suna kallonta.

“To an yanka ta tashi! duk wani ‘kumbiya ‘kumbiya da munafurcin da kuka kulla ya fito sarari Allah ya toni asirinka ni Uwani na samu labarin abunda kukayi wa yarinyata Wasila, Na farko dukaninku da kai da ‘yan uwanka baku san ci da shan Wasila da Rashida ba tsawon shekaru goma sha, kwabonku bai ta’ba shiga tsakaninmu daku ba, Kuna katsina muna daura muyi aikatau muyi sirfau muyi daukau da duk da sana’ar data kama domin mu ciyar da kanmu kuna a matsayin iyayen Wasila da Rashida baku sani ba, to tur! da wannan zumunci naku Allah ya wadaran irin wannan zumuncin……Sai da na gama shan wahala da ‘yayana suka girma suka kawo munzali sannan ne zaka nuna min iko a kansu! bai zai yiwu ba! Shin malam wane irin zagi ne ba kayi min ba wace irin kalma ce bakayi jefe ni da ita ba ! amma kuma saboda tsabar son zuciya katsaham! sai na tsinci labari a gari cewa ka daurawa ‘yata aure saboda kwadayin abin duniya! Yanzu bakaji kunyar wannan abun da ka aikata ba.”!? Ta kare maganar tana tsare shi da manyan idanunta.

Malam jikinsa yayi kwata’kes! tunda yake a duniya ba’a ta’ba tsinkashi cikin jama’a ba irin yau!!! amma babu shakka Uwani ta gawurta gurin rashin kunya da rashin arziki…..Ta sake tsareshi da ido tana fad’in”Kai nake jira ka bani amsa malam.”? Gefan babbar rigarsa yasa ya goge gumin goshinsa, Yace.”Idan kin koma gidana a nutse zanzo nayi miki bayanin yanda al’amura suka kasance.”

“Babu wani gidanka da zan koma in koma inyi me? hukunci na riga na gama yankewa shine idan kana takamar kaine waliyin Wasila to nice nan na tsuguna na haifeta saboda haka ka kwana da shirin wannan auran da ka daura shi da niyar biyan bukatar ranka sunanshi lalatacce don ko sati biyu baza’a cika ba sai Wasila ta fito, mu zuba ni da kai.” Tana kare maganarta ta kade zaninta ta kara gaba, zuciyarta wasai! yau ta rama irin rashin arzkin da malam yake mata shekara da shekaru.

Uwani na barin gurun malam ya sunkuyar da kanshi ‘kasa masifar kunyar al’majiransa yake yi babu shakka dukanin maganganun da Uwani ta fada a kanshi gaskiya ne, tun bayan rasuwar dan uwansa Yahuza da ya dauko su Wasilan suka bujere masa tsayin shekaru goma sha biyu bai sai waiwayar inda suke ba daga shi har sauran ‘Yan uwanshi, Uwani ita ya kasance take dauki ba dadi da ‘yayanta har Allah yasa suka kai munxalin girma…..Hakikanin gaskiya yanzu shima ya gano laifinsa, zumunci ba abun wasa bane a lokacin da su Wasilar suka bujere masa a kwai kuruciya a tare dasu bai kamata yace zai wofintar dasu ba a matsayinsu na wad’anda basu da kowa a garin kano Uwani tayi namijin kokari a kansu da rayuwarsu…….Yanzu ya gano abunda suka aikatawa yaran sam bai cancanta ba kuma duk abinda Uwani tayi masa a halin yanzu bata dai laifi tabbas hakane kamata yayi kafin daurin auran a sanar mata kome zatayi dai na lokaci kankani ne magana ta wuce amma ga yanayin yanda yaga ta dauki lamarin da zafi dole yayi wa tufkar hanci idan ba haka babu shakka tana iya zuwa ta girgid’e wannan auran da ya daura wanda yake sanya ran mutuwa ce zata rabashi…..Ya sake sanya gefan rigarshi ya goge gumi kana ya dago yana kallon almajiransa sai hayaniya suke! bulala ya d’aga Yace.”To a cigaba a cigaba.”!!! Su rud’e da karatu ko wannensu da allo a hannunsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button