NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Khalifa yace.”Mu aje maganar Alhji ‘Danliti a gefe guda ni muhimiyyar magana ce nake tafe da ita.” Ahamdu ya kalleshi a nutse yace.”To ina sauraranka.”

Khalifa ya dan gyara zamanshi sosai ya mai da hankalin sa kan abokin nashi ya bude bakinsa a nutse yace.”Shin kasan matarka da ka saki tana dauka da cikin ka har na tsayin watanni uku da sati biyu.”

Yaji wani irin shocking a jikinshi ya zubawa khalifa yana kallonshi yana so yayi mishi ‘karin bayani. Khalifa ya gyara fuskarsa sosai alamun maganar da zaiyi mai muhimanci ce Yace.”Wasila na da ciki kamar yanda kaji na fada maka da farko, Dazu ina kan hanya ta ta zuwa gidanka Hafsa ta kira ni a waya kan cewa inyi gaggawar zuwa babban asibitin murtala dake cikin gari ga abinda ke faruwa, dalili kenan da ya sanya kaji ni shiru banzo ba…………Khalifa ya shiga warware masa abunda ya faru da Wasilan da irin sirad’in da ta tsallake dashi kanshi cikin jikinta da yake cikin wasiwasi da ‘kila wa ‘kala ya kuma tabbatar masa da cewar mutukar ana so cikin ya inganta a kuma haifeshi cikin salama da nutsuwa da kwanciyar hankali tilas yarinyar ta samu kulawa mai kyau sannan ne za’a samu dukanin abinda ake so.”

Tunda Khalifa yake maganar yake jin wani iri a jikinshi, ya shiga lissafin watannin cikin dai dai lokacin auransu ne dan a hasashen sa ma yana zargin haduwarsu da yarinyar ta farko ta same shi………..Jikinsa ne yayi sanyi sosai kafatanin hankalinsa ya karkata kan ingantuwar d’anshi da samun xaman lafiyarsa a cikin uwarshi, gabanshi ya dinga faduwa yana addua da godewa Allah da bai sa cikin ya zube a kan hanya ba! Ji yay wani irin gumi na keto masa, Khalifa ya lura abokin nashi ya shiga rud’u da tashin hankali sai ya dafa kafad’arshi a nutse yace.”Yanzu wace shawara ka yanke dangane da yarinyar dashi babyn dake cikin cikinta.” ? Ya dan kalli Khalifa cikin yanayi na damuwa yace.”Nama rasa me zanyi wallahi Khalifa nagode kwarai da gaske Allah ya bar abota da zumunci mai amfani yanzu idan da babu kai mybe da tuni na rasa gudan jinina, bana haufi kan cikin yarinyar nan nawa ne Khalifa nasan lokacin da nayi abina.” Khalifa yace.”Haba babu komai wallahi ni da kai yanzu ‘yan uwane mun wuce a kira mu abokai duk abinda nayi maka kaina nayi wa, ina tambayar ka matakin da zaka dauka dangane da yarinyar da abinda ke cikinta babu shakka dukaninsu suna bukatar kulawa mai kyau…….Yace.”Khalifa kasan dai halina idan nayi magana kan abu ko kuma na yanke hukunci kan abu bana ta’ba barin abu daga baya in waiwayeshi, amma tunda haka ta kasance Zan sakata gida in killace ta sannan in hada mata komai na jin dadin rayuwa ta zauna ta cigaba da kula min da yaro na har sanda Allah zai sa ta haife mun abuna…..Idan ta haihu in taga zata shayar dashi ok idan taga bata da ra’ayin hakan zan nemi mai raino insha Allah amma bana ji sanadiyar wannan yaro ko yarinya na cigaba da zaman aure da ita.

Khalifa bai so jin haka da gareshi ba amma bashi da magana dama kuma yayi al’kawari kancwa ya bar cewa dashi ya mai da yarinyar, yasan duk sanda ya gane mahimancin ta a gurinsa zai dawo yana neman shawararshi, Sai kawai yace.”Shikkenan hakan yayi dan gaskiya na fahimci akwai matsatsi da rashin sukuni da rashin abinci mai kyau a tare da ita da Mahaifiyarta da yar uwarta ina ganin idan anyi hakan zasu samu sakewa sosai kai kuma zaka samu lada kuma dan Allah ko bayan ta haihu ka kar’bi d’anka ko ‘yarka to ka bar musu gidan da komai na ciki su zauna sada’katuljariya zaka samu lada.”

Yace.”Khalifa a yanzu yarinyar nan zan iya yi mata komai albarkacin gudan jinana da take dauke dashi kasan ni idan nayi kyauta bana waiwaye saboda haka bayan gida ma ni mai iya mallaka musu wani abun ne kar ka damu da wannan.” Khalifa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Hafsa dake karasowa inda suke……Ta zauna kusa da mijinta a hankali kai da ka gani kasan itama tana cikin damuwa, Wai shin Shi governor wane irin mutum ne? ace ayi ta abu d’aya haba ai yaci ace ya hakura ya dawo da yarinyar nan, ta lura kamar ma ya fiso yayi ta zama a haka babu aure da shekarunsa da komai shiyasa mutane ke masa kallon mara lafiya da sauransu. Irin abinda take ta fad’a kenan cikin ranta……..Ya d’an kalli agogon hannunshi shifa da ba dan dare yaja ba da ya dauki khalifa sunje ya gano yarinyar nan ba wai dan ita zaije ba a’a dan abinda ke cikinta cikin fargaba yake sosai yana ganin kafin gari ya wace cikin zai iya zubewa…… Babu zato khalifa yaji yace.”Tashi muje nagano yarinyar nan.”

Khalifa ya kalleshi cikin mamaki yace.”Yanzu da daran nan dubi time fa sha d’aya shaura.” Ya d’anja tsaki yana mutsika goshinsa yace.”Gabad’aya hankalina ya kasa kwanciya Khalifa ina jin a jikina kafin safiya cikin nan na iya zubewa ko wani abu ya faru, nasan mutukar banje na ganota ba ba zan iya rintsawa ba.” Khalifa ya dinga kallonshi yana jijjiga kai yace.”Shin wai ita kake son gani ko kuma abinda take dauke dashi.”? Da sauri yace.”No ni abinda ke cikin cikinta nake son gani ba wai ita ba meye gamina da ita.” Khalifa yayi wani murmushin takaici yace.”To ina me tabbatar maka da cewar ko kaje yanzu wahalar banza xakayi dan nasan tayi bacci kuma ka’idar masu lalurar ciki ba’a tashinsu daga bacci, kuma kana maganar ba dan ita zakaje ba to shi cikin naka in kaje ganinsa zakayi ido da ido ko kuwa zaka ce ta d’aga maka riga ne ka gani.”? Ya shiga kallon Khalifa yana me nazarin maganarshi, Ya akayi kwakwalwarshi ta toshe ne? shifa a tunaninsa idan yaje yace ta bud’e masa riga yaga d’anshi! sai kuma yanzu maganar Khalifa ta sanya ya hango kuskuransa, yanzu dai babu aure a tsakaninsa da yarinyar nan yasan ko yaje bashi da hurumin rike mata koda d’an tsaya ballanta yace ta bud’e masa riga yaga d’ansa

Gumi ya shiga karyo masa ya ciro hankici yana gogewa ranshi sai ‘kuna yake yi yarinyar nan tayi bala’in cutarsa yasan kuma yanzu shi da kwanciyar hankali har sai yaga d’anshi a hannunshi tukkuna

Khalifa yace.”Hakuri za kayi gobe idan Allah ya kaimu sai mu je da wuri ku gaisa kasan kuma ko kaje babu ruwanka da ita tunda ba muharramarka bace.” Sai yaji kamar ya kwad’awa Khalifa mari da jin maganar da ya fad’a Yaja karamin tsaki yana me mikewa tsaye da fad’in “Allah ya kaimu goben zan shigo da wuri muje, kuma a goben nake son sauya musu gurin zama duk domin samun nutsuwa da kwanciyar hankalina inaji a jikina mahaifiyar yarinyar nan zata iya zubar min da ciki koda kuwa ita yarinyar bata so.” Khalifa yace.”Kai kake wannan hasashen amma a dazu munyi magana da mahaifitar yarinyar ta tabbatar min da cewar kwanaki sunzo har gida domin su shaida maka abinda ke faruwa basu sami ganinka ba kaga kuwa idan hakane to bata da hannu gurin zubewar cikin ka.” Yayi shiru yana nazarin khalifan kafin ya kad’a kanshi yana fad’in”Koma dai menene ni bazan ta’ba aminta dasu ba tunda sun shani na warke Allah ya kaimu goben kawai.” yana gama maganarshi ya nufi hanyar fita, Khalifan ya mike yabi bayanshi…..Hafsa kam dama tuntuni tayi shigewarta d’akin Governor bai ta’ba ‘bata mata rai irin yau ba mutum sai kace fir’auna zuciya kullum babu kyau ace kayi ta ri’kon mutum a ranka.

Yanda yaga dare haka yaga rana ya kwana yana juye juye da zumud’in son gari ya waye duk domin zuwa ganin gudan jininshi dake kwance cikin mahaifar Wasila……Asubar fari ya mike ya shiga toilet wanka ya soma yi kana ya dauro alwala ya fito ya shirya tsaf ya nufi masjid, ya kasance mutum na farko bayan liman da ya fara isa masalacin, sai ya zauna cikin nutsuwa ya fara jan carbi kafin liman ya tada sallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button