NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Cikin ikon Allah Wasila ta shige cikin ‘yan mata ‘yan ajinsu Rashida ta saje dasu ba zaka ta’ba cewa matar aure ce ba, kuma babu abinda ya gagareta gurin karatun dan dama kafin zuwan ranar jarrabawar yana dan koya mata wasu abubuwan dake kuma tana da saurin fahinta babu wani abu da shige mata duhu ko ya daga mata hankali sukayi jarrabawar fita daga secondary skull cikin narasarori masu yawa.


Ana ya gobe zasu tafi Garko Kawu Habibu ya kira wayar Amadu yake shaida masa halin da ake ciki, cewar malam mai allo zai daura aure ranar juma’a mai zuwa, kuma ba da kowa sai da mahaifiyar matarshi Uwani, Amadu yayi mamaki sosai da maganar Kawu Habibu daga karshe yayi addua gami da fatan alkairi ya kuma tabbatar wa da Kawu Habibun cewa insha Allahu suna tafe kafin zuwan ranar……….Kasa hakuri yay ya kirata a waya yace.”Akwai albishir din da zan shigo miki dashi, amma meye tukwicina.” Tana dariya tace”Ai kaima kasa ni.” Yace.”Nasan me? kawai ki fad’amin tukwicina.” Tace.”To zan barka kayi sau goma.” Dariya ya ‘kyal’kyale da ita yana sake rike wayar a hannunshi, yace.”Kamar gaske ko?

yarinyar daka amfara zaki hau ihu kina cewa na daina ke zafi kikeji.”
Ma’kale wayar tayi sosai ta wani lumshe ido tace”E mana ai kaine kakeyi da ‘karfi shiyasa.” Yace.”To me yasa idan na bari ke kikeyi da ‘karfin.”? Kunya ce ta rufeta ta hau inda inda! Yace.” Ai nagane wannan kukan da kikeyi na sharri ne dan dana bari ke kuma kikeyi da kanki kukan d’adi ne ko.”?
Sai ta soma shagwaba da sangarta tana fad’in “Ya bari ita bata so.” Yana daiya yace.”Na bari shikkenn idan na dawo gida bazan fada miki albishir din ba sai nayi sau goma kamar yanda kika fada kin amince.” ? “Umm.”! tace” Tana lumshe idonta wannan ‘yar wayar da suke tasa gabakid’aya hankalinta ya tashi sha’awa duk ta taso mata……

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE‘Yr Bngr Sys
84
Aikuwa da ya dawo gidan ta dameshi kan lallai sai ya fad’a mata albishir d’in shi kuwa yay ta ja mata rai, sai da suka gama komai na rayuwarsu sannan yake shaida mata abinda ke faruwa, farin ciki ya lulli’beta tamkar anyi mata albishir da gidan aljanna gaskiya taji dad’i sosai da wannan abu dama itama sam bata son zaman mahaifiyarta ta a haka tunda dai ba wuce auran tayi ba, koda Rashida ma taji labarin abinda ke faruwa tayi ta murna da farin ciki da ‘kyar sukayi bacci a ranar saboda farin cikin da suke ciki.

Gari na waye wa ta tashi da walwala da farin ciki sai shiri takeyi shi kam yana kwance yana kallonta kwata kwata baya son tayi nesa dashi dan dai bashi da yanda zaiyi ne kawai, ya shirya cikin manya kaya kamar dai yanda ya saba, duk ranshi babu dadi kawai dai yana kokarin daurewa ne amma duk da haka sai da fahimta to itama nata bangaran tasan tilas tayi kewarsa amma haka zata hakura dan gaskiya tana so taje ta gaisa da iyayenta sosai…..Kafin su tafi sai da ya fara kaisu gidan Hajja suka gaisa sosai Hajja tayi mamakin girman baby zahra yarinyar tayi wayo sosai sai kace wata ‘yar wata biyar.
Hajja ta ke’be da Wasila tace”Dama inata so inzo gidan naku Allah be nufa ba to tinda Allah ya kawoki sai ki tafi da ajiyar da nayi miki.”
Wani garin magani ne a cikin wani madaidaicin bokiti tace”Kullum ki dinga sha da madara ko nono daga can sakwatto nasa aka hada miki, ita kuma wannan zuma ce kada kiyi wasa da ita kullum kina shan murfi biyu safe da dare, idan kikaji dad’insu nasan da kanki idan sun kare zaki bukaci ayi miki wani.” Wasila ta sunkuyar da kanta kunyar Hajja takeji sosai godiya tayi mata cike da kunya tana kara jin kaunar matar a cikin ranta.

Hajja har mota ta rakosu tana fad’in “Su gaishe da mahaifiyar tasu insha Allah ranar daurin aure tare da ita za’azo.”……..Garba ne ke driving Rashida na kusa dashi da baby a hannunta….Ita dashi kuma suna bayan mota sai kalamai take mishi wai ya kwantar da hankalinsa insha Allahu sati guda kamar yau ce.”
Ya kalleta sosai yace.”Ni nace miki sati guda zakiyi.”? Ta kalleshi tana marairace fuska a langwabe tace”Hakafa kace dani shekaran jiya.”
Yace.”Takura min kikayi shiyasa na fada miki haka, yau laraba ko.”? Ta daga kanta tana kokarin mai da hawaye, yace.”Zan iya daurewa kuyi kwana biyu shima dan dai babu yanda zanyi ne! Ranar juma’a idan na shigo daurin aure sai mu tafi.”
Murya na rawa tace”To baza muje pataskum din ba.” Yace.”Wane pataskum kuma Itama Momyn ai nan za’a kawo ta sai ku had’u kawai ku gaisa.”
Tace.”Ai sai dare za’a kawota kuma lokacin nasan mun tafi.” Yace.”Ni zanyi magana da Malam d’in kancewa ana daura aure a tura mota a daukota ke Ni da kaina ma zan tura Garba ya daukota da sauran ‘yan uwa sai ku gaisa da juna.’
Shuru tayi masa domun ta fahimci duk dubarar da zatayi masa ba zai amince ba.
Haka suka isa Garko kowa na jin damuwa cikin ranshi mussaman shi Uban gayyar da yake fargarbar dare yay yasan kuma shi da bacci sai dai yaga anayi.

Amadu kafin ya tafi babu inda bai je sun gaisa ba cikin dangin Wasila yau kowa yaga mijin da take aure suka zama abun kallo a garin ba’yan uwansu kadai ba harda jama’ar gari fitowa suke suna kallonsu mussaman da wani matashin saurayi dake shiga kano sarin kaya ya gane fuskarshi sosai ya dinga watsawa mutane ai shine Amadu Musa Ba.Iya.ka d’an takarar governor Kano Aikuwa Jama’ar garin Garko tamkar an musu albishiri da gidan aljanna! suka fito kwantsinsu da kwarkwartasu suna ihu da fad’in “Allah ya baka mulki jahar kano fari mai farar anyi maliya mai ruwan ‘kare kukanka.” Ganin yanda Jama’a suka nuna masa ‘kauna sukayi dafifi a jikin motarsa ya sanya ya koma cikin motar tashi ya bude wata ma’ajiya da yake aje kudi ya daukosu dami guda, ya wakilta mutane biyar yace.”kowa a bashi abinda ya samu.” Aikwa Jama’a sukayi layi suna ihu da ‘kara yi masa kirari…..Wannan damar da ya samu ce ya sanya ya Umarci Garba da yayi maza maza yaja motar su bar gurin dan idan ba haka ba jama’a baza su bari ya tafi ba.
Su Wasila na cikin gidan Malam mata dam’kam tamkar suyi mata sujjada ita abun ma mamaki yake bata sai wani bata girma ake kowa so yake yayi tozali da ita, wato tun mijin nata bai zama governor ba har sun soma kiranta da matar governor dariya kawai take musu itama ta fito da kudi daga jakarta ta shiga raba musu……Deluwa sarkin kanzagi tace”Hajiya Wasila ina fatan idan kun samu mulki a Hannuku baza ki manta da Kauyen Garko ba domin dai nan ne tushenki asalinki Karamar hukumar garko na bukatar hanyoyi masu kyau, na bukatar wuta da ruwa da kuma makarantu gami da asibitoci sannan muna bukatar tallafi domin mu inganta harkokin noma da sauransu.”
Wasila dukanin abinda Deluwa ta fad’a sai da ta rubuta a wayarta tace”Insha Allahu duk su kwantar da hankalinsu idan mijinta ya samu mulki a hannunsu Wannan karamar hukuma zata zama city za’a gyara sosai yanda kowa zaiyi sha’awarta.

Sai bayan magariba suka samu sassaucin mutane a gidan, Bitan ta shigo dakin bayanta goye da zahra tace”Oh! ai shikkenan kuma gidan nan zai zama sansani na jama’a duba dai mutane sun kasa bari ki huta abincin ma sun hana kici cikin nutsuwa.”
Wasila tayi dariya tace”Bitan ai haka siyasa take dama zakiga mutum kwata kwata baida nutsuwa daga zarar na bar garin inace shikkenan kuma.” Bitan tace”Aikuwa dai kuna kokari wallahi ga baiwar Allah nan itama an shiga hakkinta.” Tafada tana kokarin kwance zahra daga bayanta.
Tace”Ki bata nono tasha Rashida zata shigo muku da abinci.”Yarinyar na ganin mamanta ta soma cilla kafafu tana b’angala dariya.
Bitan tace”Ji ja’aira wai ta san uwarta.”
Wasila na dariya tace”Bitan wannan yarinyar wayo ne da ita ai.”
Bitan tay dariya tana kokarin fita daga dakin tace”Ai yaran yanzu dama da wayonsu ake haifarsu.
Tana fita Inna Hajara ta shigo gidan tare da dan autanta da yake dauke da kwanukan abinci.”
Bitan tace”Yanzu Hajara sai da kika yi girki bayan komarwar ki gida.”
Hajara tace”Murhu biyu nayi shiyasa nayi sauri.”
Bitan tace”A gaskiya dai mana.” Kicin ta nufa ita kuma Inna Hajara ta shige masaukin su Wasila.
Wasila tace”Inna Hajara sannu bakya gajiya da zurga zurga koda yake babu nisa sosai ai…..Hajara ta zauna tana fad’in”Ke ni zurga zurgar da nakeyi kullum ai koda kudi aka hadaki ba zaki iya ba.” Wasila tayi dariya tace”Ai kam wallahi bazan iya ba, tace”Inna hajara shine tun bayan tafiyarki baki sake zuwa ba ko.”
Inna hajara tace”Ke rabani da zuwa wannan gidan da ba’a bukatata a ciki.”
Wasila kamar tayi dariya sai dai ta daure tace”Haba Inna waye baya bukatarki.” Tace”Rufe min baki kina so ki kare mijinki ko? bayan kin san shine ya koreni daga gidansa to me zai kaini ni ba kwad’ayayya bace.”
Wasila tasa dariya tace”Haba Inna yaushe zai koreki a gidansa Wallahi bakiji yanda yaji rashin dadi ba da ya dawo yaga bakya nan yayi ta fada wai nice nayi miki laifi shiyasa kika tafi.”
Tace”Oho! dai ni duk abinda nakeyi dominsa nakeyi da har zai dinga jin haushina dan nace ki gyara kanki ai shine zai mora shiyasa ai koda ki kayi ar’bain banyi gigin zuwa ba dan nasan dole zaki zo da kafafunki, in yaso sai nayi miki abinda nayi niyya ba don halinsa ba kome za’ayi ai shi za’ayi wa amma saboda tsabar rashin hakuri irin nasa yake ganin aibun mutune.”
Wasila tace”Dan Allah Inna kiyi hakuri magana ta wuce Yace a baki hakuri.” Ta’be baki tayi tace.”Uhmm! ni dama ai ba bakuwar zafi bace, Wannan kwanon da kike gani roman ‘yan shilla ne mai had’e da maganin gyaran matantaka da kuma ni’ima ki cinye tas ki shanye roman duk wani abu da kika rasa gurin haihuwa idan kinsha wannan roman zai maye gurbinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button