NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

ce abun dauka a gaskiya yanda naji dad’in wannan kujerar zai yi wuya na barta kai tsaye kai ni ko da d’an da na haifa za’a bu’kata zan iya badashi tunda dai nasan ai ba gama haihuwar nayi ba.” Haruna haruni yace.”Haka ake son cikkaken namiji jarumi me a’kida, kada ka damu idan Muktari ya shigo fadar gomnati ka kar’beshi hannu biyu zamu ‘bullo musu ta bayan fage, mulki dai sai dai suga anayi insha Allah duk jama’ar da suke dashi sai ta dusheshe ranar za’be mune zamu lashe.” To Wannan maganganun da sukayi ne ya sanya Governor Lawan Rabo kwantar da hankalinshi kamar tsumma a randa, ya tabbatar suna da ya’kinin akan cewar mutukar bokan da yayi musu aiki da ‘kuk’onan kawunan yara yana nan a raye cikin duniyar to sun tabbata sai sun watsa shirin su Amadu da Muktari

Amadu na isa gest house din nashi Alhaji Muktari ya soma tsokanarshi da fad’in “Da har ina cewa bari mu tafi tunda dai mu gaisa da Khalifa ya isa kai sai ayi maka uziri tunda kana tare da Uwargida.” Amadu ya zaune kan kujera yana murmshi hularshi ya cire yana kallon Khalifa yace.”Nasan wanda ya fad’a maka cewar ina tare da Uwargida” Khalifa yace.”Nine na fad’a mishi da kayi zamanka ma yayi maka uziri ko bakaji abinda yace bane.” Murmushi yayi yana girgiza kanshi yace.”Uwargida bata da ‘koshin lafiya me kuke tunanin za’ayi.”? Alhaji Muktari ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare Yace.”Yana da kyau dai muje na dubata kafin na wuce, dan Khalifa yanzu yake shaida min an samu ‘karuwa to Ubangiji Allah ya raba lafiya.” Amadu yace.”Ameeen ya rabbi, yace.” Khalifa ya fad’a maka na samu ‘karuwa shi bai fad’a maka tashi ‘karuwar ba.”? Alhaji muktari ya kalli khalifa da son jin ‘karin bayani.” Khalifa yasa dariya yana kallonshi shima Amadu yace.”Shima iyalinshi juna biyu gareta.” Alhaji Muktari ya shiga girgiza kanshi yana kallonsu da fad’in “Gaskiya mutanan nan bakwa wasa.” Khalifa na dariya yace.”Bama wasa ko dai baka wasa Alaji matanka biyu ‘yayanka shida ai kaine shugaba gwara mu da mace daya muke zaune.” Alhaji muktari ya dan tura hularshi ‘keya yana gyara zamanshi yace.” Ai mata biyu shine jin dad’i Alaji sai ranar da kukayi zaku gane haka.” Amadu dai murmushi yake yace.”Duk mutumin dake da mace biyu bashi da kwanciyar hankali Alaji bana jin zan iya had’a mace biyu a gidana in dai ba Allah ne ya ‘kaddara ba.”

Khalifa na d’auke da murmushi a fuskarshi yace.”Ni kam ina tsammanin had’a mata biyu anan gaba dan gaskiya ina da ra’ayin yin hakan.” Alhaji Muktari ya bashi hannu suka tafa…..Amadu kuwa kallonshi yay da mamaki a fuskarshi yace.”To tunda ka tona asirin ranka sai na fad’a mata kasan ni da Hafsa akwai amana ba zan yarda kaci amanarta ba.”

Khalifa yasa dariya yana fad’in “Kafi tsuntsu gudu dan Allah! haka kawai Allah da annabi sun halasta min ace kada nayi, Kasan Allah idan lokacin aurena yazo dole ne Hafsa tayi hakuri dan ina da wannan niyyar.” Amadu ya dinga girgiza kai yana kallonshi, shi kam a nashi ra’ayin bai son had’a mata biyu ko sama da hakan a ganinshi duk damuwa ce mutukar matarshi zata dinga dauke mishi dukanin laluranshi bai damu da lallai sai yayi wani auran ba koda kuwa ya samu mulki a nan gaba.

Tattaunawa suka shigayi da sabbin tsare tsaren da zasuyi mutukar Allah ya cika musu burinsu akan abinda suke nema mutukar sun samu nasarar d’arewa kujerar mulki to babu shakka Al’ummar jahar kano da katsina zasuyi farin ciki zasu ga sauyi ta ko wanne ‘bangare

Misalin ‘karfe tara da rabi na dare suka fito daga gest house d’in Alhaji Muktar yace yana so ya duba Wasila kafin ya koma dan gobe da asubah yake so su wuce, To dan kar ya watsa masa ‘kasa a ido ne ya sanya ya amince da bukatarsa, saboda baya son abinda zai sanya girma da mutuncinsa ya zube a idonshi, baya so suje gidan Yarinyar tayi wani abun wanda zai nuna babu jituwa a tsakaninsu domin har yanzu ya lura da ita bata wani saki jikinta ba sosai.

Goma shaura motarsu ta shiga cikin gidan garba nayi parking ya fito cikin sauri ya bude musu kofa suka fito, tare suka nufi cikin gidan dukaninsu harda khalifa.

Rashida ce ita kad’ai a palon tana kallo Hajjah tuni ta shige daki ta

kwanta dan tanayin sallah isha’i take kwanciya, Wasila kam bata jima da barin palon ba itama wanka ta shiga tayi ta kwanta dan har yanzu jikinta bai dawo dai-dai ba akwai sauran gajiyar hanya

Rashida ta mi’ke tsaye tana musu barka da zuwa, ta gaishe su a nutse tana kokarin shigewa Har zai yi mata magana sai kuma yaja bakinshi yayi shuru ya kalli Abokan nashi a nutse yace.”Bari na fito da ita.” Khalifa yace”Kada kayi wannan dad’ewar da ka saba.” ‘Karamin tsaki yaja ya yana girgiza kanshi ya tura kofar dakin ya shiga wanda yayi dai-dai da lokacin da ta fito daga toilet jikinta daure da towel iya cinyarta…..Sallamar dake dauke a bakinsa ce ta gagara fitowa, da kyar ya janyo dauriyarshi da jarumtarshi ya shiga dakin, ‘Dan tsayawa tayi tana kallonshi tana turo bakinta gaba, shiyasa ta’ki shiga dakinsa ta gudo nata ashe bata tsira ba yazo zai takura mata, ‘Bata fuskarta tayi ta wuce a hankali taje ta zauna gaban mirror tana bud’e man shafawa

Bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin mudubin tana shafa mai a hankali tana shafawa a hannunta, ba tare da yace komai ba ya sanya hannunshi cikin vasilin din ya soma shafa mata sassan jikinta, jin saukar hannunsa a jikinta ya sanya ta sauke ajiyar zuciya me tafe da tashin tsigar jiki, hannunsa ta cire wanda yake kokarin cusawa cikin towel din ta sake daure kirjinta dashi, bai ce mata komai ba, ya dan rankwafa a hankali ya d’an ja ‘kafafunta ya soma shafa mata vasilin din a cinyoyinta da kafafunta…….Ido ta tsira mishi yayin da kanshi ke ‘kasa, taji wata ‘kwallah na kokarin zubo mata daurewa tayi ta dauke kanta da sauri lokacin da ya dago ganshi, bayan ya gama shafa mata vasilin din, Ta mike tana sake rike daurin towel din a kirjinta wardrobe ta nufa ya bi bayanta, kayan bacci masu taushi ya dauko ya rike hannunta a hankali yake kokarin kwance towel din, tasa kuka tana tureshi, ya mi’ka mata kayan da fad’in “Kiyi gaggawar sanyawa tunda baki so nasa miki akwai ‘baki na jiranki a palo abokina ne yazo duba jikinki.” Cikin rawar murya tace” Ni ka fita to nasa kayan zan fito yanzu.” Harararta yayi yace.”Meye abinda zaki ‘boye min a jikinki ? wai ke dan Allah yaushe zaki daina wannan ‘kauyancin ne? Shiru tayi mishi ta nufi bed da kayan a hannunta, zama tayi gefan gado ta soma zura dogon wandon tana kare cinyoyinta da towel, shi dariya ma take bashi wallahi, yay tsaye a kanta har ta gama sanya kayan ya mi’ka mata ‘katon hijab d’inta na sallah tasa kana ya nuna mata hanya da hannunsa……Gaba tayi yabi bayanta haka suka fita palon.

Alhaji Muktari ya kalleshi a lokacin da suke karasowa inda suke yace.”Ashe dai da gaskiyar khalifa shiyasa kafin ka shiga ya tuna maka.” Amadu yayi sauri bagarar da zancen dan baya so ta fahimci inda zancen nasu ya dosa, shi baiga wani dad’ewar sa a ciki ba sa’ido ne kawai irin na khalifa.

Ta gane khalifa, d’ayan ne bata gane ko waye ba, a nutse ta zauna kusa da mijin nata ta shiga gaishesu, Alhaji Muktari ya shiga mamakin ‘kan’kanuwar yarinyar wai itace matar abokinshi Yo ai wannan za tayi sa’ar babbar ‘yarshi Sa’adatu, babi shakka dole abokin nashi yace bashi da sha’awar ‘kara wani auran saboda yasan yana da wacce zai mori ‘kuruciyarshi da tsufanshi.
Cikin kulawa yake amsawa ya dan tsokanta ita kuma sai sunkuyar da kanta take kunyar mutumin takeji sosai ganin kamar ma ya girmi mijin nata, Wanda sam ba haka bane Alhaji Muktari sa’an Amadu ne dan shima baifi shekaru arba’in da biyar ba , kawai dai dan yayi aure da wuri ne kuma yana da jikin girma ba kamar Amadu da bai da ‘kiba ba, Tana zaune tana sauraransu suna hira duk ta ‘kosa ta bar gurin ta d’an muskuta a hankali zata tashi, Ya ri’ke mata hannunta ba tare da ya kalleta ba ya juya suka cigaba da magana da Khalifa, tamkar zata fashe da kuka haka ta kalleshi to meye amfanin zamanta a gurin bayan sun gaisa ba sai ya kyaleta taje ta kwanta ba……Kirane ya shigo wayar Khalifa sai lokacin suka san dare yayi sosai sha d’aya da rabi Hafsa taji shuru bai dawo ba ta kira wayarshi, Ya mike da sauri yana kallon agogonshi, yace”Ashe dare yayi sosai sha d’aya da rabi yanzu.” Duk sai suka mi’ke tare Alhaj

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button