NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Sai wajejan goma da rabi na dare Al’amura sukayi sauki a babban boutique d’in…(Gurin sai da ‘kananun kaya irin na yara da na manya maza da mata takalma irin su booth helf cover da na yara da manya duk zaka samu a gurun a goguna masu kyau deznar iri iri akwai a gurin kai mutukar kana so ka had’a dreesing na kece raini to idan ka shiga gurin ka gama saboda zaka samu duk wani abu da kake bukata )kayan dake cikin boutique din A.M. B Na mussaman ne dan sai ka gama xagaye kafatanin kasuwar kwari da sabon gari wambai da duk sauran kasuwanni baka samu irin oder shi ba Ahamdu na kawo kaya masu kyau da ‘karko shiyasa kullum a gurin a ciki yake da Costoms duk wani ko wata mai ji da kansa burinshi ya shiga gurin yayi siyayya……Har wannan lokacin suna tare da Khalifa sai bayan sun tabbatar da komai yayi clear sannan suka wuce gida…….. Khalifa na draving yace.”Afnan fa ta damu kullum kuka takeyi wai sai ankaita gurin auntynta tun sanda taji muna maganar da momynta zamuje gurin amarya shikkenan take rigima wai a kaita gurin aunty amarya ita dai.”

Dariya yasa yace.”Ai ni rigimar wannan yarinyar ita ke had’ani da ita haka kawai tazo ta hanani baccin dare tayi zamanta wallahi bana nemanta.’
Khalifa yace.” Kai dai kawai kace kar tazo ta hanaka amarci wa zaka mayar karamin yaro okey shikkenan tun da haka kace sai na kawo ta dan haka gobe ka shirya zamu zo tare da momynta kuma tare da kayanta zamu zo tunda anyi hutun skull sai ta zauna ta d’ebewa amarya kewa.”

Murmushi yayi ya dan tura hularshi ‘keye yace.”Kai a tunaninka amarci nake ci da wannan yarinyar? lallai Khalifa ka mance dalilin da ya sanya na aureta ko, shin mai zai sanya ni na ‘bata lokacina a kanta da har zanci amarci da ita.” Khalifa yace.”Bafa zan dauki wannan maganar ba Alaji nasan dai idan bakayi me gabadaya ba to nasan kana tatta’ba ta dole ne nasan ba zaka sanya mata ido kawai kana kallonta ba.” Murmushi yayi yace.”Malam kai kake wannan tunanin ni sam! wannan yarinya bata bani sha’awa.” Dariya kawai Khalifa yayi yace.”Mubar maganar kawai ni dai ba karamin yaro bane na kuma san abinda za kayi da wanda ba zakayi ba

Har cikin gidanshi Khalifa ya ajiye shi dake a motarshi suke ya bude motar ya fito suna sallama, Khalifa yace.”Ka fadawa amarya idan Allah ya kaimu gobe tana da babbar bakuwa saboda haka sai ta shirya.” Yace.”Ni dai tunda ba bakuwa ta bace shikkenan.” Ya juya yana kokarin shiga ciki Khalifa yace.”Kayi mantuwa fa.” Sai sannan ya tuna shi masa site din baya ya bude ya dauko wasu manya manyan ledoji guda biyu yana fadin”Na manta shaf wallahi.” Garba ne ya karaso gurin yana musu barka da zuwa ya mika hannu ya karbi ledojin hannunsa, gaba yayi da ledojin a hannunsa shi kuma ya tsaya suna sallama da khalifa.

Tsit! palon tamkar babu wani mai rai a ciki….Ya nufi bedroom dinshi nan ya tarar dashi kaca-kaca har yanzu shimfidar gadon a hargitse take kamar dai yanda ya fita ya bari sannan ga tsintsiya da makwashin shara nan a tsakiyar kafet gashi kuma bata dakin kamar yanda ya saba idan ya shigo ya ganta kwance tana bacci bata dakin yau! Ya ajiye ledojin hannunsa ya fita daga dakin…..Bedroom din dake kusa da nashi ya murda yaji a kulle gam ya wuce dayan shi yana murdawa ya bude babu kowa a ciki….Ya bude ba kusa dashi shima bata ciki zarginsa yafi tabbata akan ta kulle a cikin wanda ya murda yaji a rufe…..Ya dawo a gajiye shi mai zai iya asalima tsintsiya bai iya rikewa ballanta ya iya wata shara dama su Garba ne suke masa aikace aikacensa, dan haka ma yanzu Garban ya kira yace ya shiga ya gyara masa daki shi kuma ya zauna a palo yana duba wayoyinsa yini guda yau bai duba wayar ba test messages gasu nan rututu haka dai ya dudduba wad’anda zai iya ya bari……Mutum ne shi ma’abocin jin zafi dalili kenan da ya sanya ba ya zama da manyan kaya a gidanshi mutukar yana gida zaka same shi da gajeran wando iya gwiwa da shart ko kuma singilet ko cikin kayan bacci yafi tu’ammali da masu mad’aurai da botira idan ya ga dama ya daure ko yasa botiran idan bai ga dama ba ya bar kirjinsa a bude, yanzu ma wata irin zufa ce take keto masa ba abinda yake so sama da ya watsawa jikinsa ruwa, Garba na fitowa ya mike ya nufi dakin Garba ya d’ebi wayoyinsa ya bi bayansa dasu.

Sanyi ko Basir na sanyawa gaban ki ya ‘bude!!!! ki Haihu ki’ki kula da gabanki shima na sanya wa ki bud’e ba tare da kin fargaba, Namijin dare (ba’kin aljani) idan yana kusantar ki ya kan janyo miki masifar bud’ewar gaba, kuyi ta rigima da miji idan da tsautsayi da rashin hakuri sai kiga an rabu!!! wane mataki ya kamata mu dauka domin mu kare kanmu daga fad’awa cikin wannan tashin hankalin!?

Littafin na kudi ne……..!
Kika futar min da book! Ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar.
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
31
Koda ya shiga dakin kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka ya fito sanye da rigar wanka, tsayuwa yayi gaban mirror ya goge jikinsa kana ya shafa vasilin a jikinsa gami da turaran jiki ya sanya Karamar t-shart mai yankakken hannu da boxer tamkar wani sauri dan 20 years haka ya dawo kuruciyarsa ta fito fili dama kuma in dai zai sanya ‘kananun kaya haka yake zama dan saurayi sosai suke masa kyau sai da kuma bai da ra’ayin sanya su ya fita ‘karkarin shi ya sanya a gida kawai….Parlor ya fito ya nufi daining komai tsaf tsaf Rabe ya jere masa kayan abinci babu alamun an ta’ba komai a gurin…..Cikin mamaki ya fara bude kulolin abin bai ga alamar wani ya d’iba, ya zuba iya dai-dai cikinsa yana ci a nutse yana had’awa da lemo, tunaninsa duk ya ta’allaka ne kan yarinyar babu shakka shima sai yanzu da ya zauna yayi nazarin abinda yayi mata yaga bai kyauta ba, bai kamata yayi nufin tozarta uwarta a gabanta ba duk lalacewar uwarka ba zaka so wani ya ci mata mutunci a gabanka ba, amma baya jin ko da wasa zai iya tunkarar ta da niyyar ya bata hakuri idan ta gaji da fushin za ta daina……..Sai misalin sha biyu da rabi ya bar palon…..Yau kadai da zai kwanta shi kadai a dakin sai yaji wani iri tsayin kwanakin da tayi a gidan tana kwana a dakinsa har ya saba da hakan duk da kafin suyi bacci dukaninsu sai suyi fada sau nawa hakan nayi masa dadi in dai zai ga giftawarta a dakin, shi kanshi ya fahimci zuciyarsa ta damu da yarinyar kuma ya soma zargin wani abu ya soma ziyarta zuciyarsa dangane da yarinyar…..Da kyar! bacci ya dauke shi mai cike da tunani da mafarkin gashi yana saduwa da ita.

To itama nata ‘bangaran hakane ya kasance….Tun rana da suka rabu ta kudiri aniyar bar mishi dakinsa tunda ya kirata da kazama, har yana mata gorin daki kana kuma yana cin mutuncin mahaifiyarta a gabanta yasa taji sam ba zata iya had’a numfashi dashi ba domin wani irin tsanar sa takeji a cikin zuciyarta, haka ta kwana ba taci abinci ba tun bayan abincin da taci da rana har garin Allah ya waye babu komai a cikinta.

Shida dai-dai na safe! Ya fito daga bedroom dinshi cikin shigar Kayan motsa jiki wani wando ne da rigarshi masu dan kauri wandon iyakacinsa gwiwa kuma ya matse masa jiki sai rigar mai yankakken hannu itama ta kamashi sosai power dinshi ya fito kafarshi na sanye da booth, ya nufi kofar fita ba tare da yayi tunanin buga kofar dakinta ba yasan ‘batawa kansa lokaci zaiyi kawai idan ya gama abinda yake ya dubata…….Ke’batancen gurin da gym dinshi yake girki ya nufa, Ya hau kai ya soma yi babu ji babu gani Garba da Hani na tsaye a gefan hagunshi da damanshi, Ya jima kan Gym din kafin ya sauka ya kwanta kasan gurin yana hutawa, sararin samaniya ya zubawa ido yana kallo yana mai da numfashi Garba ya miko masa sassayan ruwan swn ya mike zaune ya karba ya fara tuttulawa cikinsa, a kuwa gumi ya yanke masa kamar wanda ya watsa ruwa, wata iriyar kwanciya yayi ya soma training a haka ya kai ya kawo haka ya dinga yi ko wace jijiya dake jikinsa ta mike gashin jikinsa ya mike tsabar yanda jikinsa ke budewa, sai da ya kai kimanin minti talatin yana mota jikinsa a kwance kana ya saurara, ya kar’ni karamin towel dake hannun Hadi, yana goge jikinsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button