NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wasila tace”Haba Uwani wannan wace magana kike ? wane irin ciki kuma ai tunda naje gidanan d’an yatsana ban bari ya rike ba. Uwani ta sauke ajiyar zuciya tana fad’in”Alhamdullhi to yanzu me muke ciki.” Wasila tace “Mun riga mun gama magana da As insha Allah komai yazo karshe zan cigaba da rayuwa tare daku aurena da wannan mutumin ya kare daga yau.” Uwani tace”Naji dadin hakan! Dan na lura bashi da mutunci bai daukeni a matsayin mahaifiya yana kallona a tsaye ya tuka motarshi ya tafi, ko ya tsaya ya gaisheni to idan nice nasha wahalar haihuwarki da rainon ki sai kin rabu dashi har abada mu zuba mu gani.”

Rashida tace”Wallahi anti Wasila ki kiyaye kiyiwa kanki fad……”Zanci Uwarki! kika sake min wata magana anan gurin!!!! Rashida tayi shiru tana kallonta ta cigaba da surfa mata ashar tana fad’in”Banza mara zuciya da kishin kai! a gabanki fa ya kad’a kansa ya tafi ba tare da ya gaishe da uwarki ba, kudi hauka ne! ni wallahi duk wanda zai ta’ba min martabar Uwata sai inda karfina ya kare, na lura ke din ‘Yar jam’iyyarsa ce shi da wancan tsohon me allo to wallahi zaki fice min daga gida dik sanda kika sake min maganar banza.” Rashida ta ta’be bakinta ta mike ta shige daki tana ‘kunkuni.” Tsaki taja ta maida hankalinta kan Uwani Tace”Wannan yarinyar bata da hankali wallahi.” Uwani tace”Haka nake fama da ita kullum zagina ne kawai ba tayi.” Wasila ta dinga zaginta tana fadin”Aikuwa mutukar tace zata goyi da bayan Ahmdu da mai allo to zata bar mata gidanta in yaso sai ta koma can garkon da zama…….Uwani tace”Wannan hukuncin da kika yanke shine dai-dai.

Nan Wasila ta shiga warware mata abubuwan da suka faru da ita gidan Ahamdu da yanda ya dinga sumar da ita yana mata kamshin mutuwa amma kuma bata fada mata cewar mu’amular aure ta shiga tsakaninta dashi, ta fada mata irin bindiddigin da yake mata da furucin sa kan gidan da suke ciki cewar idan ya kar’bi mulki sai ya tuhumeta idan ya kama ma ya daureta sai ya daureta kan kud’adan mutane.” Uwani tace”To ai kema baki sukayi ba sata Kikayi ba saboda haka kada ki wani damu duk barazana ce babu abinda zai iya yi miki, Amma kuma nafi so, gobe mu kama hanya mu wuce potsikum sai ‘kura ta lafa sai mu dawo mu san abinyi, sai dai kawai yaji kira daga kotu.” Tace.”To shikkenan yanzu dai dole zanje banki in samu na ciro kudi masu dan kwari a hannuna kafin zuwa goben.”

Da misalin karfe biyar da rabi na Yamma Wasila da Camas! suka fito daga bakin union duk wasu kud’addanta ta sanya ankwashe mata su daga asusunta an maida accont din Camas kudin sun tasamma miliyan hud’u da d’aruruwa, Cikin rashin dubara da wayo ta barwa Camas! Atm din a hannunta suka wuce gida,

Sai gab da magariba suka isa, Uwani tayi musu girki mai dad’i da nama sukayi sallah tukkuna kafin su zauna zaman cin abincin, kira ya shigo Wayarta….Sabida tsabar yanda ta haddace numbarshi yasa ta gane, gabanta ya dan fadi sai dai ta dake! tayi masa sallama Ya amsa yana tambayar ta mutan gida tace”Sunanan kalau.” Yace.”Ina fatan kin shirya ko dan ganinan kan hanya.” A kumbure tace”Abinci zanci.” Murmushi ya saki wanda har sai da taji sautinsa a kunnanta, taji tsigar jikinta ta mike, yayi amfani da wata iriyar murya “Ki aje min nawa.”! Ta sakejin wani bakon yanayi a jikinta jin muryar da yayi amfani da ita, Sai tayi saurin fad’in” To! ta kashe wayar dan bata so ya samu nasarar kashe mata jikinta….Uwani tace”Shine ko.”? daga kai tayi kawai tana jujjuya abincin, Jin muryarshi kawai ya sanya mata kasala da mutuwar jiki!Uwani tace”Kiyi da azama yana zuwa ku tafi ni wallahi so nake inga komai ya faru na gaji da wannan abu.” Wasila ta sakejin wani karfi da kuzari gami da dakiyar zuciya yazo mata, ta dan caccakali abincin ta ajiye cokalin kana ta ‘kame kan kujera tana jiran zuwanshi.

Littafin na kud’i ne….!
Kika fitar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 10:55 pm] +227 98 36 59 34: Afuwa jiya nayi mistake gurin sa numbar a mai makon 46 sai na sake sanya 45 nasan dai babu matsala tinda book din na tafiya kan tsari…….VIP ‘Yar Banga! sannu ku da ‘kokari! ina ‘kaunarku kuna fitar da book ina ‘kara samun costomars???????????? masu karantawa baku biya ba kuma sannuku da kokari ????yawwa! guys mu cigaba da gashi!! ku d’auki abu mai amfani na cikin book d’in nan ku watsar da mara amfani……Muje zuwa

‘Yr Bngr Sys
47
Kimamin mintuna goma sha biyar da kiran wayarshi, ya sake wani kiran yana sanar mata da cewar gashinan a bakin gate dan bai shigo ciki ba ma saboda yanayin akwai hadari sosai dan har an soma iska da walkiya yace maza maza ta fito su tafi. Ta mike da sauri tana gyara jakarta, Uwani tace”Kada fa kiyi da wasa kina samun kufcewa ki nemi mafaka ki ‘buya idan ya bar gurin sai ki fito, Tace”Ai As ma yana gurin dan yayi min bayanin yanda zanyi.” Camas dake danna wayarta tace”Ni kam inanan sai gobe ma had’u a gest house din As nasan dai can zaki kwana ko.” ? Tace”E mana amma da wuri zan fito xamu wuce fataskum sai komai yayi normal kana mu dawo.” Tace.”To shikkenan.” Rashida dai na zaune bata sanya musu baki ba cikin maganarsu duk haushi suke bata har Uwanin sam basu san inda yake musu ciwo ba, shiyasa tayi al’kawarin daina sanya musu baki a maganarsu idan ta kwa’be musu ita ‘yar kalloce tinda ta fad’a musu gaskiya sun’ki ji.

Har bakin gate Camas da Uwani suka rakota, sai da ta fita tukkuna suka koma ciki…..Tana fita aka soma yayyafi da sauri ya bude mata motar ta shiga tana gyara mayafinta, ya kunna motar suka bar gurin, Sai da suka hau titi sosai ya d’anyi gyaran murya yana kallonta yace.” Ya mutanan gidan ina fatan kin mi’kamin gaisuwa gurin momy kafin naje da kaina.” babu yabo babu fallasa tace”Eh tace tana amsawa.” Motar tayi shiru bayan maganarta ruwa ya soma yin ‘karfi gabanta na cigaba da fad’uwa!
Saboda yanayin goslow din dake tsakanin tal’udu da goran dutse ya sanya yayi yanke hanya ya shiga ta wajan ma’kabarta zai bi ta ‘yan rake yana ganin hakan zaifi masa saukin shiga unguwarsu tasu ta tudun yola, duk wannan yanke yanken da Ahamdu yake yi da mota, Motar su Mada! na biye dashi amma saboda tsananin taku mutum ba zai gane hakan ba, Sosai yake gudu sam baya son ruwa yayi karfi wanda zai tilas tashi yatsawa a kan hanya shiyasa ya kara karfin motar, Wanda ita kuma sai zazzare ido takeyi kamar kace kyat! ta ruga a guje tunani takeyi ko tana ina su Mada! zasu fito……..Kasancewar ruwan ya soma ‘karfi ya sanya masu siye da siyarwar dake kan titin kansakali mahad’ar ‘yan rake ya sanya suka fara kwashe kayaiyakinsu kowa na neman tsira titin tayi shiru hanya tayi tsit! sai saukar ruwa sai kuma ababen hawan dake ta sharara gudu kan kwalta kowa na so ya isa gida.

Yana fitowa daga tsukin titin kansakali ya hau titi sosai, yana kara karfin motar! Kawai motar su Mada! ta daki tashi motar wanda ya sanya hannunsa ya goce daga kan sitiyarin motar ta gangara wani layi! Dake titin dama motoci basu fiye binshi ba ya sanya jama’a basu ankara ba, bayan haka kuma ga ruwan da akeyi babu kowa a gurin masu wuce wa a baben hawansu basu fahimci komai ba dan dik wanda yaga motar Ahamdu cikin layin zai dauka a fake take dan bata nuna komai ba da zai dauki hankalin jama’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button