NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Tayi wanka tsaf! ta shirya jikinta cikin dakakkiyar shaddar galila irin ta mata, kalar shaddar ta kasance C green ce anyi mata wani irin stone work rigar duguwa ce ta zauna sosai a jikinta ta fitar mata da tsarin hallitarta, yau ta danyi make up ba kamar da ba ta shafa hoda kana ta zirara kwalli ta goga jan janbaki a le’benta, tayi amfani da wasu had’addun pashion yari da abun wuya da hannu sai walwali takeyi, kasancewar ba ta iya daurin dankwali ba, kawai sai ta nannad’ashi ta daura kanta daurin da tayi ya fito mata da tarin suman kanta ba’kakirin sai she’ki takeyi abin sha’awa, Gefen bed ta nema fuskar nan kamar an aiko mata da mala’ikan daukar rai! kuka ma take so tayi abin duniya ya isheta..

Bai tunkari inda take ba sai da yayi wanka tukkuna ya Shirya jikinsa tsaf! kana ya fara duba Cctv domin ganin a wane irin hali take, Kawai sai ya ganta a kame a bed taci uwar kwalliya kamar ka dauketa ka gudu, sai dai kuma ya hango damuwa a tattare da ita, koda yake dai dama kullum cikin damuwar takeyi, maimakon ya fita kawai sai ya nemi guri ya zaune jikinsa dik yayi sanyi ya zubawa cctv din ido yana kallon duk wani motsinta.

Gani yayi ta mi’ke a hankali ta nufi bakin window ta d’age labule tana le’kawa…..Ya zubawa bayanta ido yana kallonta, Ta kai minti goma a tsaye a gurin kafin yaga ta juyo a gaggauce ta fad’a kan bed ruf da ciki ta cire dankwalin kanta tana ya mutsa gashin kanta, tana kuka da dukan katifar dake shimfide a bed din……Ya mike da sauri ya nufi dakin nata, Tanan nan yanda take tana wani irin kuka da dukan bed din sam! bata san ya shigo dakin ba…..Sunkuyawa yayi ya tattarota ta jikinsa, ta kalleshi fuskarta jage jage da hawaye! sai ta fuzge ta koma ta kwanta tana kuka da fad’in “Na shiga uku Allah ka kawo min a gaji.”!!! Sai yaji duk wani karsashi nashi ya sare ya zaune kusa da ita jikinsa yayi sanyi, shin wai yarinyar nan wace irin ‘kiyayya take masa da take wannan kukan da kiran ta shiga Uku! Hannuwansa yasa ya rike hannunwata dake dukan bed ya burkitota sosai ya jayota jikinsa, matseta yayi ya rufe mata baki da hannunshi guda, kawai ya zuba mata ido yana kallonta, hawaye sai kace ruwa ake akwara mata shatata kawai sukeyi.” Kimanin minti goma suna haka kafin yaji tayi sanyi a jikinsa kuma ta rage zubar da hawayen ya tallafo fuskarta tana kallon tashi fuskar, idanunta ta lumshe sam bata so ta kalleshi shi din ya kasance azzalimi ne a gurinta……”Me kike bukata nayi miki wanda zai sanya ki ki daina shiga cikin wannan yanayin na damuwa da tashin hankali? shin me kika nema kika rasa a gidan Ahamdu! menene nake miki wanda kike kiran kin shiga uku, Ki fad’a min dukanin bukatunki amma banda guda daya, ni kuma nayi miki al’kawarin insha Allahu zan yi kokari gurin ganin kin samu abinda kike muradi.”
Shiru tayi masa tana sauke ajiyar zuciya, ya dan dora hannunsa saman le’bunata jan! janbakin da tasa yayi mata kyau sosai burinshi ya tsotsi lebunan domin sun masifar bashi sha’awa, Gyaran mirya yayi yace.”Ke! nake sauraro!? Dan motsa jikinta tayi sai ya saketa ya cigaba da binta da kallo, ta gyara zamanta tana daura dankwalinta kafin tace”Nifa bana bukatar kudi ko wata kadara a gurin ka ni kawai ka rabani da wannan ‘kadarran auran ka takure min rayuwa ina rayuwa cikin kunci da damuwa, ka hanani hulda da kowa uwa uba mahaifiyata da ‘yar uwata na can guri daya ban san a wane hali suke ciki ba, ka kar’be min wayoyina ballanta na kirasu naji dadi, kullum ina cikin wannan uban gidan a kulle sai kace mayya! ni nagaji!! nagaji!! nagaji! kawai ka sakeni! na huta.”!!!! Ta’karashe maganar cikin wani irin kuka mai shashshe’ka.

Ya jima kanshi a ‘kas! yana jin wani irin d’aci! a ma’kogwaronsa, Yaji bala’in shaushin yanda take kiran auransu da kaddara! illah ‘kuruciya kenan! Sai ya dinta tuno had’addun ‘yan matan dake rubibinsa a da da yanzu yana watsar dasu, kusan kullum sai ya goge messages sama da ashirin da wani abu duka na matane wasu ya sansu wasu bai sansu ba basu ne a gabanshi ba shiyasa ma sam! baya tsayawa ya duba, ballanta ya basu amsa, haka al’amarin ubangiji yake da ya tashi jarrabarsa sai ya jarrabeshi da auran ‘karamar yarinyar da bata wuce ya haifeta ba gashi tana bashi wahala da fad’a masa dukanin maganganun da suka zo bankinta!!! Kokari yayi ya danne abinda ke damunsa ya dago kanshi yana kallonta tana kuka idanunta sunyi fululu! Ya zaro karamin hankici a a cikin aljihunsa, hawayen fuskarta ya shiga goge mata, tana kauda kanta hade da zumbura baki, sai da ya goge mata tas kana yace.”Zanyi miki abu biyu da kika bukata amma banda na farkon….Kwanaki idan baki manta ba ni Ahamdu na tabbatar miki da cewar Ni ba zan rabu dake ba kome za’ayi kuwa, maganar na baki takardar saki ki ajeta gefe guda, Maganar mahaifiyarki da ‘yar uwarki ni ban rabaki dasu ba, amma yanzu ki kwantar da hankalinki idan Allah ya kaimu gobe Ko Jibi ki shirya zan kaiki ki wuni tare dasu, maganar wayoyinki kuma, tuntuni na bayar dasu amma babu matsala idan mun fita zan siya miki wasu, maganar ‘karshe da zan fada miki itace Kada na sake jin kin kira auranan namu da sunan ‘kaddara idan ina kusa dake sai na fasa bakin ki! Ni wannan auran alkari nake so zama da samu kyakkyawar zuria da makoma, Saboda haka ki kiyaye kuma ki shiwa kawunki albarka a yanzu kuruciya ke damunki shiyasa kika kasa gane abinda ake so ki fahimta okey! nan gaba kadan nasan idan kinyi hankali zaki gane gaskiya.” Ita dai jinsa kawai takeyi tuntuni ta shiga tunanin yanda za’ayi ta tsira a ranar da suka fita dama babban burinta ta futa daga gidan to duk hanyar da zatayi ta kubuta ta sani…..Yace.”Yanzu kije ki wanke fuskarki ki sanya kwalli zakiyi bakuwa Hafsa ta kira waya tace xata zo dubaki.” Simi simi ta sauka daga bed din ta nufi toilet zuciyarta wasai! Allah Allah take gari ya waye ta samu ta ku’butar da kanta…

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE

[07/08, 10:55 pm] +227 98 36 59 34: ‘Yr Bngr Sys
45
‘Dan sulaika communication center
Nan yayi parking din motar kafin su fito sai da ya lalabi glass dinshi ya sakaye idanunshi saboda baya son sanya ido na jama’ar gari, fuskarshi dai ba ‘boyayya bace tunda gashinan pastes dinshi na yawo sa’ko da luko na cikin gari da kewaye, yasan tilas ya shiga gurin nan jama’a zasu shaida shi, Handbag dinta ta gyara kafin ta sanya hannu ta bude kofar motar tana kokarin fitowa taji saukar hannunshi a bayanta, mayafinta da ya fad’i kan kafad’arta ya gyara mata ma’ana ya d’ora mata saman kanta, Ta dan juyo tana masa murmushi, Dan ‘bata fuska yayi yace.”Wannan gyalan naki na tuna asirin tufafin dake sanye a jikinki bashi da sirri gare ki kuma kin san da haka kika dauki riga mai faffad’an wuya kikasa bayanki duk a waje.” Da sauri ta hau gyagygyarawa tana fad’in”Ai haka akayi yin d’in ki ba laifina bane.” Yace.”Wannan d’inki na banza ne, kyawun shi ki sanya a gidanki ba ki fita dashi ba kwata kwata ban lura ba sai yanzu dan haka ki zauna cikin mota in shiga in siyo miki wayar.” Marairaice fuska tayi”Dan Allah ka bari mu shiga tare na gyara wuyan rigar ai.” Tafada tana sake gyarawa…..Girgixa kanshi yayi ya dan zura jikinsa kan jikinta ya kulle motar kana ya bude bangaran da yake zaune ya fita daga motar ba tare da yace mata komai ba…..Kamar ta fashe da kuka, ta bishi da kallo tana jan tsaki! idanunta ya sauka kan wayayonshi dake aje, da sauri ta dauki daya hannu na rawa ta saka numbar As ta soma kira, As ya gane numbar dan haka da sauri ya dauka! Tace”As gamu cikin gate din ‘Dan sulaika ya shiga ciki zai siya min waya da badan ya kulleni cikin motar da tuni na fice sai dai ya dawo ya tarar bana nan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button