NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wata ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi a take taji zuciyarta tayi wasai! da jin wannan magana ta Camas! tace”Haka za’ayi wallahi ni ko nawa suka ce zan basu amma kin san inda gixo ke sa’kar tun sanda nazo ya dauke mim pose da wayoyina Atm dina na ciki yanzu ya za’ayi.”? Camas! tace.”Kinji wata matsalar kuma ko da yake babu damuwa nasan idan na sanar da As abinda ke faruwa ko nawa ne zai bayar saboda shima ya damu da rashinki wallahi baki ga yanda duk ya susuce ba.”
Da sauri tace.”Yawwa Dan Allah ki mai magana Camas! kuma ki shaida masa cewar wallahi ina fitowa to ya sanya ranshi cewa na zama tashi nayi masa wannan al’kawarin.” Camas! tace”Kar ki samu damuwa kawata ni zan tafi, kinga har na wuce mintinan da suka bani.” Mikewa tayi tana fadin”Don Allah ki gaishe min Da Uwani kice su kwantar da hankalinsu insha Allahu zan fito da wannan kurkun dana fada.”

Suna fitowa harabar gidan suka hada ido da Abdulmumini dake bawa shukoki ruwa yayi maza ya ajiye abinda ke hannunsa ya karaso inda take “Madam! akwai abinda kike bukata ne.”? Harara ta watsa masa ” Bakuwa nayi ko itama bani da damar yi mata rakiya.”? Girgiza kansa yayi ya koma bakin aiki. Tsayawa tayi ta fasa raka Camas din bakin gate dan ta lura yaron kamar munafiki ne me yiwuwa idan mai gidan ya dawo ya fada masa ta fito yanxu har shakkarsa takeyi saboda tana jin tsoron kar ya kara yi mata sha’kar mutuwa shiyasa take kaf kaf dashi.

Abdumumini yana bawa shukoki ruwa hankalinsa na kansu amma sam ba zaka fahimci hakan ba……”Camas! Ina ganin da kaina zan fara aiwatar da wannan aikin kafin ki sake dawowa ni zanyi kokari gurun ganin na kar’bi pose dina a gurinshi zan fara yi musu bayani duk sanda na samu sarari.”

Camas! tace”Yawwa kema kiyi kokarin yin haka nima mybe jibi ki ganni.” Shikkenan ki gaida gida dan Allah kar ki manta da sa’kona gurin su Uwani.” Camas! tayi gaba tana fadin”Insha Allahu daga nan can zan wuce domin na isar da sakonki.”

Abulmumini na ganin Wasila ta koma ciki sai yabi Camas! da kallo har ta isa bakin gate yana kallon sanda ta dan tsaya suna magana da Sundu’ki! na minti biyar kana taga ya bude mata karamar kofa ta fita….Al’amarin sai ya shiga bashi mamaki ya akayi suka bar wannan ‘yar iskar matar ta shigo gidan da kagani ba mutuniyar arziki bace amma babu shakka zai sanya ido sosai a kan lamarin domin shi ba zai yarda a cuci mutumin da ya rufa masa asiri ba.


Malam mao allo na komawa gida ya sanya babban danshi ya kira masa Kattime da Habibu domin ya shaida musu abinda ke faruwa…..Lokacin da ya gama zayyane musu irin tujarar da Uwani tazo tayi masa cikin almajiransa, dukaninsu sai suka hasala suka dinga zagin Uwani suna tsine mata, ganin yanda suka fusata yasa ya dakatar dasu da fadin”Ku saurara haka, sukayi shiru suna sauraransa sai mai da numfashi suke….Yace.”Idan anbi ta ‘barawo to abi ta mafi sahu! hakika muma muna da laifi babba kan wannan al’amarin da yake faruwa, Banga laifin Uwani ba akan abinda tazo tayi min na gane gaskiya kuma na amsa laifina da bamu wofintar da Yayan nan ba da babu abunda zai sanya ta samu damar zuwa cikin almajirai na ta fada mun magana, To d’an adam ajizi ne munyi kuskure sai dai mu kiyaye gaba kuma ni babban abinda ke daga mun hankali anan shine kada ta samu nasarar kashewa wannan yarinya auranta shine babbar damuwa ta.”
Kawu Habibu yace.”Insha Allahu hakan ba zata faru ba ni da kaina zan kira Alhajin a waya na shaida masa abinda ke faruwa.” Malam yace.”To alhamdullahi ga hanya mai sauki dama ina ta tunanin ya za’ayi mu sadu dashi tinda da numbar wayarshi kirashi yanzu sai muyi magana dashi.
Habibu ya fito da gudar dari biyu ya baiwa Musa babban yaron malam yace ya siyo masa kati can bakin kasuwa, Ba tare da bata lokaci ba Musa ya karbi kudin ya kama hanya ya tafi.

Suna tsaye tare da Khalifa cikin babban boutique dinshi mai suma A M B ma’aikata sun kai talatin ko sama da haka suna ta sauke kaya da alama an shigo da sabbin kaya….Shiyasa gurun ya hargitse da yawa, Wayarshi dake hannun Garba ta soma ringing, Garba Yayi saurin mika masa wayar ba tare da ya kalli mai kiran ba ya daga da sallama a bakinsa.

Jin muryar mai allo na amsa sallamar ya sanya ya dan risina kamar yana gabanshi ya gaishe shi kunya ce ta kamashi Tun ranar da aka daura aure bai sake waiwayar mutumin ba, Mai allo Yace.”Ina magana da Alhaji Ahamdu ko.”? Ahamd yace.”Kwarai kuwa arrama ni ne ayi min afuwa arrama al’amura sun sha kaina wallahi ina ta so na kira waya nayi bangajiya Allah bai nufa ba.” Malam mai allo yace.”Ayya ai babu komai Ahamdu. ku da kuke da hurd’od’i da yawa ai dole sai na muku uziri, dama wata magana ce ta taso shine nace to tunda ka bamu numbar wayarka bari na sanar da kai.”
Ahamdu ya dan bar cikin mutane ya samu ke’bantaccan guri ya tsaya yace.”Ina sauraranka malam.”! Mai allo yace.”Alhaji ba wai zan raba Wasila da mahaifiyar ta bane a’a ina so Yarinyar nan Wasila ta tsira da auranta, mahaifiyar yarinyar nan ta dauki alwashi kan duk rintsi sai ta lalata wannan auran domin ba ta da’de da barin garin garko ba, tazo har inda nake ta tabbatar min da wannan maganar shine na gaza samu nutsuwa nace bari na kira ka na shaida maka ka sanya ido sosai kana kuma ka tsaurara matakan tsaro kan shige da fice a cikin gidanka.”

Ji yayi jikinsa na tsatstsafo da gumi! Anya kuwa wannan Uwar arziki ce? Bashi da mai bashi wannan amsa, Dan haka sai yace.”Gaskiya naji dadin wannan magana taka arrama zan kara kula sosai nima ba zan raba Uwa da ‘Yarta ba amma mutukar naga tazo gidana da wata munufa to babu shakka zan sanya a hanata shigowa gidan.” Malm mai allo yace.”To masha Allahu Alhaji Allah yayiwa wannan auren albarka ka kula sosai insha Allahu zakayi alfahari da wannan auran.” Ji yayi ya kara jin kaunar mutumin cikin ranshi bai san abinda yasa yake son auransa da yarinyar ba kullum adduarsa Allah yasa auran nan yayi albarka shi kuwa zai yi kokarin ganin ya rike yarinyar da kirki duk wani alwashin da ya dauka a kanta zai sauke su…..Sallama sukayi da juna cikin mutunci da mutuntawa…..Ya katse wayar sai yaji duk hankalinsa yayi gida ya iske Khalifa tare da Manager suna magana yace.”Khalifa ka tsaya komai yayi Clearing ni zanje gida yanzu.” Khalifa yace.”Lafiya dai ko.”!? Yace.”Normal ba zan dade ba zan dawo insha Allahu.” Yana gama maganar ya juya da niyar tafiya Garba da Hadi suka rufa masa baya.

Ya dad’e tsaye a harabar gidan nashi a tsaye yana nazarin ko ina da ina na gidan…..Har masu tsaron kofar shiga gidan suka soma shan jinin jikinsu mussaman Sunduki da yayi ‘kas! da kansa yana Allah Allah ya bar gurin babu shakka Alamun mara gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake domin dai Sunduki wani irin gumi ne yake karyo masa yana jin tsoron kar yallabai ya fahimci abinda ke da akwai!!!! AbdulMumini ya karaso inda yake tsaye hannunsa rungume da tarin kayansa wanda ya wanke su tas ya gogesu ya shiryasu cikin wata leda mai sheki! gaisawa sukayi Ahamdu na tambayarshi aikinsa. Abdumumini yace.”Aiki alhmdullihi Yallabai.” Ahamdu yayi gaba da niyar shiga cikin gidan Abdulmumini ya rufa masa baya hannunsa rungume da kayan wanki……..Dan juyowa yayi yace.”Dakata nan tukkuna.”! Abdulmumini yaja ya tsaya, A hankali ya sanya hannunsa jikin kofar yana latsawa……Tana can cikin daki a kwance abin duniya ya taru yayi mata yawa taji alamun ana so a shigo da sauri ta diro daga gadon ta nufi kofar fita, Allah yasa tayi wanka ta shirya cikin wani les mai ruwan goro (orange colour) yayi mata kyau sosai yayin da dinki ya zauna das a jikinta, sai kace an gwadata bata daura dankwalin ba sai ta lullube jikinta dashi, tun kafin ta karasa bakin kofar palon ta hangoshi tsaye dake kofar tana nuna mutum amma shi wanda yake waje bai ganin na ciki sai dai na ciki yaga mai shigowa, Ta bude a hankali taja gefe guda ta tsaya, juyawa yayi kawai ya kar’bi kayanshi dake hannun Abdulmumini ya sallameshi da fadin”Jeka kawai.” Abdulmumini ya bar daga gurin da sauri….Shigeta yayi ba tare da ya tanka mata ba ya nufi bedroom dinshi…..Yana shiga ya tadda shimfidar bed din a hargite duk pillows din sunyi d’ai-d’ai kasan kafet din ragowar abincin da taci ga plate da goran ruwa da lemo duk a ajiye ko ina yayi kaca kaca babu kyan gani…..Wardrobe dinshi ya bude ya ajiya kayanshi yana dan jan tsaki ya fito ya sameta zaune kan kujera ta zuba tagumi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button