NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Rashida ta tinga share hawaye Hafsa na rarrashinta, Ita kuwa Wasila idanunta bushewa sukayi ‘kamas! hausawa sukace da wata wuyar ai gwara wata ita yanzu wace irin wahalace bata sha ba shiyasa sam bata damu ba tana ganin Allah ne mai rayawa da kashewa.

Cikin nasara akayi mata aiki aka fitowa da ita dakin da suke sistar Aliya tace ta zauna ta huta tukkuna sai sai su tafi gida amma kuma ta kafa mata sharad’ai sosai kan dole ta kula da kanta babu aikace akaice da zurga zurga sannan kuma ta daina zama da yunwa ta kuma nemi magunguna na karin jini.”

Bayan fitar Aliya daga dakin, Khalifa ya dinga tausarta yana bata hakuri kana yace tunda haka ta kasance cewar tana da cikin Ahamdu to lallai zaiyi mishi bayani domin ya sani….Tace”Ni dai bana so ka fada mishi don Allah ka bari duk ranar da Allah ya saukeni lafiya sai ya sani amma bana so yanzu ya san inda ciki a tare dani…..Khalifa yace.”Hujjarki zaki fada min da kike cewa bakya so ya sani? mutum da abinshi, ai ya zama dole ma ya sani idan sanadiyar cikin yasa ya mayar dake dakinki dama haka muke so.” Tace”Bana son haka nafi so kowa Allah ya hadashi da dai-dai dashi dama kaddarar wannan cikin ne Allah ya hadani dashi duk sanda na haife shi kuma zai bashi abinshi.” Khalifa ya girgiza kanshi yana kallon tsananin wauta da rashin wayo a tare da ita.

Hafsa da kanta ta fita bakin asibiti ta shiga wani kanti da suke siyar da dogwayen riguna da hijab ta siyo mata riga kala biyu da hijab biyu sai pants da audiga…….Zeey sai jin haushi takeyi tana ganin duk ‘yar uwar tata ta ‘bata musu lokaci gurin wata shashashar da basu da hadi da ita taji zafi sosai dan ganin yanda Hafsan ke ta rawar jiki kan Wasilan…….Jikinta babu kwari suka fito daga dakin….Khalifa ya bude musu motarshi suka shiga, duk gabad’ayansu….Yaja motar suka fita daga asibitin

Har cikin gidan ya shiga da motar, Uwani ta fito ta tsaya dama yini tayi cikin fargaba da tashin hankali ganin ‘yayan nata sun fita tun safe amma yanzu gashi har karfe shida na yamma basu dawo ba dalili kenan da ya sanya hankalinta tashi…….Fitowar Wasila daga motar yasa ta fuskanci da akwai matsala, sai dai tayi kokarin kar’bar su khalifa hannu biyu suka shiga cikin gidan

Khalifa ya shaida mata shi din abokin Ahamdu ne ya kuma shaida mata abinda ya faru da Wasilar shine dalilin da ya sanya ma suka dade basu dawo ba, Sai kawai ta tsinci kanta da yi masa godiya har muryarta na rawa, wato ita tanan sake da baki ‘yarta zata mutu akan titi lallai akwai mutanan arziki a duniya…….Khalifa ya shaida mata abinda Dr Aliya tace dangane da ita Wasilan dole sai an kiyaye an kuma sa ido, har sai sanda cikin yayi kwari tukkuna….Uwani tace”Insha Allahu za’a kiyaye….Yace.”Insha Allahu zan sanar da Abokina abinda ke faruwa mybe ma gobe mu shigo dashi ko da daddare nasan yaji labarin cikin nan zai bukaci sanin abinda ke faruwa….Uwani tace E hakan nada kyau sosai dan muma munyi wannan maganar kuma munje can gidan nashi domin mu shaida masa sai da bamu sami ganinsa haka muka dawo gida.” Khalifa yace.”In sha Allah zai zo da kafafunshi kar ku damu…Kudi ya basu kimanin dubu ashirin yace su rike a hannunsu tukkuna, kana ya mike Hafsa dw zeey ma suka mike suna musu sallama, Wasila da kyar ta mike tsaye domin rakasu, godiya kawai takeyi dan ta rasa ma da wace kalma za tayi amfani lallai yau taga ranar d’an adam Khalifa da matarshi nada hali irin na mutanan arziki.

Tun a cikin mota Khalifa da Hafsa suke mamaki ikon Allah kenan! Hafsa tace”Shiyasa ba ba’a saurin yin saki komai ‘bacin ran da mutum yake ciki kafin ya yanke hukunci ya samu nutsuwa, ko ni anan gurin naga wautar governor wallahi duk dai komai kaga ya faru da mutum kaddara ce amma dai rashin hakuri shike jawo wani abun, yarinya karama da ko 2years bata cika ba take fuskantar kalubale irin wannan Allah Abban Afnan da ba dan zuwana asibitin nan da sai da cikin nan ya zube in ba wani tsananin rabon ba.” Khalifa yace.”Tun yaushe nake nuna masa gaskiya ya’ki fahinta kin sanshi fa taurin kai gareshi sai abu ya kwabe yazo yana nadama ni wallahi na yarda da tuban yarinyar nan bana haufi a kanta kuma ina masa sha’awar ya mai da dakinta tunda dai har rabo ya shiga tsakaninsu………Tace”Aikuwa dai amma ina jin idan yaji labarin tana da dauke da cikinsa zai sauko zai kuma so ya dawo da ita duk domin cikin jikinta.”

Khalifa da Hafsa har suka isa gida suna zancan Cikin wasila da yanda ta basu tausayi Zeey kam dama tun a hanya ta sauka tace zataje gidansu friend dinta sai suka sauketa ta samu abun hawa ranta a ‘bace! sosai take kishin Wasila da ita da abinda ke cikinta.

Duk rashin imani irin na Uwani sai da ta tausayawa ‘yar tata ta dinga rarrashinta taci abinci tasha magani sai ta kwanta, Wasila ta dinga mamaki ashe Uwani dama nayi mata irin wannan son, taji kwalla ta taru a idonta, tana so ta faranta ran uwarta da ‘yar uwarta amma babu hali Kudi suna suke magana, gashi kuma ita tayi al’kawarin barin harkar dake kawo mata kudin da suke jin dad’i.

Bayan sallah isha’i Khalifa na shirin zuwa gidan Abokin nashi motar shi ta shigo gidan……bayan motar ta tsaya Garba yay gaggawar bude masa motar ya fito….Khalifa ya karasa gurinshi tare da mika masa hannu yana fad’in “Fitowar nan da nayi, nayi ta ne da niyar zuwa gidanka sai gaka kazo.” Yace.” Okey Allah yasa alkairi ne zai kawo ka.” Khalifa yace.”Idan kaji ana alkairi d’aya kenan muje ciki.” Suka jera a tare suna tafiya domin shiga cikin gidan kai kana kallon yanda suke mu’amula kasan abokai ne masu tsananin zumunci da kaunar junansu.

Littafin na kudi ne……!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[14/08, 12:04 pm] Farida Books: ‘Yr Bngr Sys
56
Hafsa ta gansu sun shigo tare sai ta saki fuskarta sosai tana dariya tace”Sannu da zuwa gwara da Allah bai sa ka bawa mijina wahala ba kazo dama bana so ya fita ya barni ni kaina a gida naji dadin zuwanka.” Ya danji wani iri da jin maganar Hafsa!wato shine mara galihu kenan wanda bai da mata mai tattalin sa yana yawo da daddare babu me cewa dan me.”?

Kan kujera ya zauna yana jan kafafun Afnan dake kwance kan kujerar tana kokarin yin barci, jin muryarshi yasa ta bude idonta a hankali ta shige jikinshi tana fadin “Dadyna yaushe kazo ina Aunty Amaryata.”? Rungume ta yay yana shafa kanta yace.” Baby Afnan iya rigima baki bacci ba.”? Kai ta daga mishi tana lumshe idonta….Hafsa tace”Yanzu nan ta gama rigima ai ta gaji ta kwanta tana son yin bacci ‘kiriniya da fitina a gurin Afnan sai a hankali.”

Dan hararata yay yace.”Ke waye yasan abinda kikayi kina yarinya gwara nata me sauki ne.” Hafsa tasa dariya tare da wucewa daining tana fad’in “Governor da Afnan kenan ai fada a shirya.” Shima dariyar yake yana shafa kan Afanan din yana lallabata tayi bacci.

Khalifa ya zauna kusa dashi yana me cire halar kanshi da fad’in”Yau na sha zurga zurga Wallahi da tun safe ban zauna ba.”

Yace.”Shiyasa nayi ta tsammanin shigowarka naji shiru kasan dai maganar nan ba zata yiwu ta waya dole sai mun tattuna akai , Alhaji Danliti ya matsa min da kiran waya kan dole sai mun bashi rancen kudi har miliyan saba’in wai zai shigo da kaya, kudinshi sun yanke kasan sam bana son mu’amula dashi saboda bai da dad’in sha’ani.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button