NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wasila tace”To shikkenan Innata nagode sosai babu shakka duk wanda ya rasa iyaye a duniya dole yayi kuka.” murya na rawa ta ‘kare maganar.
Inna hajara tace”To meye abin kuka kuma mu dai kullum fatanmu ki zauna dakin mijinki lafiya kiyi masa biyyaya domin ki samu rabauta duniya da lahira, itama Rashida addua muke kan Allah ya kawo mata miji nagari kamar naki.”
Wasila tace”Ameen Inna insha Allah Rashida zatayi aure komai nada lokaci dama.
Tace”Inna gaskiya bazan boye miki ba naji dadi sosai da faruwar wannan abu Kawuna Malam zai auri Uwani wallahi ji nake tamkar babu wanda ya kaini farin ciki da faruwar al’amarin.
Inna Hajara tace” Shi al’amarin Ubangiji dama haka yake ai Allah ya kaddara akwai aure tsakanin Mahaifiyarki da Malam babu abunda zamuce sai dai muyi fatan alkairi shi kuma Yahuzu Allah ya jikansa ya gafarta masa.”
Tana goge hawaye ta karashe maganar, itama Wasila taji zuciyarta na kokarin karyewa tuno mahaifinta da tayi sai dai kawai ta daure ta cigaba da yi masa adduar samun rahamar Allah a cikin zuciyarta.
Inna Hajara bata bar gidan Malam ba sai da ta tabbatar da Wasila ta shanye roman ‘yan shillan nan sannan tayiwa Bitan Sallama ta tafi gidanta.
Koda malam ma ya dawo suka ke’be suna sake gaisawa da tambayar bayan rabuwa Wasila tace”Malam ji nake kamar nafi kowa murna da farin cikin da kasantuwar wannan abu kai da Uwani Allah Ubangiji ya sanya alkairi a ciki.”
Mai allo ya dinga amsa cike da walwala da farin ciki, Yace.”Hakan shine suttura da kuma mutumcin mahaifiyar taku.”


Sai bayan goma da rabi ya shiga gida a gajiye sosai dan bayan sun bar garin Garko can ‘karamar hukumar Gaya suka Wuce shi da Khalifa da jama’arsu, sai yamma lis suka dawo saboda yasan masu gidan basa nan yasa ya yada zango guest house dinshi Khalifa ya zauna yana d’eba masa kewa Sai da Hafsa taga dare yayi mijinta bai dawo ba ta kirashi a waya, sannan ne suka rabu kowanne ya tafi gidanshi

Yana sane ya’ki kiranta a waya sabida yana so yaga shin zata manta dashi ko a’a bini bini zai duba wayarshi babu text dinta babu kiran wayarta gashi sha biyu na dare har ta wuce……..Allah sarki Wasila tana can network ya sakata a gaba tun bayan tafiyar Inna Hajara take ta kiran numbarshi tana ‘kin shiga ko kuma data fara ringing sai ta katse har kuka tayi saboda bakin ciki kowa na kwance a daki cikin dare ta fito tsakar gida wai ko dakin ne babu network nan ma tayi tayi kiran baya tafiya, sai ta koma daki ta kwanta lamo tamkar mara lafiya bini bini ta duba wayarta ko zataga test dinshi shuru duk ta rasa abinda ke mata dadi da kyar bacci ya dauketa.

To shima nashi ‘bangaran hakane, da kyar bacci ya daukeshi wanda tun yana saka ran ganin test dinta ya cire ya rungume filo kamar wani maraya yana fizgo bacci da karfi, gabadaya gani yay dare yayi mishi tsayi, dan haka uku da rabi nayi ya tashi yaje ya dauro alwala ya hau dadduma yay nafila, kafin ta dauki cazbaha ya wuce masallaci.

Da safe da kyar ta karya duk takaici ya isheta, ga mutane sai shigowa sukeyi wai sunzo gaisheta sai kawai ta koma daki ta kwanta tace da Rashida duk wanda yazo tace musu bacci takeyi.
Haka kuwa Rashida ta dinga sallamarsu, da cewar bacci take wasu masu naci zama sukeyi wai sai ta tashi sun gaisa da ita Wasu kuwa sai suce bari su tafi sa dawo da yamma.
Wasila na ciki tana ta famar kiran wayar tashi wannan karon tana shiga sai dai kuma bai daga ba, nan ma zuciyarta ta sake hasala ta goge hawaye tana mikewa zaune……Sake kiran wayar tayi a karo mara adadi dai-dai lokacin da ya fito daga toilet da alama wanka yay dan ga jikinsa nan duk ruwa, da sauri ya karasa inda wayar take ya dauka, ajiyar zuciya ya sauke ya zauna gefan bed kana ya daga wayar.
Kuka ta fashe dashi harda shashsheka, yaji duk jikinsa yay sanyi gabakidaya a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka….
A tausashe yace.”Menene.”? Tace”Me yasa ka ki daukar waya zuciyata kamar zata fashe.”
Ya sauke ajiyar zuciya yana furzar da wani huci daga bakinsa, yace.”Sai kuma kiyi kuka babu sallama da gaisuwa da tambayar yaya na kwana.”?
Tace.”Duk hankalina ne a tashe wallahi zuciyata sai sa’ke sa’ke take min.”
Yace.”Ina Mommyna.” A hankali tace”Tana can gurin Bitan.”
Yace.”Kun tafi kun barni da damuwa ko.”? Tace.”Wallahi nima da kyar nayi bacci ban san haka nake sonka ba sai da na kasa samunka a waya ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo inda kake.”
Yaji wani irin dadi na ziyartasa, yace.”Nima haka naji na kuma gane kece mahad’in rayuwata.” Dariya tayi tace”Nagode mijina, yanzu kayi break fast ko.”
Yace.”Nakasa komai tunda na tashi kinga ni da kyar ma nayi wanka.” Tace.”Wayyo babyna da ina nan Wallahi ni zanyi maka wanka in rungumeka in shafa maka mai in saka maka kaya.”
Yayi wani killer smile kafin yace.”Tunda ni baby ne idan kinyi min wanka kin shafa min mai kuma kin sa min kaya sai ki bani nono nasha ko.”
Ta saki dariya da shashsheka tace”Allah da ina kusa zan baka kasha.”
Yaji tsigar jikinsa ta tashi Yace.”Mu bar wannan maganar kada kisa nazo inda kike yanzu.”
Ta ‘kyal’kyale masa da dariya tace”Ai dama kaina ka fara maganar.” Yace.”Tom na daina maganar.” ya cigaba da cewa yau zan tafi katsina amma kuma komai dare zan dawo insha Allah.” Tace”Wayyo Habibi Katsina me zakaje kayi.”? Yace.”Zanje Gurin abokina mana mutumin da yazo dubaki lokutan da baki da lafiya.”
Jiki a sanyaye tace”To Allah ya tsare min kai ya dawo da kai lafiya.” Ya amsa da “ameen.” Yace.”Kinga yanzu na dan samu sassauci zan iya cin abinci sabida kin bani kulawa duk da bakya gabana naji dadi sosai Allah yay miki albarka.”
A nutse tace”Ameen.” Bari na bari ka nutsu kayi break sai na sake kiranka ko.”
Yace.”Okey my Princess! Murmushi tayi ta kashe wayar tana fad’in “Nazama gimbiya kenan…..Cike da nishadi ta fito tsakar gidan gidan malam ta cigaba da hada hada da jama’a masu shigowa.

Gangami!! da turnu’kun!! haya’ki!!! nake hangowa kan titin zuwa gidan gomnati wato government house, mutane sunfi dari biyu sun kashe titi sai ‘kone -‘kone sukeyi suna tada ‘kura gami da ‘kona tayoyi suna watsa fetur suna ‘kyasta ashana, sai ihu sukeyi suna buga ganguna, guri ya hargitse da hayaniya gami da haya’kin! wuta, dan wasu ma har sun soma galabaita duk da sune suka saka kansu abunda sukeyi din basu sare ba so sukeyi su shiga cikin government house din domin su cimma manufarsu kan mai girma governor Lawan Rabo, mafi akasarin jama’ar da suka tada wannan tarzomar iri-iren wad’anda aka rusawa gidaje ne da masana’antu gurun aikin titin jirgin ‘kasa wanda ko rabin aikin ba’ayi ba an dakata gashi su kuma anyi musu al’kawari za’a biya su diya shuru kakeji malam yaci shirwa kullum ‘karya daban ta gobe daban sam basa gajiya da shiga gidan redio suyi karya, sukuwa suka ga rainin hankalin yay yawa kawai suka yanke wannan hukuncin duk da sun san wannan abun da sukeyi din xai iya barazana ga rayuwar wasu daga cikin amma dai duk da haka sukaji suka gani domin suna so su kwaci hakkinsu da’aka danne musu,
Mai girma governor Lawan Rabo hankalinsa yay masifar tashi sosai ya lura Jama’ar Jahar kano suna so su ga karshen sa dan duk abinda ke faruwa a kan titin yana gani ta cikin CCTV Dan haka sai kawai ya umarci Securities kan suje suyi aman wuta da alburusai a gurun wanda kwanansa ya ‘kare shi ya jawo kansa.
Ba tare da ‘bata lokaci ba kuwa, Police din gidan gomnatin suka shiga motocinsu suka durfafi kan titin suna sakin harbi ko ta ina!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button