NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Camas da Silinda sabuwar yarinyar dasu As suka samu kenan wacce ta zama makwafin Wasila dan abinda Silinda takeyi wane Wasila, tunda Silinda tazo government house suke fad’a da Camas! dan ganin komeye za’ayi sai a turata gefe guda Silinda itace a kan gaba, ko yawonsu sukaje na campaign Idan sun dawo Silinda ake bawa kudi ita kuma ta bata abinda tayi niyya shiyasa kullum suke cikin fad’a da juna, Camas! ta kare mata dan duk ‘yan kud’ad’en da take samu sun ‘kare ‘yan damfara sun damfareta kowa ya samu rabonsa yanzu motar kanta bata da ita manya sutturunta ta kwashe ta kaisu gurin mata na kasuwar rimi ta siyar a banza a wofi dan idan ba tayi shaye shayenta ba bata jin dadi, gashi governor kwata-kwata yanzu ya daina sakin kudi kamar da suma su As din lallabawa suke domi

n governor Lawan Rabo ganin yanda jama’ar gari ke masa tawaye ta kowane fanni yasa yasha Jinin jikinsa yana ganin da wuya ya kai labari dan tuntuni ya sare da al’amarin saboda kusan kullum idan ya fita sai jama’ar gari sunyi masa ihu anyi fad’a da ‘kona ‘kone dan akwai wani matashi ma da yay kundumbala yayi tsale kan titi motar da yake ciki na gudu ya d’aneta sai da ya fasa gilashin motar da wata shar’bebiyar wukarsa wai sai ya kasheshi yayi masifar tsorata da al’amarin ya kuma fahimci cewar jama’ar jahar tashi a shirye suke da shirin ko ta kwana suna jiran lokacin za’be yazo yasan idan yace dole sai ya zarce to zasu iya halakashi, a take securities din da suke tare da governor din suka farwa wannan matashin da duka sai da sukayi masa jini da majina tukkuna suka daddaureshi suka kaishi suka kulle.

Silinda ta kaiwa Camas! wani bahagon mari wanda ya sanya shatin hannunta suka fito rad’au! Camas ta rike kumatunta tana wani irin huci tace”Me nayi miki kika mareni.”? Silinda ta hau cusa mata ashar tana fad’in “Waike wace irin dabbace shegiya kawai wane kudi kuma zan baki jiya da muka dawo ba na baki dubu goma ba shegiya kawai wacce babu abinda ta iya sai shaye shaye.”
Camas na ‘kwallah tace”To ina ruwanki idan ina shaye shaye da kudinki nakeyi macuciya kawai tare fa muke tafiyar nan amma idan an bamu kudi mu raba sai dai ki bani abinda kikayi niyya jiya a gabana ina gani As ya baki dubu hamsin yace mu raba sai ki bani dubu goma saboda ke ‘barauniya ce!.”
Silinda na cije baki tana hura katon hancinta tace”Wallahi Camas kika sake wata magana anan gurin sai na hanaki shigowa wannan gidan kin san dai yanda kusancina yake da governor zan iya tozartaki wallahi gwarama ki lallabani ki zauna lafiya kina gani duk taurin kai irin nasu kwage da Mada sun sallama min ballanta ke banza galli ga horo.” Camas ta sha’ki hanci! tana jin wani irin takaici a ranta ta girgiza kanta ta wuce ta bar gurin tamkar kububuwa.”
Silinda taja tsaki tana tsartar da yawu ta wuce ta nufi inda motarta take tana karkad’a key.
Ta fito daga cikin gidan ta hangi Camas na tafiya a ‘kafa takalmin ‘kafarta na gurd’eta, Dariya tayi hade da buga sitiyarin motarta tazo ta wuceta fuuuuuuuu! Camas! ta tsorata da sauri ta matsa gefe tana cizar yatsa(Hausawa na cewa idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi dai-dai da kai dan watarana kaine zaka fada ciki)


Malam Mai allo
Yau kusan sati guda kenan yana irin mafarki guda daya, kawai sai ya yanke shawarar yin istahra domin yana so zuciyarsa ta amince masa da abinda yake gani cikin mafarkinsa, karfe daya na dare ya tashi ya daura alwalarshi a nutse ya gabantar da istahara kamar yanda annabi ya koya mana, ya nade dadduma ya koma ya kwanta bacci, cikin iko n Allah sai dai ya sake yin irin mafarkin da yake yi dai shi da ita wannan karon ma gashinan har da albarkar haihuwa dan yaro ‘karami ya gani a tsakaninsu, zuciyarsa ta aminta da abinda Allah yake nuna masa cikin mafarkinsa tsayin sati guda, tabbas jikinshi na bashi alkari ne tartare da al’amarin, kawai sai ya yanke shawarar tunkarar inda take ya cire fargaba da shakku gami da tsoron kada tayi masa rashin kunya kamar yanda ta saba.

Allah ya tabbatar mana da Alkari


Bayan ta idar da sallah isha’i ta nufi kicin, abinda ta ajiye a frdge ta dauko ta fasa madara gwangwani guda biyu ta juya kan damammiyar kabewar nan ta juya sosai ta hade jikinta sai ta zauna kan wata kujera a kicin din ta shiga sha a hankali a hankali tana lumshe idonta, za’ki za’kin kabewar da gard’in madarar na ratsata,( Macen dake yin irin wannan had’in tana sha to za tayi gard’i tayi za’ki sosai sannan gabanta zai ciko kuma zata dinga jin sha’awa a kai a kai zakiyi ni’ima wacce maigida zai dinga sakar miki ihu yana sa miki albarka)

Sai da tasha sosai sannan ta mayar da ragowar fridge ta bud’e ji’ka’kken kaninfarin data ji’ka ta sanya cup madaidaici ta d’ebo ta xauna ta shanye tas ta ajiye Cup din ta fita daga kicin d’in.

Tana ‘kokarin shigewa bedroom dinta Hajja tace”Zo ki kar’beta ki bata nono tasha tin dazu take kusurkusur kin san idan ta fara tsandara ihu to ba zamuji da dad’i

ba.” Tace”Hajja da wanka nakeso nayi wallahi.”Hajja tace”A’a kada a shiga hakkin yarinyar nan Wasila zo dai ki fara bata nono tasha.”
Sai ta zauna kusa da Hajjan tana fad’in “Gaskiya Hajja duk sanda kika tafi zanji jiki wallahi Allah yarinyar nan zata hanani komai da komai na rayuwa ita dai komai nono.”
Hajja tace”Aikuwa dai tafiya ta ta zama dole dan gobe i yanzu ina gida.
Ta dan marairaice fuska tace”Yanzu Hajja da gaske dai gobe zaki tafi.”? Tace”To me zan tsaya nayi gobe zan wuce insha Allah da safe zanje can gidana zanyi aikin wainar gero da za’ayi sadaka da ita, tunda Allah tasa kin yada ganye lafiya lau ai dole mugode Allah.”
Tace”Hajja meye amfanin yin sadakar.”? Hajja tace”Wasu na cewa al’adace amma ni yanda na dauki al’amarin ba al’ada bace dan kayi sadaka ranar da ka yada ganye hakan na nuna cewar kana farin ciki da abinda Allah yay maka kuma duk yaron da ka bawa sadaka yaji dadi zaice Allah ya raya ya d’ayyaba.”
Rashida dake danna wayar Wasila tace”Gaskiya kam ai sadaka maganin masifa ce ba laifi dan kayi sadaka lokacin da kake cikin farin ciki ko kuma ubangiji yay maka wata kyautar.”
Hajja tace”Ai kowane mutum da irin fahimtarshi wasu mutanan babu ruwansu da yin irin wad’annan abubuwan.”

Shigowarshi palon ce ta katse musu zance da suke, Hajja tayi mishi sannu da zuwa Rashida ma haka, ya amsa yana kokarin zama kujerar dake fuskantar Wasila, carbin dake hannunsa ya nannad’e a hannunshi Hajja tace.”Jiki yay kyau kenan tunda gashi har ka iya zuwa massalaci.” Yace.”Alhamdullhi Hajja yanzu babu zazza’bin sosai sai dai ciwon kai kad’an kad’an!
Tace”Allah ya sawa’ke.” Amsawa yay da “ameen.’ Yana mai da hankalinsa kan Wasila dake kokarin gyara rigarta tace” Hajja kinga bacci za tayi ma.” Hajja tace”To ai sai a goyata dan yanzu tunda tayi bacci da wuri kika kwantar da ita to idan ta gaji da kwanciya zata hanaki bacci da daddare.”
Rashida tace”Kawo na goyata.”
Tana kokarin mika mata yarinyar yace.”Bani ita nan.” Ta mi’ka masa ya d’orata saman kad’arshi yana shafa bayanta……Hajja tace”Aikuwa ka sabawa da yarinyar nan da haka to zaka sha wuya dan idan taji dad’i to cewa za tayi ba zatayi bacci a ko ina ba sai a kirjinka.”
Yace.”Hajja wannan goyon ne ni bana so sai naga kamar ana takure ta wallahi.”
Hajja tace.”Babu maganar takurewa, da goyo na kisa da duk baku rayu ba, dan kai d’in nan da kake gani babu irin goyon da baka sha ba a bayana.”
Yace.”Allah Sarki Hajja Ubangiji Allah y saka da alkairi ya kara miki nisan kwana.”
Ta amsa da “amee.” Tana murmushi hade da tuno lokacin kuruciyarshi sai da ta share hawaye a fakaice data tuno mahaifiyarshi Yafindo mutuniyar kirki Allah dai ya jikan musulmi.”
Mikewa yay ya nufi bedroom din Wasilan da babyn a kafadarshi, shuru dakin sai Uban ‘kamshin turaran wuta yakeyi
Turaran Wuta ne dana tsuguno wanda Hafsa matar Khalifa ta kawo mata kwana uku da haihuwarta bata ta’ba amfani dashi ba sai yau, mafi akasari tafi anfani da air freeshnar da tirare na tsinke koda ta haihu da irinsu ta dinga amfani yau kawai tayi sha’awar sanya na gurin Hafsa tana sanya shi kuwa dakin ya game da ‘kamshi mai dadin gaske, turare ne wanda yaji kayan hadi ya kuma ji madarar turare ‘yar gasken had’e ruwan ji’ko turarene da manyan mata ke amfani dashi, shi na tsugono d’in nada bala’in kyau sosai yana sanya gaban mace ya tsuke! yayi ta masifaffan ‘kamshi, Allah Allah take ta fito daga wanka domin ta tsuguna kan turaran domun Hafsa tayi mata bayani dallah dallah cewar idan ta tsuguna kan turaran sai ta goga miski a gurin idan tayi kwana uku tana yin haka ita kanta zataji sauyi sosai dan gurin zai nuna alamun tamkar ba’a ta’ba haihuwa ba.
Tana fitowa kawai sai ta ganshi a zaune, gabanta ya fadi sosai gaskiya ita bata son haka to me kuma za tayi mishi da zai kama ya shigo mata daki……Ya dinga binta da kallo har ita isa gaban mirror towel din na ‘bantarewa daga jikinta cinyoyinta na fitowa, rasa inda zai saka kansa yay sai kawai ya kwanta saman bed din hade da d’ora baby zahra saman cikinsa ya rintse idanunsa gam! yana sauke ajiyar zuciya yana jin yanda joystick dinshi ke wani irin harbawa……Ganin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button