NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Gyaran mirya yayi a nutse yace.”Ina so ki fad’amin nawa aka biya ki kika tsunduma kanki a wannan harka ta jagaliya ki fada mun ko nawa suka baki ni nayi miki al’kawari zan nin ka miki abunda suka baki ko sukayi miki alkawarin mutukar zaki dawo kiyi harkar ta siyasa mai kyau, da tsari!

Ta mike tana karkad’e hijab d’inta ta kalleshi ido da ido tace”Ni! bana jagaliya siyasa nake tsaftacciya kuma kai baka da kudin da zaka iya biya na kan wannan harkar.”

Murmushi ya saki yace.”Kina bani tausayi yarinya baki san waye Ahamdu ba ko.”? Tace”Saninka ba zai amfana min da komai ba tunda nasan anayi siyasa ne da ra’ayi ni bana ra’ayinka kuma baka isa kasa ni na sauka daga a’kida ta ba.”

“God.”! yafada yana tafa hannunsa ya kalleta da kwantaccen murmushi a fuskarshi yace.” Gaskiya kin burgeni yarinya kuma ana siyance ana son mutum mai a’kida ni kaina idan da zan samu abokin tafiya irinki da naji dadin harkar ammafa ni yanda na dauka kin tsunduma kanki wannan harka ne domin cimma wata manufa taki.

“Kwarai kuwa akwai manufofi da nake dasu akan wannan harkar wanda ni kadai na barwa kaina su ina so kuma Allah ya cika min burika na.”

“Masha Allah shin meye sane kuka daura tuntuninku akaina kuka tsawwala min sai kace ni kadai ne dan takarar Governor dake takara da governor ku me yasa duk inda nake kuna bibiyata da al’amurana saboda tsabar bin diddigi irin naki har gida kike biyo ni kina kokarin ci min mutunci shin wai me kuka dauki wannan harkar ne.”!?

Wasila tayi shiru yace.” Siyasa ba hauka bace! wad’anda suka san abunda sukeyi sunayi ne kan tsari amma ke naga kina so ki wuce gona da iri saboda talauci yayi miki katutu shiyasa kike ganin zaki iya zagin mutum kamar ni wanda yake da shekarun da suka nunka naki sau uku, okey nasan babu abunda ke damunki sai jahilci da rashin mafad’i to wannan shine lest winning na ‘karshe kada! na sake ganin wad’annan kafafun naki a gidana duk ranar da kika sake kuskuran shigo min gida to a ranar ki kwana da shirin wad’anann kafafun naki ba naki bane dan sai na sanya an ragargaje su! in yaso sai naga kafafun yawon Banga ban hanaki ki zageni ba ko ki jefe ni kije kiyi tayi idan kin cimma burinki nasan zaki bari gidana dai ban lamunce in sake ganin kafafunki a ciki ba.”

Maganganunsa sunyi mata zafi sosai! ta kalleshi tana girgiza kai “Jagaliya da Banga yanzu na fara.” Tana fadin wannan magana sai tw zuge jakarta ta zaro kudinshi na jiya ta jefa masa “Wannan kudin da ka bawa Mamana da kanwata basu ishemu kallo ba saboda aban bamu wanda yaf………. Taji saukar Wani bahagon mari a kumatunta! A razane! ta dafe fuska idanunta yayi jawur! Ya dam’ki! wuyanta ya sha’ke cikin hijab…..Ta dinga kyarma! tana kyafta ido!! Ganin idanunta sun soma shagid’ewa ne ya sanya ya saketa sai ta fad’i a gurin ragwajab! tana kakari! tare da rike ma’kogwaronta! kanta ‘kas!! ya tsugana dai-d’ai kafafunta, A kausashe yace.” Har yanzu baki san waye Ahamadu ba ko! ni zaki jefa da kudi! ke! wai shin ma dame kike takama ne.”!!! Wasila tayi shiru bakinta ya mutu har yanzu ma’kogwaronta suya yake mata wai! sauran kadan ta bakunci lahira……”Wallahi wallahi duk ranar da kika sake gangancin aikata min abu makamancin wannan sai kin raina kanki in yaso su wad’anda suke daure miki gindi su same ni da kansu ni bana tsoron kowa kije ki fada musu basu isa nayi dake ba su zasu zo da kansu mu fafata! mahaukata kawai wadanda suka dauki mulki wata tsiya kije ki fad’a musu ni Ahamadu ina jiransu suzo da kansu sa’ko na baki duk ranar da suka sake turo ki to zan huce fushina a kanki Tausayi da jin kai ya sanya nake kyaleki kina min abunda kike so kuma ina baki damarki a siyance okey tunda ke d’in dabbace! mara kishin kanta zan fara cin ubanki idan kin soma ji a jikinki sai kije ki gyara BANGAR SIYASAR KI Tashi! maza ki kwashe min wannan kudin da kika watsar a kas! dubban mutane nacan suna nema ke kin samu kina zubarwa saboda kina da masu baki….Ki shirya min kudina tsaf! a cikin kyaure kamar yanda suke tunda bakwa so akwai dubunku masu so.”

Wasila ta yunkura ta tashi tsaye idanunta yayi jawur!!! Gefan hijab dinta tasa ta goge gomin goshinta ta ratse shi zata wuce!!! Tare ta yayi da kirjinsa ta dannata a jikin bango (garo) Sai ya zamana ma nuffashi da kyar take futarwa Gaggausan mutum irin wannan ya sanya mata nauyinsa ai sai Allah….”Ni zaki nunawa zafin kai ko.”!? Yafada yana sake matse ta a jikin bango…..Kanta tasa ta daki kirjinsa dashi Yace.”Idan kukan jini zakiyi anan gurin sai dai kiyi sai naga karshen tashen balagarki kiyi abinda nace kawai shine mafitarki.”

Cikin ‘kunar rai! tace”Ka matsa daga jikina ka matseni a bango domin ka cimma wata manufa taka akaina to Allah ya isa kudi kuma zan tsince dan karan kaina ba dan wani ba.”

Ya matsa daga jikinta yana ya mutse fuska…….Bani da wata manufa da zan cimma akanki saboda na had’u mata iri iri wad’anda suks fiki komai kazama dake mai zanji a jikinki da kike wannan maganar.” Shiru tayi masa ba tace komai ba ta hade masa kudinsa ya sanya hannu ya karba da hannu ya nuna mata ‘kofa “Fice min a gida wannan shine karo na biyu idan kika kuskura kika sake shigo min gida to kin san abunda zai biyo baya.”

Hijab! d’inta ta buge! tayi masa wani irin kallo mai nuna alamun akwai sauran kalubale tayi kwafa ta juya tana tafiya da sauri sauri!!! Hannuwa ya zuba cikin aljihu yana kallo ta tsaya ta daura niqab dinta kana ta murda kofa zata futa……Dake a kulle take daga waje, Hadi yazo da sauri ya bude mata ta fice da sauri tamkar zata tureshi…..Can ta hango Camas tsaye jikin wata bishiya ta nufe ta da saurin gaske sam! bata damu da kallon da mutanan dake gurin suke mata ba, saboda babbar dama ce ta samu domin cimma manufofinta a kansa…..Suna fita suka samu babur kai tsaye government house suka nufa.

‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi

 *NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300   Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176  sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_


 *Free Pege12*
Sai da sukayi nisa sosai Wasila ta cire niqab din fuskarta tana goge fuska  Camas tace"Ammafa matar nan taso ta saka ki a bala'i wallahi dan naga guy ranshi ya 'baci sosai ni na dauka ma zan ga kin fito da fasashen baki! wallahi."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Bai fasa min baki ba amma ya mareni ya sha'ke min ma'kogwaro har na soma jiyo 'kamshin mutuwa! ammafa bai daki banza sai na kulla masa sharri nifa naji dadi da hakan ta faru wani plan zan shirya a kanshi ke dai kawai mu bar maganar sai munje gida tukkuna." Camas tace"Shiyasa naga kin fito a furgice! gaskiya Wasila akwai ki da jarumta wallahi da nice da tuni na karaya da wannan harkar akwai hadari a cikinta......"Camas idan kinga na daina banga to na cimma manufofina ne kawai ke dai ki cigaba da take mun baya insha Allahu wannan plan din da zan shirya shine zai janyo min arziki na har abadah."
Camas tace"Allah yasa kawata kice dai mun kusa daina yawo a babur din haya zamu mallaki motar kanmu." Murmushi tayi har fararan hakoranta suka bayyana tace"Ke dai lokaci Camas! Allah dai ya taimake mu." Camas! ta amsa da "ameen" kana suka cigaba da wata hirar.

Koda suka isa government house din Governor da sauran mukarrabansa suna dakin meeting sai da sukayi xaman awa biyu tukkuna suka fito lokacin har magariba tayi duhu ya shigo a gurguje suka gaisa kana Wasila ta fada musu abunda ya faru a gidan Ahamadu tace....Wannan damar tamu itace zata rusa duk wani shirinsa a gaban bainar jama'a al'amarin ya faru saboda haka da kaina zan shiga gidan redio in watsa maganar  nasan wad'anda abun ya faru a gabansu zasu gazgata kaga da kanan shikkenan magana ta kare."

Governor Lawan Rabo yace."Mutukar wannan magana taki ta rusa shirin Ahamdu to ni Lawan Rabo nayi miki al'kawarin baki kud'in da zasu gigitaki! zan baki mamaki 'Yar gaske in har wannan plan din da kika shirya kan Ahamdu ya sanya ya janye kudirinsa na zama dan takarar governor a jam'iyyar *CPC."*
"Kar ka damu mai girma governor insha Allahu  magana ta 'kare kujerar mulki kam kaine zaka cigaba da zama a kanta."
Tafada cikin karfafawa kanta gwiwa kuma tana sanya ran insha Allah bukatarta zata biya.

Basu dawo gida ba sai kusan karfe goma na dare dan daukarsu sukayi a mota suka nufi wani kayataccen hotel sukayi ciye ciye kana sukayo guzirin wasu, har bakin layi Alhaji Tasiu ya kawo su  yana so ya fadawa Wasila munufarshi a kanta ya kasa wani irin kwarjini take masa shiyasa har ya yanzu ya kasa tunkararta yana kallon yanda abokansa ke shakawata da mata sam baya sha'awa amma yanzu ganin Wasila ya sanya yaji yana sha'awarta kuma ya daura aniya a kanta insha Allahu sai ya dandani zumarta yaji ya take....Dama tuntuni Alhaji ma'aruf ke kwadaita masa harkar yana basarwa sai yanzu kuma yaji yana sha'awar yi da Wasila *'Yar gaske!*

****

Bayan mako biyu da faruwan al'amarin Ahamd ya sake fita kamfen dashi da mutanansa alhamdullahi anyi an kare lafiya dan har gidajen redio sai da suka sanyo muryarsa yanda take jawabi da irin ayukan da zaiyi idan Allah ya bashi gwamnati a hannunsa.....Ahamdu yaga masoya ta ko wane bangare dan gurin cika yayi ma'kil! da jama'a 'yan nahiyar birget da kwana hudu, babban abunda zai baka mamaki! shine yanda mata da maza manya da yara suke fitowa suna turmutsutsu da fad'in "Se jam'iyar *CPC* sauyi muke so da *Ahamdu dan Musa* insha Allahu kano takace." 

Wasila na zaune kan tabarma anci kwalliya da wani uban les kunnanta da wuyanta gold ne sai sheki yake yi kawai taji muryarsa na jawabi yanda zai kula da gari da ayyukan da zaiyi mutukar Allah ya bashi iko, ta karo murya tana sauraran jawabin nasa da ba'aji sosai sakamakon hayaniyar da tayi yawa, mamaki take ya akayi har ya fita yayi wannan kamfen din basu sani ba.....Cizan lebe tayi ta dauki tafkekiyar wayarta mai tsadar gaske, Alhaji Tasiu ta kira ya daga wayar da sauri tace"Yallabai ka kunna redio kaji abunda ke faruwa mutuminka ya fita kamfen sai alkawarin karya yakeyi jama'ar gari na yi masa ihu.'' Alhaji Tasiu ya kunna redion wayarshi yana saurara......Kiranta ya sakeyi a waya bayan ya gama saurara yace."Yanzu meye matakin dauka." Kwafa tayi tace"Bari bayan sallahr isha'i kazo ka dauke mu muje gidan redion *Salama* zan musu magana idan Allah ya kaimu gobe su sanar da cewar za'a hira dani *Wasila 'Yar gaske* a filin mu Siyasa." Yace." Hakan yayi dai-dai 'Yar gaske insha Allahu zan shigo da wuri sai muje ammafa nima ina da wata bukata da nake nema a tare da ke." Yafada yana wani kashe murya.....Tuntuni ta riga ta gama gane inda ya dosa kawai tana basar dashi ta fahimci yanda yake kulafucinta bai san me cin wannan budurcin nata ba sai ya shirya ji takeyi dashi domin tasan shine darajarta ta gama yawace yawacen ta dawo tilas tasan zatayi aure kuma shine mutuncinta shiyasa take tattala abinta domin ta mika shi ga namijin da yayi nasarar auranta......Amsa masa tayi kawai da shikkenan sai kazo d'in." Alhaji Tasiu ya kashe waya yana me cike da nishadi zai biya bukatarshi gurin Wasila.....A waya ta kira Camas! tace bayan sallahar isha'i ta fito zasuje inguwa. Aikuwa Camas! na idar da sallah tayi kwalliya tayiwa mahaifiyata sallama ta nufi gidan su Wasila mahaifinta na zaune kan tabarma yana shan iska yana kallon fitarta baice komai ba wanda inda dane da tuni ya korata gida amma dake yanzu ta toshe masa baki da kudi shiru kakeji wai malam yaci shirwa.


 Cikin wata dan'kareriyar mota Alhaji Tasi'u yazo daukarsu Wasila matasan unguwa suka dinga zind'en Wasila da Camas! cewar ba harkar siyasa  kadai suka tsaya ba harda karuwanci ganin irin manya motocin dake zuwa daukarsu, ganin irin shigar da Wasila tayi ta fito dashi ya sanya suka sake gazgata zatonsu a kanta tana sanye da wani material roba roba anyi mata wani irin dinki riga da siket ne sun matseta ga wuyan rigar daga baya a fafake! daga gaba kuma anfutar da gidan nono ya matseta sosai Wasila akwai hips da brest duk sun fito sun das duk lafiyayyan namijn da ya kalleta a lokacin sai ya d'arsa wani abun a ranshi gashi ta kawo wani siririn mayafi ta rataya a kafadarta hannunta sakale da jakarta mahadin takalminta kana kallonta zaka gane ta soma wankuwa  idanunta sun bude tar! tar! sai taunar cingum takeyi.....Alhaji Tasiu yaji jijiyarsa ta mike ganin tsarin jikin Wasila ashe cika da 'kasaitar yarinyar ya kai haka babu shakka dole xaiyi mata kwance kwance ya dandana zumarta.

Gaban mota ta shiga ta zauna camas ta zauna a baya Kana Alhaji Tasi'u As  na gomna ya tuka motar suka fuce daga layin yara na jifan motar da fad'in"Ba mayi! Kano ta d'an Musa ce wallahi.....Alhaji Tasiu yace."Na lura jama'ar unguwar nan taku basayin wannan gwamnatin tamu shin bakya musu hasafi ne kin san fa dole ki sake musu kudi sosai saboda ranar za'be! su fito su mara miki baya.

Wasila ta sauke ajiyar zuciya tace"Na rasa abunda mutumin nan yake bawa mutanan jahar nan wallahi in kaga yanda jama'a ke sonsa sai ka rike baki ni kaina wani sa'in idan na fito jifana sukeyi sai nayi da gaske tukkuna." Alhaji Tasiu yace."Ai yana da masoya gaskiya dalili kenan da muke so mu dakusar da duk wani shirinsa muna so mu kashe masa gwiwa kan harkar yaji kwata kwata ta fita daga ranshi." Wasila tace."Kar ka damu insha Allahu bukatarmu zata biya a kanshi.

Alhaji Tasiu ya biya tashar redio *Salama* kudi masu kauri yace."Tun yanzu su soma watsa wa cewar zasuyi hira da *Wasila 'Yar gaske* Yar partyn Lawan Rabo governor mai ci a yanzu." aikuwa kafin ma su bar cikin gidan redion sun soma sanarwa kan zasu hira da Wasila 'Yar gaske a filinsu na Siyasarmu da misalin karfe takwas na dare." 


Tun a cikin mota Alhaji Tasiu ke yi mata wani irin kallo yana lumshe ido tana hankalce dashi kawai tana basarwa ne babu zato taji saukar hannunsa kan cinyarta....kici kici tayi da fuska tace"Meye haka kuma kar ka kara kuskuran ta'ba jikina duk mutumcin da muke da kai naga zaka keta min martaba ta mutuntaka to zamu raba hanya."

As ya soma yake yana sosa kai yace."Har yanzu baki gane inda na dosa ba kenan *Yar gaske* ki taimaka min rana daya ki mallaka min kanki." Ta watsa masa wani irin kallo, kankance ido tayi tace"As ina ganin girmanka da mutuncinka muyi harkar data hadamu da kai wato siyasa ni ba yar iska bace bana kuma shiri da mazinaci saboda haka kada ka kara yi min magana irin wannan duk ranar da ka sake to kam zan fadawa mai girma governor yayi min tsakani dakai ka kyaleni nayi sana'a ta kaje ka nemi 'yar iska kuyi iskancinku amma ni ba wannan na fito ba."

As yaji ciwon magangunta Wasila butuluce meye bai yi mata ba a rayuwa da girmansa da komai take fada masa irin wannan maganar.....Shiru yayi bai sake tankawa ba Ita taci kunu tana tauna cingum dinta jefi jefi tana amsa waya Camas na baya da tata wayar a hannu tana chating duk tana jin abunda sukeyi tana ganin idan da itace Wasila da gudu zata amince wallahi ai duk sana'a ce a wannan zamanin samun irinsu As  zaiyi wuya kuma ta fahimci mutumin bashi da mugunta iya kudi yana sakar musu ya kaisu su dungo siyayya harda ta banza ya biya kudin kuma ya basu wasu ita kam idan ya nemeta zata amince masa da gudu.


****
Washe gari gidan redion *Salama* suna bude tasharsu da abunda suka fara kenan "Jama'ar gari da misalin karfe takwas da rabi na dare zamuyi hira da Hajiya Wasila 'Yar gaske a filinmu na Siyasa   kowa ya kasance da redionsa a kusa dashi a dai-dai wannan lokaci domin yaji abunda yake tafe da wannan shahararriyar 'yar siyasar."

Gari ya dauka kowa na jiran lokaci......Labari ya iske Ahamdu ta bakin abokinshi Khalifa wanda yake mara masa baya ga dukanin harkokinsa tare sukeyi kuma shine a matsayin mataimakin shi idan Allah ya basu mulki a hannunsu.........Sam bai wani damu ba da jin wai zai ai hira da yarinyar a tashar redio ta *Salama* yasan dai zancan gizo baya wuce na 'koki shirme ne zasuyi tayi har su gaji su daina, Khalifa kuwa yasha jinin jikinsa jiran lokaci kawai yake yi.

***
Karfe takwas da rabi an soma gudanar da shirin *Siyasarmu*
Jama'ar gari na makale da redionsu da wayoyinsu.

Mai gabatarwa ya fara magana kamar haka....

"Jama'a yau filin namu na da babbar bakuwa Hajiya Wasila 'Yar gaske wanda tun kafin zuwan wannan lokacin muke ta sanar daku cewar zata shigo cikin shirin Siyasarmu domin ta warware mana zare da a bawa kan wata kullalan kulli dake faruwa a wannan jahar wanda jama'ar gari basu sanshi ba yau dai tace bari ta shigo wannan fili ta fasa 'kwan! kowa yaji ya san abunda ke faruwa 'yan takarkarin da suke gwabzawa guda biyu, masha Allah *'Yar gaske!* filin Siyasarmu ya shirya tsaf hakanan masu sauraro suma sun shirya suna sauraranki."



*'YAR BANGAR SIYASA!!*
   ???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE…….!
Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za’a tura kudin.0542382124…….Binta Umar gtbank….Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din….07084653262_08089965176 sai na fad’i yanda za’a biya kud’in…..Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars…….90899076_88137740 katin airtal ko orange

YABON GWANI YA ZAMA DOLE
????????????????????????????

PEGE DIN YAU KACOKAN! NAKI NE UWAR ARZIKI MACE MAI FARAR ANIYA DA FARAR ZUCIYA KINYI MIN KINA KAN YI MOMYNA FATIMA MUSA NIJAR ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE DAKE DA ZURIARKI BANTA’BA MU’AMULA DA MUTUM IRINKI BA BANI DA BAKIN GODIYA A GURINKI MOMY ADDUA CE A TSAKANINA DAKE UBANGIJI ALLAH YA DUBA ‘KARSHEN KI YASA KI GAMA LAFIYA ALLAH ABUNDA KIKEYI MIN ALLAH YAYI MIKI MOMY BAZAN TA’BA MANTAWA DAKE BA DOMIN KINYI MIN ABUNDA BAZAN MANTA DASHI BA NAGODE NAGODE NAGODE ALLAH YA AMFANI ZURIA????????

*Free Pege13*
Cikin zazza'kar muryata tayi sallama har da addua kamar wacce za tayi  abun arziki...."Bisimillahi rahamanir rahim rabi sharali sadari wayasirli amri wa'alal u'kudatun millisani yaf'kahu 'kauli ameen ya Allah, to jama'a assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu kamar yanda mai gabatarwa ya fada musu suna hakane nice Wasila 'Yar gaske 'yar partyn mai girma Governor Lawan Rabo governor da ba za'a ta'bayin irinshi ba insha Allah to a yau dai na shigo wannan filin ne domin nayi tankade da rairaye kana kuma na fed'e muku biri har hutsiyarsa, to jama'a hausawa nacewa yabon gwani ya zama dole dan haka kafin in fara cewa komai zan yabi   maigirma Governor na saboda ya cancanta a yabe shi duba da irin dumbin ayyukan da yake a wannan  jahar tamu......*A dad'e anayi sai gaskiya Engineer Turmi kake sha sassaka! Gugan 'karfe sha kwarafniya!  kayi mun gani jama'ar gari sun gani sun shaida! mun shaida! A daka a bari dole uwar na'ki! ayi ayi a hakura kai d'in dai kaine duk inda akaje aka dawo sai kai!!! Engineer ma'kiyan ka! sai da su mutu domin ka riga kayi musu nisa sai dai kallo daga nesa! mu dai kaine gwaninmu kai muka za'ba jama'ar gari kai suka za'ba kawai dai 'yan adawa nayi musu romon baka da kuma al'kawaririkan 'karya! tare basu tsohiyar hanci domin a siyi kuri'arsu mu mun yarda da kanmu ba sai munyi kamfen ba insha Allahu babu canji da yardar Allah sai mun maimaita  4+4  Ba sauyi  insha Allahu."
Ta kare maganar tana sauke nuffashi, Mai gabatarwa yace."Hajiya Wasila wannan yabon da kikeyi fa ni sai nake gani kamar kune kukeyi irinshi dan tuntuni jama'ar wannan jahar tamu suka dawo da rakiyar wannan gwamnati a cewarsu har yanxu basu gani a 'kas ba ance za'ayi mugudanar ruwa kana za'a saki wutar lantarki za'a biyawa yara kudin makaranta za'a gina sabbin makaranta da asibitoci da dai duk ayyukan da mai girma governor ya fada zaiyi kafin hawansa kujerar mulki shuru kakeji malam yaci shirwa wasu ayyukan idan an fara gadan gadan sai ajiye a shiga wata sabagar gashi yanzu har kunci shekaru uku akan wannan kujera babu wani sauyi da suka gani shiyasa suke ganin gwara su nemawa kansu mafita tun kafin dare yayi musu."

Wata siririyar dariya ta saki tace"Haba d'an jarida kasa kunne kaji da kyau!! Wallahi wannan gwamnatin ayyukanta daban suke dana sauran gomnonin da suka gabata haba Alaji ka duba babbar gadar da mukayi wacce ta fara tun  daga farkon titi gwaron dutse bata tsaya ba sai da takai unguwar na'ibawa, wannan katuwar kwatar ta jakara mun rufe ta ruf! idan ana ruwa mutane hankalinsu akwance duk wannan fargabar da suke a da sun daina sai ka fada min wace gwamnati ce tayi wannan aiki."? 

''To ai ba anan take ba 'Yar gaske sufa jama'ar gari suna magane akan al'kawarrikan da kuka dauka baku cika ko daya ba ba wai gada da aikin katuwar kwata ne ya damesu ba burinsu kawai suga ruwa da wuta kana kuma 'yayansu su samu ingantaccan ilimi har yanzu fa akwai makarantun da suke zama kan buhu babu banci da sauran abubuwan amfani kuma kafin hawanku wannan kujera kunyi alkawarin kan zaku inganta ilimin yara kana kuma kuyi karin albashi ga ma'aikata."

"Humm! ai kaji gareje irin na mutane jama'a basa tsayawa suyi aiki da lura wannan gwamnati fa kafin hawanmu akwai abubuwan da muka tarar akai akwai tarin bashishshika da gwamna na baya ya bari bai biya ba tilas! mu muka biya wanda har yanzu ba'a karasa ba haba jama'ar gari ku kwantar da hankalinku kamar tsumma a randa insha Allahu dukanin abunda mai girma gwamna ya ambata zaiyi to zaiyi ku dai kawai ku mara masa baya a za'be na gaba ya maimaita insha Allahu zakuyi mamakin aikin da zaiyi muku kano zata koma tamkar kasar waje saboda yanda za'a gyarata da titina da makarantu da asibitoci da sauransu."

" 'Yar gaske na tabbata jama'ar gari na sauraranki da duk bayanai da kikeyi to amma inda gizo ke sakar anan shine! sufa a halin yanzu duk wata magana da zaku fito ku fad'a a yanzu ba zasu dauketa da muhimanci ba saboda zuciyarsu ta riga ta gama makancewa da kaunar wannan d'an tahalikin mutumin wato *Ahamadu Musu* wanda suke masa inkiya da *(Ba'iya ka!)* shine nima nake ganin gwara kawai ku hakura ku bar masa tunda a zahiri kamar yafi ku mutane a wannan tafiyar."

Dariya ta saki harda tafa hannu "Oh! mutane kenan!? Ni wallahi ma abun mamaki yake bani idan naji suna kiran wannan mutumi da sunan dan takarar gwamna banta'ba jin inda *Gwauro* yayi mulki ba babban mutumin dan kimanin shekaru ar'abain da biyar yana zaune banu aure ai dole a bunkice shi.....To jama'a yau dai bari na fad'a muku abunda baku sani ba akan wannnan mutumi da kuka nace ya zama shugabanku.....Ahamdu dai tunda yake bai ta'ba aure ba duk wani mai shakku yaje yayi bunkice akai, yana zaune a gidanshi yaci karansa babu babbaka ya kawo  duk macen da yake so yayi mu'amula da ita tamakar matarshi....Jama'a ni Wasilatu 'Yar gaske zancen dai da nake muku nima ya auna ni a gidanshi Allah ne ya tseratar dani nasan mutanan da suka je gidanshi kar'bar tallafin da yakeyi duk karshen wata sun gani lokacin da ya sanya aka daura min ankwa babu ji babu gani ya sanya aka shiga dani ciki gidanshi a kulle da kwado..... dan jaridar ya katseta da fadin" To Yar gaske ya akayi kikeje gidanshi bayan kowa yasan ke ba 'yar bangaranshi bace shin ko zaki fadawa masu sauraranki dalili."?

Shiri fa ya dauki zafi!!

Zama ta gyara tace"Eh tabbas jama'a zasu zargi haka to abunda ya kaine gidanshi shine sati biyu da suka wuce yazo har kofar gidanmu da niyyar yaudarar kanwata sai ni kuma Allah ya nuna min shi ya dauki makudan kudi ya bata nice nan na hanata ta'ba kudin washe gari na nufi gidanshi domin na bashi kayanshi sai na tarar yana rabawa jama'ar gari kudi......Kafin nayi aune! kawai na ganshi tare da wata mata a kaina tana nuna masa ni wai nice! 'kawata Camas! da muke tafiya tare ta shiga rudani  a gaban mutane ba tare da yayi wani bunkice ba ya kira police yasa aka buga min ankwa aka tasa 'keya ta cikin gidanshi a kulle to wannan damar ya samu yaso ya biya bukatarshi a kaina sai Allah ya kare ni."

Dan Jaridar maganar tasha masa kai sosai.....Ashe bashi kadai ba harda jama'ar gari dake sauran shirin kafin kice kwabo zantuka sun soma tashi a garin wanda tun kafin a rufe shirin gari ya hargitse da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa kan Ahamdu ashe dama bashi da aure Gaskiya magana ta fito kan zargin da mutane ke masa gurin bada kudin da yake a cikin gidansa yana lalata da 'yayan mutane, sai wad'anda akayi abun a gabansu suka fara gazgatawa har suna bada larabi zance fa yayi tsanani a gari anata kace!kace! masu tsinewa Ahamadu sunfi yawa kan wadanda suka karyata maganar.


Wani irin gumi yake tsiyayarwa a jikinsa ita kanta rigar dake jikinsa sai da ta jike saboda tsananin tashin hankali ashe dama alkairi yana zama sharri! bai ta'ba nadamar zamanshi a haka ba sai yanzu shin wai yama akayi yarinyar nan tasan bashi da aure.....Shine taje ta kwancewa zani a kasuwa tilas masu karamin tunani su gazgata maganarta, Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! bai ta'ba tunanin al'amarin siyasa ya kai hakaba amma kuma wannan siyasar da sukeyi kamar ta sa'bawa dokar 'kasa 'kazafi! babu shi a siyance.
*Humm! Ahamdu kenan har yanzu baka san meye Siyasa ba.!*

Garba da Hadi suka fusata sosai Suka mike cikin zafin nama zasu fita Khalifa ya dakatar dasu da fad'in"Ina zakuje a wannan halin."? Garba Yace."Yallabai yarinyar nan yau sai tayi nadamar uwarta bata haifeta ba mu za tayiwa 'kazafi! banta'ba ganin butulu irinta ba, wallahi da ba don Yallabai yace tun farko a kyaleta da yanzu na zubar mata da hakora da tuni tana kwance tana jinyar kanta dan sai nayi mugun sa'ba mata kammani."! Khalifa yace."Ku dawo ku zauna ku samu nutsuwa." Suka koma suka zauna suna huci! yanda suka fusata niyyarsu subi Wasila gidan redion tana fitowa suci ubanta sai kuma aka katse musu hanzari.....Khalifa yaje ya zauna kusa dashi ya sanya hannu ya dafa kafad'arshi a hankali yace."Siyasa ce f........! katse shi yayi ta hanyar d'aga masa hannu Khalifa ya tsira masa ido ganin yanda duk ya wani burkice har yanzu yana digar da gumi kamar dakin babu Ac   'yan ya tsunsa biyu ya d'ora saman fatar le'bunansa ya tsurawa guri daya ido yana girgid'a kansa.

MYSON, NAJIB SA'ID*
       Tare da  kai da 
      *LAWAN RANO*
Nagode kwarai da kulawar ku akan wannan book din Allah ya 'kara kauna ya baku mata na gari????????

~~~

Free Pege14
To ganin Malam mai allo ya nufi masallaci yasa suma suka daura alwala domin gabatar da tasu sallahar kafin ya shigo gidan su tattauna abunda yake faruwa, suna zaune kan tabarma ya shigo bakinsa da sallama kamilin mutum ne wanda karatun al’kur’ani ya ratsa shi fari tas dashi kana ganinshi kaga bafulatani usul……Bitan! ta gyara masa tabarma ya zauna yana fad’in”Ashe bakuwa mukayi a gidan Hajara kece kike tafe.”? Ta amsa da “Eh wallahi malam tun kusan azuhur nake gidanan Bitan tace min kana tsangaya tare da yan makaranta malam ya gida ya damuna dafatan duk mun same ku lafiya.”? Ya aje carbin hannunsa a gefe ya amsa da fadin” Lafiya lau Haraja ya yara ya mai gidan naki.”? Duk sunan lafiya kalau wallahi ai yace ma a gaishe ku da kyau.”! To masha Allah muna amsawa amma dai za kiyi mana kwana biyu kafin ki koma.” Murmushi tayi “A’a malam gobe nake sanya ran komawa dama muhimaniyar maganace ta taso wanda shi mai gidan nawa ne ma yace lallai nazo na shaida maka abunda ke da akwai.” To Allah yasa alkairi Hajara ina sauranki.” Malam mai allo ya gyara zamanshi yana fuskantar Hajara wacce ta soma warware masa abunda ke faruwa ga iyalin Dan uwanshi Yahuza mai rasuwa………Ta kara da cewa”Malam yana da kyau ku sanya ido sosai kan wannan yarinyar domin a gaskiyar magana abun da takeyi ya soma wuce gona da iri watarana zata dauko muku abin kunya ko kuma taje ta zagi wani babban mutumin da zai daureku gabadaya yau da al’amarin ma a kanta zai tsaya da sauki wani abun idan ta dauko to ku da bakuji ba baku gani ba sai ta shafeku wannan shine dalilin da ya sanya nace to bari nazo na fada muku halin da ake ciki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button