NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

A daran Wasila taje gidansu Camas! ta fada mata abinda ke faruwa, Camas ta dinga she’kawa Suhairat da wanta dariya tana fad’in”Wallahi Wasila ni na dade da sanin cewar kina tattare sa sirrika a tare dake ke d’in ‘yar baiwa ce shiyasa nake so ki zage ki mori ‘kuruciyarki kinga wallahi sana’ar karuwanci zata kar’beki tunda kina da duk wani abu da d’a namiji yake bukata a jikin ‘ya mace, namiji mutukar lafiyayye ne shi ya kalleki sai yaji sha’awarki.” Da jin irin maganganun da Camas! take masa ya sanya ta had’e rai! sosai tace”Kada ki sake min irin wannan maganar banzar idan ba haka ba kuwa wallahi zamuyi fada dake fadan da bamu ta’bayin irinshi ba , a duniya akwai abunda na tsana sama da karuwanci da har zaki dangatani dashi bana so kada ki sake, wannan budurcin nawa insha Allahu sai na kaishi dakin mijina.”

To ganin yanda ranta ya’baci ne yasa ta dinga bata hakuri Wasila tayi tafiyarta ranta idan yayi dubu ya baci hakika taji bala’in haushin camas da irin maganar da take mata,

Tundaga ranar Camas bata sake yi mata maganar ba amma dai ita in ta samu wanda zasu sha minti ya latseta ya bata kudi tana yarda tun Wasila bata gane har dai tazo ta gane, ta dinga hanata amma taki dainawa kawai sai ta zuba mata ido.

Tun bayan komawarsu makarantar al’amura sukayi sauki dalili sun hakura da siye da siyarwa da sukeyi a makarantar sai suka dukufa gurin wanki da guga na mutanan dake unguwar tasu, idan kuma ta samu aikin wanke wanke gidajan amare taje tayi su biyata……..Gaba mai tsanani ta shiga tsakanin Wasila da Suhairat tsakaninsu kallon banza ne da tsartar da yawu, amma basu ta’ba caccaar baki ba a tsakaninsu, har lokacin da Suhairat suka fita daga makarantar ta shiga scondry lokacin ita kuma Wasila da Camas Da salimat suka shiga aji shida, tsakanin Salimat da Wasila gaisuwa ce dan ita Salimat halin ta ba irin na ‘yar uwarta bane Suhairat ita bata shiga abinda bai shafeta ba shiyasa ma dik gabar dake tsakanin wasila da Suhairat din bata shiga ba duk inda taga Wasila tana mata magana……Shigar su Wasila aji shida sai idanunsu ya sake budewa, sosai sunanta ya ‘bace! daga Wasila mutane suka koma kiranta da ‘Yar gaske…….Saboda yanayin da’kikancin su yasa suka fad’i a jarrabawa, su biyu ne kawai basu ci ba, Wasila ta nufi ofis tana kuka wai wallahi tayi kokari amma za’ace ba zataje scondry ba, Malam Isa shine suke dan shiri da ita, shine ya shiga ya fita ya sama musu makaranta ‘yan mata ta Sani mainage Wasila da Camas! aka shiga socondry sai rawar kai ya ‘karu, da ‘yan matanci, lokacin kuma dama ana tashan balaga suka dinga tsula tsiya da rashin mutunci a makarantar, Lokacin jarrabawa nayi suka fad’i ! sunaji sunaji suna gani ‘Yan ajinsu suka shiga Ss1 su suna js3 haka aka kawo ‘yan ‘kananun yara aka gwamutsasu! ba’kin cikin wannan yasa suka sallama makarantar suka hakura akan su tsaya wata shekarar ta zagayo, su ka daina zuwa makarantar gabadaya, Rashida na ganin sun daina zuwa itama sai ta nemi guri ta zauna alhalin ita tayi gaba sune a baya taga gwara ta hakura da karatun tunda babu su a makarantar……
Wannan shine abinda ya faru a tarihin Wasila da ya shud’e!

Mun dawo labari

Hajjah Babba tace”Da alama kun shaida junanku akwai alamun sannaya a tare daku.” Salimat tace”Sosai kuwa Hajjah Tare mukayi pramiry da ita Sunanta Wasila Yahuza.” Suhairat kusa wani irin mamaki takeyi da al’amarin ya akayi wannan ‘kazamar yarinyar jahila ‘yar tallah kuma ‘yar bangar siyasa ra jagaliya ta samu nasarar auran Masoyinta??? Bata da me bata amsa dole sai ita wasilar sai kawai ta shiga watsa mata mugun kallo tana ji kamar taje ta sha’ke mata wuya dan takaici.

A nutse ta gaisa Hajja ta amsa tana tambayar ta jiki tace”Naji sauki tana wasa da hannunta, Ta gaishe da Aunty Kubra itama ta amsa babu yabo babu fallasa, itama ta shaida fuskar yarinyar, a cikin ‘yan watannin da suka gabata ta ta’ba ganinta a tv tare da governor da mukarrabansa a lokacin da sukeje duba aikin titin Wuju wuju! shine tashar stv suka nuna su, tayi ta mamakin yanda akayi wannan al’amari ya faru to amma dai zata bugi cikin ‘yar uwarta Hajjah taji ko tana da masaniyar akan yarinyar dan gaskiya duniya da mutanan dake cikinta basuyi mata shaidar arziki ba mybe ma domin su cimma wata manufa tasu a siyasance ya sanya suka shiryo wannan auran kuma suka yadauri Ahamdu din ya aureta dan su kasheshi ko su shirya masa wata ma’karkashiyar……….. hira sukeyi wanda ita jinsu kawai takeyi so take ma taje ta kwanta dan har yanzu jikinta bai gama kwari ba, sai kawai taji muryar Suhairat na fad’in”Yaya Ahamduo ya akayi ka auri abokiyar adawarka ina ce itace Yarinyar data shiga gidan redio taci maka mutunci ta ta’ba martabar iyayenka kana kuma tayi maka ‘kazafi na zinaaaa.”! Dukaninsu suka mai da hankali kanta a lokacin da take wannan maganar……….

Littafin nan na kudi ne…!
Kika futar min da book keda Allah! kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[12/08, 7:55 pm] Farida Books: ‘Yr Bngr Sys
43
Hajjah tace”Wace irin magana ce wannan kikeyi Suhairat? maganar ko dad’in ji babu a bakin ki.” Da sauri ta bude baki za tayi magana ya d’aga mata hannunsa, fuskarsa da akwai alamun ‘bacin rai! yace.”Hajjah kar kiyi mamaki! da jin maganar Suhairat gaskiya ne Wasila tayi harkar siyasa a cikin harkar ma na ganta na aureta dan karan kaina ba wai da wata manufa ba.” Ya mai da hankalinsa kan Suhairat da jikinta yayi sanyi sam bata zaci wannan amsa daga bakinsa ba ita ta dauka zaiyi mamaki! idan yaji maganar, Yace.”Ke kuma suhairat daga yau kada na sake jin magana makamanciyar wannan ta fito daga bakin ki, nasan komai dangane da Wasila so bana bukatar bayani, ni da kaina naji na gani naje har can mahaifarta kawunta ya bani auranta kuma ya bani cikakken tarihinta naga asalinta da duk danginta, daga yau kada ki kara kiranta da ‘yar jagaliya.”
Aunty Kubra tayi saurin fad’in”Ahamdo kayi hakuri dan Allah wallahi na rasa meke damun Suhairat wautarta tayi yawa bayan haka kuma ai kowa da kuruciyarsa mu kam mun yaba da yarinya sosai tana da hankali Ubangiji Allah ya sanya alkairi ya kawo ‘kazantar daki.” murmushi yayi ya amsa da “Ameen Aunty Kubra nagode.” Suhairat kam tunda ta sunkuyar da kanta kasa ta kasa dagowa kunya duk ta isheta sosai taji haushin yanda ya gwaleta a gaban Wasilan ba, tayi da ta sanin fadar maganar inda tasan hakane zai faru, Ya’ke kawai ta cigaba dayi tana dan saka bakinta cikin hiraransu, dan dai ma macace mai wayewar kai da saurin sabo amma babu shakka taji haushin maganar Suhairat sai da kuma gogan nata ya wanke mata rai taji dadin yanda ya gwasale Suhairat din ya nuna musu ita din ba daga sama ta fad’o ba tana da daraja da martaba kuma ya nuna musu cewar yana kishinta tunda dai bai bada goyon baya kan su ci mutuncin taba……A hankali ta mike tace”Hajja ni zan shiga na kwanta jikina babu kwari sosai, ku gaida gida mun gode sosai.” Hajja tace”To babu laifi Allah ya sawake yasa kaffarane gida kuma zaiji insha Allahu.” Kama hanya tayi ta wuce daki ba tare da tacewa Aunty kubra komai ba dan ta lura da satar kallonta da takeyi a kai a kai sosai ta shiga mamakin kan abinda yasa matar take kallonta, gaskiya ta dora zarginta kan matar sam sai taji bata kwanta mata a rai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button