NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Bitan ta le’ka dakin nasu sai ta tarda rashida ita kadai a zaune Wasila tayi bacci Tace”Au bacci tayi kenan.”? Rashida tace”Eh tun dazu nayi nayi taci abinci ta’ki ci.” Bitan tace”Kyaleta na fad’a miki tana tashi daga wannan bacci xata nemi abinci da kanta.” Rashida tayi dariya tana fad’in “Aikuwa yanzu ma kawai dan tana cikin ‘bacin rai ne amma anti Wasila da abinci ba dama.” Bitan tasa dariya tare da fitowa daga dakin.

Aikuwa hakane ya kasance da wata masifaffiyar yunwa ta tashi da kyar taje ta wanke bakinta ta nufi kicin Bitan tace”A’a kar ki fara da abinci d’azu malam yace.” Kafin kici komai kisha wann

an rubutun.” Dakin bitan din ta nufa ta kar’bi rubutun ta tsuguna da bisimillah a bakinta tasha ragowar ta shafe cikinta dashi kamar yanda ta saba…..Bitan ta mike da kanta taje ta dauko mata abincin ta gyara zama sosai zauna kana tayi bisimillah ta fara cin abincin…….. Sai bayan da ta kammala cin abincin ne tace “Bitan ina Rashida.”? Tace” Bata jima da tafiya gidan Innar ku ba, malam yace taje ta fad’a mata abinda ke faruwa.

Ta sunkuyar da kanta kasa a hankali tace”Yanzu Bitan sai na koma gidan mutumin nan.”? Bitan tace”To ya zakiyi Wasila shine alkairi don Allah kiyi hakuri ki daina wasiwasi insha Allahu babu wani abunda zai sake biyowa baya kuma insha Allahu zaki haihu lafiya.” Shiru tayi tana tunanin shin idan ta koma gidan ko wane irin zama zasuyi dashi, ita yanzu ta daina jin sonsa a ranta, kawai zata koma ne ta zauna tare dashi saboda an rinjayeta.

Bayan magariba da mai allo ya shigo ya sake tabbatar mata da maganar ya kuma umarcesu da su had’a kayansu su kuma shirya da wuri don kar yazo yana jiransu………mai allo kwana yayi yana karatun al’kurani mai girma sai da ya had’a izifi sittin kana ya tofa cikin tsabtattaccen ruwan sama, ya samu jarka mai kyau ya zuba ya rufe da murfinta ya aje a guri guda, kana ya mike a nutse ya fito ya d’aura alwala ya wuce massalaci.
Karfe tara shaura na safe sun shirya duk suna zaune a tsakar gidan har da Inna Hajara data dako sammako tazo gidan, ita da mai allo sun tasa Wasila a gaba sai fada suke mata mai tafe da nasiha irin fadan da iyaye kan yiwa ‘yayansu a lokacin da za’a kaisu dakin mazajensu, Gatan da bata samu ba a farko, sosai take share hawaye tana jin wani iri a jikinta tabbas duk wanda yayi rashi iyaye nagari yayi babbar asara, Ada babu mai nuna mata ga yanda za tayi itace ke zartar da hukunci kan mahaifiyarta da ‘yar uwarta dan sai abinda tace sannan Uwani da Rashida keyi, shiyasa takejin wani irin a jikinta, gaskiya babu abinda za tacewa mai allo da Hajara da ita kanta Bitan din dan sun nuna mata kauna da so da kulawa, duk mutumin zai fad’a gaskiya yayi maka fad’a kan wani kuskure naka to babu shakka masoyinka, dan haka sai ta dauki aniyar zama lafiya gidan Ahamdu kamar yanda suke bukata ta kuma yi musu alkawari kan insha Allah za tayi mishi biyayya iya iyawarta.”albarka suka shiga sanya mata suna cike da farin ciki mara misaltuwa

Wannan karon cikin babbar mota (Sieana) sukaje garin wacce ke dauke da kayan abinci dana masarufi, Ahmadu yayi niyar farantawa mai allo kamar yanda shima ya faranta mishi saboda ya fahimci tsayuwar shi kan Wasilan da abinda ke cikinta yasan bashi da abinda zai biyashi a bisa abinda yayi mishi, sai dai hausawa nacewa yaba kyauta tukwici…..Almajirin malam ne ya hangi zuwansu lokacin da yake kokarin shiga gidan malam din, dan haka koda ya shiga gidan sai yake shaidawa malam din zuwansu, Wasila taji gabanta ya fadi har sai da ta rasa miyau a bakinta, tayi shiru tana kokarin maida kwalla ita har ta gaji da zubda hawaye……….Mai allo ya shigo dasu, cikin gidan yana musu barka da zuwa, Garba da Hadi sune suka shiga shigo da kayan abincin cikin gidan malam ya cika da mamaki yana so yayi magana Khalifa yayi saurin tareshi da fadin malam kada kace komai don Allah ba wai munyi hakan bane domin mu biyaka mun san bamu da abinda zamu biya dashi wannan ihisani ne kawai mukayi maka saboda karamcinka.” Mai allo ya girgixa kanshi yana fadin anya abun baiyi yawa ba kuwa? Khalifa yace.”Beyi yawa ba malam ka sanya albarka kawai.” Yace.”To nagode kwarai Allah ya sanya alkairi ya kara arziki da wadata.” Khalifa ya amsa da ameen ya rabbi.”
Inna Hajara kuwa mamaki take sosai ita bata ta’ba ‘karewa mijin Wasilan kallo ba sai yau! sai take ganin kamar ma yafi karfin wasilan dama haka Allah ke tsara lamarinshi Addua ta shigayi kan Allah ya xaunar da ita lafiya a dakinta.

Malam ya sanya Tanimu ya dauki jakar kayansu ya kai motar, kana dukaninsu suka fito daga cikin gidan……Ita dashi aka bari a baya, sai ta dinga ra’bewa tana so yayi gaba shi kuma ya’ki tafiya da sauri yana tafiya sannu sannu yana kallonta ta gefan ido sai ‘boye fuskarta take ci

kin mayafi, tana kauda kanta, tuntu’be tayi da bakin ‘kofa yayi gaggawar rike mata hannunta yana d’an janyota jikinsa, da sauri ta bude fuskarta tana zumbura bakinta, jikinta ta janye daga nashi, ya danyi gyaran murya a hankali yace.”Meye amfanin rufe fuskar da ki keyi ke ba amarya ba.”? Shiru tayi mishi ta dan ‘kara sauri gabanta na fad’uwa bata so wani ya juyo ya gansu suna jerawa, ganin yanda take tafiya da sauri da sauri yasa shima ya ‘kara sauri har suka iske inda motar take……Khalifa da kanshi ya bude mata bayan mota ta shiga, Rashida na kokarin ta shiga ta zauna kusa da ita yace.”kanwata zo ki zauna nan.” Sai ta zauna inda ya nuna mata,Inna Hajara kuwa hawaye ta fara sharewa ta kasa daurewa, ganin hakan ya sanya su Wasila suka fara kuka mai allo yace.”Wannan shirme ne hajara Alhaji ku tafi kawai idan ba haka yanzu xata sanya yaran nan koke koke.”! aikuwa yana ganin Wasilan na kuka yayi saurin shiga motar ya zauna kusa da ita, yana d’aga musu hannu mai allo ya mi’ka mishi ma dai-dai ciyar jarkar rubutun dake hannunsa yace.”Kullum ta dinga tsiyaya tana sha safe da dare tana kuma shafe cikinta dashi.” Ahmadu ya kar’bi rubutun yana godiya da fad’in “Insha Allah malam Allah ya biya bukata.”

Mai allo ya d’aga masa hannu yana fad’in “Ku sauka lafiya Allah ya tsare Alhaji Allah ya saka da alkairi.” Shi da khalifa suka amsa da “Ameen malam Allah ya saka da alkairi.” sai da motar ta ‘bace daga gurin sannan suka koma gida duk jikinsu a sanyaye mussaman Bitan da Inna Hajara, to shima dai mai allon daurewa kawai yake yi saboda yayi mutukar sha’kuwa da yaran kuma yana jinsu cikin ranshi.

Hawaye take sharewa tana d’an kauda kanta tare da kare fuskarta da mayafinta, ‘kamshin turaranshi da hucin numfashinsa duk ya isheta ta rasa ya za tayi gabanta sai fad’uwa yake, sai kawai taji hannunshi a jikinta ya kamo hannunta dake cikin mayafinta ya ri’ke cikin nashi a hankali ya soma murxawa yana kallonta ta gefan idonshi…….Kokarin cire hannun nata ta shigayi ya rike tam! ya had’e ‘yan yatsunsa da nata guri guda ya rintse gam gam! kamar wanda yake bata amana ko kuma yake d’aukar mata al’kawari!!! Ajiyar zuciya ta shiga saukewa ta kauda kanta tana kallon hanya, a hankali taji hucin numfashinsa dai dai fuskarta, a razane ta juyo sai kawai fuskarsu ta had’u guri guda! bakinshi ya sauka kan nata bai jira komai ba, ya sanya harshensa ya lashi le’bunanta yana sakin ajiyar zuciya! ya d’auke fuskarshi ya gyara zamanshi kamar bashi ba,
Ta dinga jin wata irin fargaba da fad’uwar gaba sai kawai ta shiga rarraba idanunta cikin motar tana kici kicin kwace hannunta dake rintse da nasa………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button