NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Kawu Habibu kuwa fad’i yake ” Garin yaya haka ta faru!? me yarinyar nan tayi maka me zafi da har zaka saketa Alhaji Ahamdu kada kayi mana haka.”

Shi dai shiru yayi kawai kanshi a kas……Mai allo yace.”Alhaji Ahamdu ka sanar min abinda ke faruwa me wasila ta aikata maka ka saketa nasan dai tabbas ba zaka aikata wannan abu ba sai da kwakkwaran dalili ina so kar ka rufe min komai ka shaida min abinda ke faruwa.

Cikin nutsuwa ya shiga warware musu irin badakalar dake faruwa ya kuma kunna musu muryar Wasila da As din a lokacin da suke kulle kullensu, ya kuma tabbatar musu da cewar dalilin kenan da ya sanya yaji zama da ita ya fice masa daga rai! bayan haka kuma koda ya zauna da ita to zuciyarsa za tayi tai masa wasiwasi a kanta ba zai iya yarda da ita ba……..Mai allo yace.”Banga laifinka ba Ahamdu banga laifinka. Hakika yarinyar nan ta cuci kanta ta cuci rayuwarta, tunda irin rayuwar data za’bawar kanta kenan to babu mu babu ita, duk wani hakki nasu munyi kokari mun saukeshi amma kullum cikin bin zugar shaidan takeyi da bib zugar mahaifiyarta, Wasila ta cuci kanta ta samu dama ta watsar babu komai Ahamdu mungode sosai da jajurcewa kuma naji dadi matuka da kazo kasanar dani abinda ke faruwa dan da baka sanar dani ba ba zan sani ba, kullum zan ta tunanin yarinyar na dakinta tunda dai ni nasan ba zasu zo inda muke ba, amma babu komai, zamu kyalesu mu zuba musu ido dan ba zamu inda suke ba, duk sanda duniya ta koya mata hankali na tabbata zasu zo su nemi inda muke.” Muryarshi na rawa ya ‘karashe maganar wanda har Ya dan bashi tausayi sai dai baice komai ba kuma ya gagara hada ido dashi ballanta khalifa da tunda aka fara maganar kanshi a kasa baice komai ba……..A hankali ya dan gyara kadan ya zura hannu cikin aljihu kudi masu yawa ya ciro ya aje gaban mai allo din yace.”Allah shi gafarta malam mu zamu wuce saduwar alkairi insha Allah zumuncinmu ba zai yanke ba ka kwantar da hankalin ka banyi haka da nufin in ‘bata maka rai ba, nayi hakan ne dan ganin kamar shine maslaha.” Mai allo ya mike yana gyara babbar rigarshi yace.”Haba Alhaji ai wannan yarinya ba zata rabamu ba kuma ni ban ‘kullace ka ba kasan shi aure da mutuwa rai garesu dik sanda kwanasu ya kare shikkenan Ubangiji Allah yasa haka shine alkairi amma ba zan gaji da fad’in cewar yarinyar ta cuci kanta ba.”

Har bakin mota suka rako su, Kawu Habibu kuwa ai tsabar bacin rai ya hanashi magana sosai yake ganin hauka da wautar yarinyar ta auri babban mutum attajiri irin wannan ta cutar da kanta, shi kam ai da yana da ‘ya mace da yay masa huce haushi da ita…….Suna tsaye a gurin har sai da motar ta ‘bacewa ganinsu.

Suka juya suka koma cikin gidan jikinsu duk a sanyaye………..Khalifa na drving yana girgiza kanshi gaskiya da ya sani kawai yake gurin rako Ahamdu mutane masu mutunci da karamci kawai ya watsa musu ‘ kasa a ido! meye rayuwa! yarinyar nan tayi laifi ta gane kuranta tayi nadama ta bada hakuri me ya kamata ayi sai a yafe mata Allah ma hakuri yake da bayinshi, kwata kwata baya son wannan d’abi’a ta abokinshi, ri’ko da ramuwa ba d’abi’a ce me kyau ba, ko babu komai yarinyar nan taci darajar masu daraja irinsu mai allo amma ya watsa wa idonshi kasa ya kalli tsabar idonshi yake shaida masa ya sakeki ‘Yarshi.

“Kasan Allah wannan abu da ka aikata ina me tabbatar maka da cewar sai kazo kayi nadama a gaba! Allah da kanshi shine ya halatta saki ya kuma umarce mu muyi amma ka sani duk ranar da akayi shi sai al’arshi ya girgixa! Ubangiji baya son kalmar gashi dai shi ya hallice ta, kuma kasan dole akwai jarabta wanda ubangiji keyi wa ma’aurata da irin haka ta ritsa dasu, ita yarinyar tata me kyauce tunda dai ta baka hakuri, ta kuma nemi yafiyarka, ka daina ganin kamar kasha wallahi Allah sai ya jarrabeka da masifar kaunar yarinyar a kuma lokacin da tayi maka nisa.”! Khalifa ya karashe maganarshi cikin bakin ciki da damuwar abinda abokin nasa yake yi…….Yace.” Sai dai kai Allah ya jarrabeka amma bani ba ni babu wani nadama da zanyi dan na rabu da wannan yarinyar Allah da zuciya yake aiki ba da wani abu so ka daina wannan maganar kawai.”

Khalifa bai sake cewa dashi komai ba kan maganar suka shiga wata hirar khalifa ya kudiri aniyar daga yau ya daina sanya bakinsa kan maganar tunda dai haka yake ganin shine dai-dai da rayuwarshi shikkenan


Kwanaki hud’u da faruwar al’marin, Wasila nata ciwo a tsaitsaye amma bata bari Uwani ta fahimci komai saboda duk sanda amai zai taso mata a sace take zuwa toliet ta kalato shi wani ya fito wani yaki fitowa ita da kanta ta zargi ciki a tare da ita sai dai tana so ta saci jiki Rashida ta rakata suke asibiti domin a tabbatar mata……Watarana haka takw wuni ba taci abinci ba saboda yanxu ba komai ke mata dadi a baki ba, wani sa’in ma abu in ta kalla bai mata za tai ta kalato amai tana ya mutsa fuska, duk daran duniya kuwa da zazzabi take kwana, Rashida taso ta fuskanci wani abu to amma ganin kamar wasilan na nuna mata lafiyarta lau yasa ta yi shiru da bakinta.


Camas duniya sabuwa, ganin Wasila ta daina kiran wayarta ya sanya ta saki jikinta ta soma fito da kudi suka hada kai da wani babban dillali dake harkar filaye da gidaje cikin unguwani masu kyau da tsada, ya kaita wasu manya manyan filaye a unguwar rijiyar Zaki cikin masu kudi, ya nuna mata su, yace.”Kinga idan kika siyi wannan filayen to ina me tabbatar miki da cewar shekara me zuwa kudinsu ya ninku kin mayar da kudinki kinci riba, mai kauri, yanzu idan kina bukatar siyan filayen zaki biya miliyan hudu duk biyun kowane guda daya miliyan biyu ne, kafin shekara guda nasan zaki siyar dasu gabadaya miliyan takwas kinga kin zama hajiya babbah.” yana dariya yake maganar yana kuma kara tabbatar mata da maganarshi, jin uban kudin da zata ci riba akai yasa ko neman ragi bai ta ta amince tace”Suje ya dauko mata takardun filayen sai su wuce banki ta bashi kudin…..Jiki na rawa Usaini dillali yay gaba tabi bayansa


As dai sarkin kulafuci da binbini bai hakura ba kusan kullum sai yazo gidan Wasila yayi ta magiya ta fito idan ta ga dama ta fita watarana kuwa haka zai karaci zamansa a mota ya tafi…….Yanzu ya daina so yayi lalata da ita so kawai yake ta amince masa ya aureta sabida jahlici kuma yake neman aure ba tare da ya bari tayi iddah ba, As din da ita Wasilan dik basu san abunda suke ba gwarama Wasilan zamu iya cewa bata sani ba tunda ba ilimin addini tayi cikakke ba shi kuwa As ya sani yake takewa yake zuwa zance………..Da dai yaga ta’ki bashi had’in kai sai kawai yace.”Ya basu notice na wata biyu duk wani abu da suka san nasu ne to su kwashe su bar gidan idan ba haka ba to zaiyi musu tozarci da wulakanci tunda dai basu gaji mutunci ba, Uwani ta dinga bashi hakuri tana kwantar da kai, shi kuma ya dinga fad’a mata ba’kaken maganganu a fakaice! takaici ya sanya Wasila barin gurin, ta rasa yaushe Uwani za tayi hankali ta daina zubda mutuncinta saboda taulaci, sai wani rarrashin As din take kamar za tayi masa sujjada.


Yau satin ta biyar da fitowa daga gidan Ahamdu rayuwa tayi musu tsanani sosai dan tuntuni kayan abincinsu sun kare sai dai kullum rashida ta fita bakin titi tayi musu cefane, watarana ma basa karyawa da safe da rana suke cin abinci suci da dare……..Wasila ta rame tayi uban haske sosai dan duk wanda ya kalleta yaga mace mai yaron ciki nonowanta sunyi girma ainun! hannayenta da kafafunta sun dashe goshinta kullum cikin zuba kyalli yake yi……..Uwani tayi masifar tashin hankalinta ta dinga zazzaginta tana fad’in “Wato ni zaki munafurta ko? to tun kafin na haifeki na san meye duniya ni zakiyi wa duniyanci ko!? to wallahi ko ‘kinki ko kinso sai an zubar da wannan cikin dan ba zaki haifeshi ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button