NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Abin kamar al’mara kiran wayar yake ana ce masa a kashe take, ya kira ya kai sau ashirin maganar dai daya ce wayar a kashe take! Ya d’ago kanshi yana wata irin zufa bakinsa na rawa yace.”Khalifa wai meke faruwa ne? Wayar nan fa ta’ki shiga kana ji da kunnanka a kashe take Why! Wad’annan yaran naso su sanya zuciyata ta buga!!!!!!! Khalifa tsorona Allah tsorona Annabi kar cikin nan ya zube, ko a samu wata matsalar nasa raina akanshi.”Ya ‘kareshe maganar cikin rauni da sarewa da al’amarin.

Sosai ya bawa Khalifa tausayi yace.”Ni ina tunanin network ne matsalar Amma kar ka damu abokina insha Allah cikin nan ba zai samu matsala ba muje tashar kabuga insha Allah xamu samesu idan ma motarsu ta tashi ai mun san inda suka nufa kai tsaye sai mu wuce can garkon ni da kaina zanyi wa mai allo bayanin komai.”

Hularshi ya cire ya ciro hankici ya goge fuskarshi da saman kanshi, Yana jin wata irin fargaba na kamashi yanzu da wane ido zai kalli mai allo to me ma zaice masa idan sunje? Yace”Khalifa bani da wani bayani da zan iya yiwa mutumin nan saboda ina jin kunya wallahi in ce masa saboda d’ana ko ‘yata dake cin Wasilan zan dauketa kasan da akwai nauyi.” Khalifa yace.”Kar ka damu zanyi mishi bayani.”
Ya shiga girgiza kanshi yana fad’in “Kamar nasan abinda zai faru shiyasa jiya nace maka muje inda suke da yanzu duk hakan bata faru.” Khalifa yace.”Ni nayi mamaki wallahi saboda jiya lafiyar Allah muka rabu dasu ko da wasa basu shaida min cewar zasu tafi wani gurin ba amma basu kyauta ba wallahi kuma Wasila tayi wautar gaske.”

Girgixa kanshi kawai yake yana adduar Allah yasa su samesu a tasha don shi kam yana bala’in jin kunyar had’a ido da mai allo.

Khalifa ne kawai ya iya fitowa daga motar bayan shigarsu tashar ya kutsa cikin mutane direbobin motoci yana dube duben motocin mutane, ko kusa ko alama bai hango koda kyallin mayafin wata daga cikinsu ba, haka ya gaji ya nufi inda motar su ke fake…..Shi kuwa uban gayyar tamkar wani zautacce ko kuma mara kunne yana ri’ke da waya a hannunshi sai kiran numbar Rashida yake tamkar mai kunnan ‘kashi ko kuma kurma yana jin abinda matar nan ke fad’a masa cewar wayar a kashe take amma ya kasa daina kiran wayar…….Ganin Khalifa ya doso motar tasu cikin sanyi jiki ya sanya shi rarraba ido yana jiran karasowarsa…
Khalifa yace.”Babu fa alamun yaran nan cikin tashar nan kawai shiga mota muje.” Jiki a mace ya bud’e mota ya shiga duk yayi wani laushi kamar mara lafiya….Khalifa yaja motar suka fita daga tashar duk rayukansu babu dad’i…….Sai da suka hau kwalta sosai kana ya sauke numfashi yana huci! yace.”Khalifa Allah banta’ba ganin sukuwar uwa irin uwar wad’annan yaran ba, ni yanzu ma ita nake jin haushi wallahi.” Khalifa yace.”Gaskiya tayi wauta itama data d’auki yarinyar nan da wannan lalurar suka dauki hanya bayan sai da na fad’a mata dokar da likita ta kafa kan ‘yar tata shiyasa wallahi mace komai shekarunta watarana ta tafka maka wani abun haushin sai kaji kamar ka d’ora hannunka akanka.

Yace.”Nifa babu ruwana Allah cikina ya samu wata matsala sai na dauki mataki kanta da ita da uwar tata.” Khalifa yace.”Ai kaji irinta wai kai me yasa kake hakane? Matar nan fa ta tabbatar min da cewar sunzo har gidanka da maganar cikin basu samu damar ganinka ba suka hakura suka koma kan me yasa za kaga laifinta anan bayan tayi kokarin ganin an fita hakkina.”
Tsaki! yay yaja bakinsa yayi shiru yana muzurai! da ya tuno wani abu sai gabanshi ya fad’i! gaskiya yana bala’in son cikin nan nashi a yanzu ji yake zai iya hakura da komai na rayuwa mutukar cikinsa zai tsira.

Tafiya suke mota na gwajab gwajab yayinda ciwon ciki da mara ya tsananta a gareta ta! ta dinga sunkuyar da kanta tana zufa da kiran sunan Allah gumi ko ta ina d’iga yake a jikinta, tsabar yanda take jin jiki sunan Allah kawai take kira tana jin wani irin imani na ziryartar ta anya kuwa wannan cikin bashi ne ajalinta ba? abinda take fad’a kenan cikin zuciyarta.

Sun isa garin Garko Lafiya sai da kuma lokacin mai allo ya jima da fita tsangaya, Tanimu ne yay musu jagora har makarantar tashi…..Mai allo na tsakiyar al’majiransa ya hango zuwansu sai ya mike a nutse yana fara’a yana musu barka da zuwa……Cikin wata rumfar kwano da babu kowa a jiki suka nufa. Ma allo da kanshi ya karkade musu tabarma suka zauna sai aka shiga gaishe gaishe, Ahamdu sai sunkuyar da kanshi yake duk kunya ta dabaibayeshi sai yanzu yake jin kunyar dattajon yaga shi kuwa sai fara’a yake yana tambayarsa gida da harkokin yau da kullum. Khalifa yace.”Alhamudllhi malam komai na tafiya yanda akeso sai da aita tayamu da addua.” Mai allo yace.”Addua munanan munayi har sai da numfashin mu ya dauke.”

Khalifa ya ja gwaron numfashi kafin ya gyara zamanshi a nutse yace.”Allah shi gafarta malam dama mun biyo sahun yaran nan ne wato ina nufin Wasila da ‘kanwarta da kuma mahaifiyarsu, domin muji shin sun iso lafiya! sannan kuma muna da tabbacin cewa nan suka nufo dalili basu da wani gurin in ba nan d’in ba, Allah shi gafarta malam babu maganar rufe rufe cikin maganar nan Yarinyar nan Wasila na dauke da ciki har na tsayin watanni uku da satika kuma akwai matsala mai girma tattare da ita da d’an dake jikinta wannan shine babban dalilin ma da ya sanya shi Abokin nawa yace.”Lallai ilallah sai munzo domin mu tabbar da zuwan nasu cikin ‘koshin lafiya.”

Mai allo ya dinga kallon Khalifa cikin mamaki da kad’uwa ya d’an gyara zamanshi kafin yace.”To Idan na fahimci inda maganarka ta dosa anan shine kana so ka sanar dani cewar kun biyo sahun su Wasila domin kuna tunani ko nan suka zo kamar yanda ka fad’a hakane ko? Khalifa yace.”Hake Malam.” Mai allo yace.”To a gaskiya ni dai har na fito daga gida banga zuwansu amma ban sani ba ko bayan na fito suka iso bari nasa yaro yaje ya duba a gida.” Ya mike ya fita daga inda suke.

Ahamdu ya kalli Khalifa cikin sarewa da tsananin damuwa yace.”Anya Khalifa anya yaran nan suna nan kuwa? jikina na bani ba nan suka zo ba.” Khalifa yace.”Ka dai bari tukkuna mybe bayan ya fito daga gidan suka sauka garin kamar yanda ya fad’a d’in in banda abinka idan ba nan suka zo ina zasuje da yafi nan d’in.” Yay shiru yana jin wata irin zufa na karyo masa, mikewa yay ya fito daga rumfar kwanon ya kama kallon hanya sai kace wani zautacce ga rana sai kwalle masa ido take.


Misalin ‘Karfe biyu da rabi na rana suka sauka garin Fataskum, bayan sun sauka daga mota Uwani ta dinga rarraba ido tana dube dube hanya dan garin gabad’aya ya sauya mata yau kusan shekaru goma sha biyu da rabonta da garin, tin tana goyon Rashida lokacin Yahuza na dan da mutuwa tunda tayi wannan zuwan bata sake waiwayar garin ba, dama mutum hud’u ne suka rage musu a dangi Babban yayansu mahaifiyarta da suke kira da Kawu Madu sai Mai binshi Kawu Isa sai kuma Iya mai waina da Tabawa dama su biyar iyayensu suka haifa mahaifiyarta itace ta uku ita ke bin Kawu Isa sai Iya mai waina sai kuma Tabawa! Mahaifiyarta itace kawai tayi aure a wani gari, amma dukaninsu cikin garin Fatskum suke tare da iyalinsu mutukar sun fita daka garin to sunje wani garin ziyara…..Tun bayan rasuwar mahaifiyar Uwani Kawu yaso daukarta domin su dinga kallonta a matsayin ‘yar uwarsu, mahaifinta ya’ki lamince masa haka suka hakura suka bar mishi ‘yarshi, gashi bashi da cikakkiyar lafiya shima a lokacin ya hana a tafi da itane domin ya dinga kallonta tana d’ebe masa kewar mahaifiyarta…….Sai da cutar ajali ta kamashi ne ‘kaninshi ya daukeshi ya kaishi gidanshi dake akwai shago a wajen gidan nan ya ajeshi yake kula dashi, to shine fa tun daga lokacin Uwani ta soma shan wahalar rayuwa gidan Kawun nata har mahaifinta ya kwanta dama, a lokacin ta ‘kara shiga tsaka mai wuya ga wuya ga maraici ga tsananin azabah! Saboda zalinci irin na Kawun ya siyar mata da gidan da ya zama gadonta ya sanya kudin a aljihunsa ya cinye matansa na zugashi da fad’in Ai idan yaci Allah ba zai tuhume shi ba tunda dai shima yana ciyar da ita………..Sai da sukayi aure da Ayuba ya jagorance da kanshi sukaje can Fatsukum din dangin mahaifiyarta da kwatance, to tun daga sannan ta gane hanya……..Saboda matsatsi da talauci da kuma rashin kudin mota ya sanya bata zuwa garin a kai a kai, sai ta dauki shekaru masu yawa kafin taje to wannan karon dai shekarun data dauka ba taje ba sun fi na baya…….Da tambaya suka iske gidan Kawu Madu dake shi d’in ba ‘boyayyen mutum bane a garin yasa basu sha wahala ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button