NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Kuluwa na ganin irin tsarabar da suka kawo sai ta hau washe bakinta ta dauki turmin atamfofi irin na leda guda biyu tace wannan ni zan d’inka in sa a jikina wannan yadin kuma na malam ne, sauran kuma Iya mai waina da Tabawa su kasafta a tsakaninsu.” Su dai kallonta kawai sukeyi duk tabi ta kwashe kayan ta shige dakinta dasu sai murna takeyi ko Kawun ma bata nunawa ba.

Sai dare suka samu suka sanya abinci a cikinsu shima abincin Inna Tabawa ce ta kawo musu cikin katuwar Samira shinkfa da wake ne da manya da wani uban yaji da yaji gishiri da citta! haka suka cuccusa dan gwarashi kan narkeken towon dawan da Kuluwa ta kawo musu, Wasila dai kad’an taci tasha maganinta ta nemi gefenan tabarma ta kwanta tana mai da nuffashin wahala………….Duhu sosai gidan babu wadatacciyar fitala sauro da kwari ka sukayi sallama! Wasila ta gigice ta dinga soshe soshe kukan sauro duk ya cika mata kunne! Uwani tace “Ku tashi mu koma daki mu kwanta kunga mutanan gidan sun shige sai mu kadai a tsakar gida ga sauro.” Rashida tace “Yanzu cikin wannan kazantar zamu mu kwanta ga yara nasan suna fitsarin kwance.” Uwani tace”To ya zakuyi ai da zama cikin sauron nan gwara cikin rumfar.” Wasila tace”Uwani ku shiga ku ku barni anan Rashida ki dauko min zanin atamfa cikin kayanmu in rufe jikina.” Uwani tace”Akwai fa damuwa kwanciyar ki anan.” Tagoge kwallah tace”Uwani nan yafi min kan in shiga dakin nan inzo ina kakarin amai da daddare d’an abincin da naci ya dawo, kuma wannan matar tazo tana miki masifa.”

A sanyaye Uwani tace”Shikkenan ai.” Ta mike a hankali ta shiga dakin rashida tabi bayanta……Nan su kaga yara birjik a rumfar ko wanne ya wargaje kafafunshi wasu sun soma sakin fitsari abinsu sai barci suke…..Uwani ta ra’ba can wata kusurwa ta karkad’e wani buhu ta shimfida ita kuma rashida ta nufi dakin Kuluwa dan jakkunan kayan nasu na cikin dakin……..Nan ta tarar da Kuluwa ta bude musu kaya sai bunkice takeyi musu, tana ganin rashida sai ta diriri ce ta hau ya’ke….”Am…dama ai nace bari na gyara muku kayan naku in adana muku su guru guda.” abinda tace kenan tana sosa kanta….Rashida bata ce komai ta dauki zannuwa uku na atamfa ta fito daga dakin….Ita kuluwa tana ganin rashida ta fita daga dakin sai ta cigaba da bincika kayan ta dauko manya manyan shaddodin Wasila masu uban stone work ta d’aga ‘kasan katifarta ta sanya ta mai da katifar……Da sauri ta gyara jakkunan kayan ta fito daga dakin tana zare ido.

Wasila kudindine jikinta tayi. ita kadai kwal a katon tsakar gidan ko tsoro bataji gari yayi shiru sai kukan tsintsaye kawai ke tashi………. Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauketa ta dalilin magungunan da takesha

Fitowar Kawu Madu daga dakinsa ne ya tayar da ita Sai taji ana kiran sallah da alama asuba tayi, Kawu Madu ya kalleta yana mamaki yace.” Ke anan kika kwanta.” Sunkuyar da kanta tayi kawai sai ya girgiza kanshi ya nufi bandaki da buta a hannunsa……..Yana fitowa ya daura alwala ya nufi masalaci,
Kasa shiga bandakin tayi sai kawai tayi gaggwar tsugunawa a bakin rariyar tayi fitsarinta ta kwara ruwa, kana ta matsa gefe guda ta daura alwala ta bar gurin.

Shimfidar data kwanta ta dauke ta cire dankwalin kanta ta gyara hijab dinta ta tada sallah……Uwani da rashida suka fito a tare suma alwalar suka daura nan tsakar gidan sukayi sallah domin dai cikin rumfar babu guri bayan haka kuma ko ina kasa ‘kafarka fitsari ne.

Suna zaune a tsakar gidan gari yayi haske Kuluwa ta fito tayi alwala ta goge bakinta da gawayi kana ta shiga kichin ta kunna wuta ta dora ruwan kunu sannan ta nufi daki domin yin sallah.

ၥYaran dake dakin suka soma fitowa su kusan bakwai wasu jikinsu da fitsari wasu babu ba tare da sunyi alwala ba suka soma wasa a tsakar gidan wasu kuma tuni sun fice waje da abubuwan wasan su……Su Wasila suka dinga mamakin wannan rayuwa….Nan rashida take shaida musu abinda taga kuluwa nayi musu da kayansu….Fitowarta yasa tayi saurin yin shiru to itama Kuluwar a kunyance take dan haka sai tayi saurin fadawa kichin tana sosa kai! Wasila abin dariya ya bata sai ta shiga girgiza kai tana fad’in ”Ni dariya ma take bani wallahi.” Rashida tayi dariya kasa kasa tana kallon kicin din.

Wani tsalan kunu ta kawo musu cikin kwanon sha da kufuna guda uku sai ‘kullin sikari akai….Uwani ta gaisheta tanayi mata sannu suma suka gaisheta Ita kuwa ta kasa tsayawa a gurin kunyar hada ido da rashida take……Tana shiga kicin Wasila ta saka fuskarta cikin hijab taci dariyarta ta koshi, kai mara gaskiya dai ko a ruwa gumi yake.

Fitowa tayi daga kicin din da katon farantin silba da narkeken d’umamen towo an yanyanka shi sai miya tsululu towon sai iyo yake cikin miyar….Ta kalli rashida tana fad’in ‘kawata ga d’umame nan idan kunsha kunun sai kuci kwaji dad’in tafiya da karfinku.” Rashida tace”Mungode Kuluwa.” Da sauri ta bar gurin tana kwalawa yaranta kira wai suzo su dauki kununsu da duk ta zuba musu a kufuna ‘kudaje sai bin bakin kufunan sukeyi…..aikuwa da d’ai- da d’ai yaran suka dinga shigowa suna daukar kufonan kunun suna sha ba tare da sun wanke bakinsu ba.

Kawu Madu ne ya shigo da sauri yana fad’in “Ina Wasila da Rashida.” Sukace gamu Kawu Yace.” To maza ku fito ga motar abokina ya kawo ice yanzu zai fita cikin gari sai yaje ku a tasha ku shiga mota.” Suka mike da sauri Rashida ta shiga dakin domin dauko musu jakar kayansu, dama tasu daya ce ta uwani daya.

Uwani ta mike tana yakar zuciyarta hawaye ne yake so ya ‘balle mata tana mayar dashi, suka je bakin kichin din da Kuluwa ke ciki tana zaune dirshan gabanta da karon bokintin da ta dama kunu tana katsewa gefanta kuma tukunyar miya ca bude ga ludayi a kasa….Uwani tace”Zasu tafi.” Sai ta hau washe baki tana fadin”Bari na taso inyi rakiya ni kuwa me zan baku. ‘Yayan nan.”? Fitowa tay ta shiga dakinta da sauri ta dauko wata yar takarda fara ta mikawa rashida tana fad’in ‘Kawata ga yariruka kwa sanya ku gaishe da kawunan naku.” Rashida ta karba tana godiya tabi bayan Wasila da Uwani da suka riga sukayi gaba.

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
59
Tun a mota yake jin alamun zazzabi zazzabi a jikinsa yasan kuma ba komai ne ya jawo mishi faruwar hakan ba sai alhini da damuwar da yake ciki idanunsa sun kad’a sunyi jawur! jijiyar kanshi ma ta tashi, yanda le’bunanshi suke a bushe haka ma’kogwaron shi yake dan rabonshi da ruwa ko abinci tun jiya da daddare da yasha coffee kafin ya kwanta, sam ya ma manta da wani abinci saboda tsananin damuwar da yake ciki….Yana kallon khalifa na tu’ki yana kur’bar lemo amma shi sha’awa ma baya bashi bakinsa duk ya bushe yana jin wani irin abu ya tokare masa a ma’kogwaronsa.
Ganin tashin hankali murarar a tartare da abokin nasa yasa ya d’an kalleshi bayan yayi parking din motar cikin gidanshi, Yace.”Kayi hakuri abinda zan iya cewa da kai kenan! ka cigaba da addua kawai kan Allah ya tsare maka cikinka da ita kanta yarinyar wannan damuwar duk ba ita mafita ba, tunda dai Allah ya raba ganawa sai ka bar mishi ikonshi, ni munyi magana da ita a jiya ta kuma shaida min cewar mutukar ta haihu to zata kawo ma’ka d’anka har inda kake.” Saurin kallonsa yayi yace.”Okey ashe da sa hannunka ta gudu kenan.” ? Khalifa yay saurin girgiza kanshi yana fad’in” No ka fahimce ni mana! Jiya nake fad’a mata cewa dole sai na sanar maka da maganar cikin ta nuna bata so nace mata ai tilas ka sai ka sani shine tace ko anfad’a maka ko ba a fad’a maka ba in ta haihu zata kawo maka d’anka kaji dalilin da ya sanya nayi maka wannan maganar amma wai maganar da sanya hannuna a cikin guduwarsu bata taso ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button