NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Uwani ta soma tunani cikin fargaba da faduwar gaba tace”Anya Camas! ba amanarki zata ci ba kuwa irin wannan kira da ake mata ai yaci ace ta dauki wayar idan ba da abinda ta shirya ba.

Rashida tace”Aikuwa wallahi ko tana yawo da ubanta sai ta fito da kudin nan tabd’ijam! miliyan shida za ta cinye lallai bata da hankali.

Wasila tace”Allah nima jikina ya soma sanyi da al’amarin anya kuwa! amma dai bari na sake kiranta mu gani.” Nan ta shiga kiran wayar Camas! gashi dai tana shiga amma babu amsa! dukaninsu hankalinsu yay masifar tashi mussaman Wasila da tasan wannan kudin su kadai ne suka rage mata kuma sune zasu taimaka mata ta ‘bangarori da dama tunda dai ta ‘kudiri aniyar barin harkar jagaliya……Sai kusan karfe daya na dare sannan sukaje suka kwanta dukaninsu babu wanda yay baccin arziki sai juyi sukeyi mussaman wasila da abubuwa suka taru sukai mata yawa, kuka take sosai shashshekar kunanta yasa Uwani mikewa zaune tana kallonta, Tsakanin d’a da mahaifi sai Allah sai taji tausayin ‘yar tata itama ta hau share hawaye tace”Wannan kukan bashi ne mafita ba a gurinki, wai shin meye abun damuwa da tashin hankali dan wannan mutumin ya sakeki ke ba abin alfahari bane a gurinki za kici karanki babu babbaka yanzu fa wata dama kika samu da zaki cigaba da neman kudinki gashi Allah ya sanya miki nasibi a cikin harkar kina nema ki ‘barar da damarki, ni dai idan zakiji maganata shine gobe idan Allah ya kaimu ki shirya ki tafi gidan gomnati domin cigaba da gudanar da harkokin siyasarki.”

Wasila taja majina tana goge fuska tace”Nifa Uwani na fada miki bazan sake yin wannan harkar ba na fada miki ni yanzu babban damuwa ta shine idan Camas! ta salwantar min da kudina ya zanyi da rayuwata da wane kudi zan kama sana’a me zan juya ni ba zanyi karuwanci ba kuma ba zan koma wannan harkar ba.”

Uwani tace”Idan ya kasance Camas! ta salwantar miki da kudi ba sai ki maka ta kotu ba, sannan kina maganar sana’a to tunda kince ba zaki koma harkar siyasa ba kuma kince ba zakiyi karuwanci ba to me zai hana ki shiga wasan hausa (film) nasan mutukar kin shiga wannan harkar zakiyi arziki na ban mamaki.”

Wasila ta dinga kallon mahaifiyar tata cike da tsananin mamaki! wai me yasa uwani take hakane? kullum bata da buri illa taga ta dorasu turba mara kyau! idan akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce wannan harkar ba film! duk lalacewa ta tattare a gurin koda kai mutumin kirki ne kana wannan harkar jama’a ba zasu kalleka da kima ba.

Ba ta sake cewa da ita koma ba ta koma ta kwanta tare da juya mata baya tana addua cikin ranta tana jinta tana sake kwarzanta mata nasarorin harkar film din da yanda ‘yan mata ke samun mahaukatan kudi mutukar sun shiga harkar….Uffan bata sake ce mata har dai taji shiru hakan ya tabbatar mata da cewar bacci ya dauke ta, sai ta mike a hankali taje ta dauro alwala ta fito a nutse ta tada sallah nafila tayi raka’a biyu ta dade sujjada karshe tana kuka da addua da fadin”Allah ya kawo mata agaji ya yafe mata kusa kuranta na baya…..Addua ta shafa ta kwanta kan daddumar bacci me nauyi ya dauketa.

Asubah suka tashi sukayi sallah Uwani ta koma tayi kwanciyarta, Wasila da Rashida suka zauna suna shawarwarin ya za suyi, Tunda yanzu ma sun sake kiran Camas! din bata dauka ba, Rashida tace”,Anti Wasila bari gari

yay haske sai muje gidansu shegiya macuciya dama ni tuntuni bana kaunar abotarku da ita na tsaneta wallahi.” Hannunta rike da wayar tana ta trying tace”Rashida bamu da tabbacin samun Camas! a gidansu shin ko kin manta ne? ko lokacin da muke unguwar sai tafi sati biyu bata kwana a gidansu ba tana can yawon bin maza watarana ma gidanmu take zuwa ta kwanta.” Rashida tace”Na tuna yanzu to ya za’ayi a same ta.”? Shiru tayi tana nazari itafa ba tasan ya za’ayi a sami Camas! ba dan bata tantance in da take ba……Rashida tace”,Anti Wasila ki shirya sai na raka ki government house din nasan za’a iya samunta a can.” Girgixa kanta tay tace”Har abada na bar wannan gidan tunda banda ala’ka dashi a halin yanzu, kuma bai zama lallai a samu Camas! a can ba, ban’ki ma idan anje gest house din Alhaji Ma’aruf mybe a iya samunta a can.”! Rashida tace”To ki shirya muje can d’in.” Shiru tayi tana naxari kafin tace”Rashida ba zanje ba kawai kyaleta don Allah ni na hakura taje kanta tayi wa in ta min maganar kudin shikkenan idan batai min ba na barta da Allah.” Rashida tace”Ni dai da zaki min kwatacen gest house din da naje naci ubanta wallahi sai ta baki kudinki.” Girgiza kanta tayi tace”Rashida ba zakije wannan gurin ba kawai dai tinda nace na kyaleta da Allah shikkenan.”

Rashida tace”shikkenan bari na hada mana abin kari.” Wasila ta mike suka shiga kicin din tare, sto ta bude tana duba abinda yay musu saura na kayan abinci shinkafa ce gatanan duka bata kai rabin buhu ba sai kwalin indomee biyu da taliya da macaroni mansu ma ya kare da kayan maggi babu siga saura kwali daya gwangwanin madara da milo biyu ya rage, hankalinta yay masifar tashi tace”Rashida abinda yay saura kenan?” Rashida tace”Eh mana kinga ni dai.” Frige ta bude wayam! babu komai a ciki sai robobin lemo da ruwa wanda suka sha suka mayar ciki……Tace”Innalili wa’ina ilaihi raj’iun.” Fita tayi daga kicin din ta koma palo ta zauna, tana kuka yanzu idan kayan abincin nan ya kare ya za tayi…….Shikkenan zasu komai rayuwar kuncin da sukayi a baya, Sai hawaye ya shiga zubowa daga idanunta tana tausayawa rayuwar da zasuyi nan gaba.

Tananan zaune Rashida ta fito da fulas din shayi da wata karamar kula data zubo musu indomee a ciki ta aje taje ta dauko sauran kayan da zasuyi amfani dashi gurin cin abincin, ta hada musu suka fara karyawa Wasila dai cin indomee kawai take hankalinta duk baya jikinta tunaninta ya ta’allaka gurin yanda za tayi asirinsu ya rufu….Rashida tace”Anti wasila ina gold din da kika siya kwanaki ba sai ki siyar dashi ba nasan kudin zasu isa ki fara sana’a dasu.” girgiza kanta tayi cikin tsananin damuwa da neman mafita tace”Rashida kin mata ranar da Ahamdu ya dauke ni da sunan matarshi, ranar nayi ado da da gold din har nasa lifaya keda Camas! kuka dinga kwarzanta kyawun da nayi gabakid’aya gold dina na gidan Ahmadu in banda wannan zoben dake hannuna.” Rashida jikinta yayi sanyi sosai babu shakka suna cikin tsaka mai wuya dama abinda takeji kenan gashi kuma ya faru, tace”Shiyasa tuntuni nake hanaki wani abun saboda dama ni tuntuni na dawo daga rakiyar Uwani wallahi duk wata masifa da muke ciki itace ta jefamu kullum burinta muje mu samu kudi ita tana zaune a gida, Allah ya baki miji nagari me kudi babba mai hankali wanda zai rike ki da kyau ta zugaki kin kashe auranki, gashinan komai ya jagu’be! dama abinda nake ta tunani kenan.” Ajiyar zuciya ta sauke tace”Rashida mu bar wannan maganar don Allah hausawa nacewa tun ranar gini tun ranar zane duk abinda kikaga ya samu bawa to da sanin Allah, ammafa wani abun mutum shike janyowa kanshi Ni da uwani mun so zuciyarmu kuma gashinan ta kaimu ta baro amma babu komai Allah yasa ya zama izina a garemu ni da ita, yanzu mu gama karyawa sai muje can d’orayin gidansu Camas ko Allah zai sa mu same ta.”

Uwani nacan na bacci suka shaida mata inda suka nufa cikin bacci tace dasu Allah ya kiyaye suka kadai kansu suka fita daga gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button