NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

ffan ‘kwai a ciki kusan guda ashirin, a jikinta ya d’ora ledar ya mai da zif din jakar ya zuge kana ya maida ita inda take ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace.”Gashinan karkiyi kuka gama naga shi kike shirin yi.” Shiru tayi masa ta cigaba da kokarin kwance ledar…….Kar’ba yay ya kwance mata ya d’auko d’aya ya soma ‘bare mata , ya mi’ka mata ta kar’ba da sauri gutsira biyu tayi masa ta cinye…..Tana kallon hannunshi dake kokarin ‘bare mata wani, Haka dai yayi ta aikin ‘bare mata kwai tana taunewa sai da taci guda tara sannan ta hakura ya mi’ka mata ragowar ruwan swan din da yasha d’azu ta ‘karba tana sha tana lumshe idonta sai yanzu taji dama dama a jikinta.

Uwani na tsaka da shanya kan katanga taji tsayuwar mota, dake katangar bata da tsayi sosai ana hange na waje kafin ta ankara taga Rashida ta fito daga cikin motar Wasila ma ta fito da sauri ta ajiye rigar dake hannunta ta nufi cikin dakin da take kwana mayafi ta dauko tayi hanyar fita tana kokarin yafawa a jikinta, a soro sukayi kicibus da Rashida sai ta rungumeta tana fad’in “Rashida sai yau kuka tunani dani ko? ke da waye a cikin mota ina Wasila ya jikin nata.”? Rashida ta dinga kallon mahaifiyarta ta ganinta gaje gaje yayi masifar daga mata hankali, Wasila ta shigo ta gansu sai itama ta shiga bin Uwanin da kallo jikinta sharkaf da ruwa……Gashi duk tayi wani wujuga wujuga da ita. Uwani ta rumgume Wasila tana hawaye tace” Yarinyar nan kullum dake nake kwana nake tashi a raina Alhamudullihi jiki yayi kyau masha Allahu ga cikin ki ya girma dama ai nasan mutukar kun koma gaban mai allo zai kula daku mutum ne shi mai tausayi kuma yana kaunarku.” Wasila da Rashida suka shiga binta da kallo jin abinda take fad’a kan mai allo wai yau Uwani ce ke yabon mai allo lallai duniya.

Gidan suka shiga gabad’ayansu, Wasila ta dinga bin gidan da kallo ko ina kaca kaca da kazanta iri iri ga wani wari na tashi da alama shaddar gidan ta cika tana bukatar agaji warin yayi yawa…..Ta dinga bin mahaifiyarta da wani irin kallo na tsantsar tausayi da jin kai. a hankali tace”Uwani wannan wane irin ‘kuraje ne a jikinki? dubi yanda fatar jikinki ta kod’e kinyi wani iri duk kin rame.”! ‘Kwallah ta cika kwarmin idon Uwani tace”Ku mu shiga ciki babu komai.” Bin bayanta sukayi suna mamaki tabbal akwai abunda ke faruwa da mahaifiyar tasu………Kuluwa ta fito daga dakinta kirjinta daure da dadd’aud’an zani!!! kanta babu d’ankwali tamkar hammatar d’an iska yayi wani cibiri cibiri dashi dan saboda tsabar dauda gashin kan nata har ya soma d’aukewa da kanshi wani guri da a kwai wani gurin babu…..Ganinsu Wasila yasa tasha kunnu tana fad’in “Ku kuma yaushe kuka zo.”? Wasila tayi saurin kauda kanta daga kallonta dan ji tayi tsigar jikinta na tashi kallon gashin kanta ya sanya mata tashin hankali amai na taso mata….Rashida tace” Yanzu muka zo Baba mun same ku lafiya.”? Kuluwa tace “Lafiya lau ina fata dai yau zaku juya domin dai muma bamu da abinda zamu baku koda yake dai ga uwarku nan na neman kudi zata iya daukar dawainiyarku.” Babu wanda yace mata ta tafasa ballanta ta sauke suka shige dakin ina Uwani ke zaune tana jiran shigowarsu……Nan suka tarar da ita a zaune a gefen wata guntuwar tabarma ta zabfa tagumi! Wasila ta dinga bin dakin da kallo daki sai kace zai rufta ya durkushe gashi babu labule babu ledar kasa sai wata guntuwar tabarma wacce take nuni da cewar nan ne makwancin mahaifitar tasu…..Kwallah ta zubo mata murya na rawa tace”Uwani wannan wace irin rayuwa kike ma’kaskanciya, wannan d’akin da kike ciki ya ru’be wallahi saura kad’an ya rufta bakya tsoro watarana ya rufta dake.”

Uwani na hawaye tace”Ya zanyi Wasila! Ya zanyi? nice na cuci kaina na kuma cutar daku na tabbata da kina gidan Alhaji Ahmadu da duk wannan wahalar bamu shigeta ba, nasan da tuni munfi karfin gurin zama da ci da sha da suttura, na cuci kaina na cutar daku Ubangiji Allah ya yaye mana wannan masifa.”!!! Ganin tana kuka sai suma suka fara kuka ta goge hawayenta tana fad’in “Idan dan kunga ina kuka kuma kukeyi to na daina yi sai kuyi shuru.” Wasila ta goge fuskarta tana kallonta…..Uwani a nutse

ta soma basu labarin wahalar da takesha a gidan da yanda kullum take cin ruwa sai kace agwagwa.

Wasila tace”Ai dole sanyi ya kamaki Uwani wannan wace irin masifa ce ace kullum mutum na cikin ruwa dubi fatar jikinki ta kod’e ta bushe ga wasu kuraje marasa kyawun gani sun feso miki a jiki.

Uwani tace”Wai sunanan ina sha musu magani da ai sunfi haka yawa a jikina.” Wasila ta shiga girgixa kanta tana tunanin yanda za tayi ta kubutar da mahaifiyarta daga wannan ukuba.

Uwani ta kalli Rashida tace”Wai waye ya kawo ku a mota ne.”? Rashida tace”Alhaji Ahamadu ne mijin aunti Wasila.” Da sauri ta kalli Wasilan tana neman karin bayani……Rashida itace ta shiga fada mata yanda al’amura suka faru…..Uwani ta dinga washe bakinta tana fad’in “Alhamdullhi Allah nagode maka daka amsa adduata kullum.burina mutumin nan ya dawo garemu naji dadin wannan zuwan naku kuma yau zanyi bacci harda munshari.” Wasila tace”To sai ki sauya kaya kije soro ku gaisa dan da kunya a shigo dasu wannan ‘kazamin gidan.” Uwani ta mike da sauri ta bude jakar kayanta ta dauko atamfar data rage mata dan duk kayan da tazo dasu Kuluwa ta sace taje ta siyar, sai dai kawai in ta fita taga kayanta a jikin mutane idan ta tambayesu sai suce kuluwa ce ta siyar musu shaddar wasila ma data sace gidan ma gari ta kai suka siya………Suna kokarin fita daga cikin gidan Kawu Madu ya shigo gidan yana washe bakinsa hannunsa rike da kud’i sabbin ‘yan dubu dubu kar kar dasu……Kuluwa yake kwad’awa kira ta fito daga d’aki da saurin gaske dan har zaninta na ‘kokarin fad’uwa ta rike da kyau! tana fad’in “Malam ya akayi ne.” Yace.”Ki fito kizo ki dangwali arziki ki barshi ashe yarinyar nan Wasila matar babban mutum ce, ikon Allah yafi gaban wasa! Kuluwa kinga uban kudin da mijinta ya bani yana waje shi da abokinsa sunzo cikin wata ‘karuwar mota kamar jirgin sama.”! A d’amauce! Kuluwa tayi hanyar waje tana tafiya kamar zata kifa ‘kasa saboda sauri! Kwata kwata ta manta a halin da take ciki babu dankwali da riga daga ita sai daurin kirji…..

Littafin na kudi ne….!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah What’spp numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
64
Da sauri Uwani ta tare bakin ‘kofar fita tana kallon Kuluwan cikin mamaki tace”Haba Kuluwa dubi yanayin da kike ciki babu suttura a jikinki kanki babu dankwali sannan kuma kike ‘kokarin fita haka gaban siriki karfa ki manta mutumin nan babban mutum ne kamar yanda Kawu ya fada miki idan kin fita haka ai kin zubar mana da kima da mutunci .” Kuluwa ta hau ya’ke tana washe baki tace”Wallahi duk na manta babu riga a jikina Uban kudin dana gani hannun Malam su suka gigitani amma bari inje in sanyo riga ku jirani dan Allah.” Da sauri ta koma cikin gidan jikinta sai rawa yake…..Wasila da Rashida suka bita da kallon mamaki matar mayyar kudi ce duk ta fita daga hayyacinta…..Kawu Madu kuwa na tsaye sai dariya yake yana ta dangwalar miyau a hannunshi yana lissafa kudin hannunshi, kamar zautacce ya kalli Uwani yace.”Uwani kudin nan dubu hamsin ne wallahi! kai masha Allahu gaskiya naji dad’in zuwan mutumin nan Uwani ashe haka Allah yayi wa ‘yar arziki amma saboda baki da hankali kika kashe mata aure, saboda kina mata bakin ciki, waye ya fada miki yanxu ana wasa da auran irin wad’annan mutanan? ai duk abinda ya faru ya fad’a min yanzu kafin na shigo sai ku godewa Allah da Allah yasa ya mai da auran dan da bai mayar da auran ba to da kun cutar damu wallahi dan wannan arzikin sai da mugani a nesa amma yanzu ko banza nasan zamu dinga samun zakka a kai a kai! idan Allah ya nufa ma wataran sai da kawai naji ance na fito an biya min kujerar makkah.” Kawu Ya ‘kare maganar tashi yana dariya had’e da gyara babbar rigarshi yana sake gyara xaman kudinshi a aljihu……..Kuluwa ta karaso cikin wata kod’ad’diyar atamfa da wani ya mushashshen mayafi da duk ya tattare saboda tsabar yaga jiya da yau wai nan sune karshen adakarta, sai wani washe baki take ta kalli Uwani tace”Ai haka yayi ko.”? Uwani dai shiru tayi dan bata da abince wa sam ma bata so Kuluwa ta bisu gani take zata iya yin wani abun na rashin hankali ita kuma bata so yanzu mutuncinsu a zube a gurin Ahmadu……Kawu ne yay gaba suka biyo bayanshi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button