NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Bayan shigarta daki kuka taci ta ‘koshi kana taje tayi alwala tai sallah ta fito palo nan ta tarar dasu Uwani zaune suna mai da magana ita da rashida zama tayi kan kujera kafin tace”Rashida bani abinci naci rabona da abinci tun jiya dana bar nan.” Rashida ta mike da sauri ta nufu kicin….Ta kalli Uwani dake shan kunu! tace”Uwani ina Camas.”? Tace”Tuntuni tayi tafiyarta bayan rashida ta gama zaginta.” Tace”Wane irin zagi kuma? Ke rashida me Camas! tayi miki kike zaginta.” Tafada tana kallon Rashidan

dake kokarin ajiye mata abinci a gabanta.” Tace.”anti Wasila bayan shigarki daki Camas! ta dinga zuga Uwani wai sai munyi karuwanci kamar yanda takeyi shine nace ta tashi ta fita amma ban zageta ba.” Uwani tace”Ma’karyaciyar banza da wofi kika zageni ma ballanta Camas.” Wasila ba tace komai ba dan ba taji haushin zagin da rashida tayi wa Camas din ba saboda itama ta tsani tayi mata maganar karuwanci wato saboda taga bata gurin shine take zuga Uwani tana kara hawa! aikuwa da yardar Allah ba za suyi karuwanci ba……..Abincin take cuccusuwa tana ya mutsa fuska duk da abincin me kyau ne amma sam bata jin testing dinshi a bakinta abubuwan da suka dame suna da yawa….Rashida ta mika mata ruwa tasha kana tace”Ki bani wayarki in kira Camas muje atm zan ciro kudi kudin dana cire jiya na bar jakar cikin motarshi bani da ko kwabo yanzu sai dari takwas da sukayi min shaura.”
Rashida tace “Aikuwa babu kudi a wayar.” Tace dauko min jakata dana zo da ita a daki.” Rashida taje ta dauko mata jakar ta bata dari biyu tace taje ta siyo kati.” bakin titi.


“Wai shin kiran me kake min ne? da alama dai an samu harka dan idan naga irin wannan kiran naka har dadi nakeji wallahi.” Khalifa ne ke wannan maganar lokacin da yake kokarin zama kusa dashi

Ya dan gyara zamanshi yana fad’in”Ba alkairi ne yasa na kira ka ba.” Khalifa yayi saurin kallonshi fuskarsa ta rage walwalar da ya shigo da ita yace.”Allah yasa dai lafiya.” ? Ya mike tsaye ya nufi bakin window hannuwansa duka a bayanshi, Khalifa ya bishi da kallo yana nazarin palon baiji motsin mutum ba, jikinsa yayi sanyi a hankali ya mike ya iske inda yake tsaye ya dafa kafadarsa a hankali yace.”Meke faruwa ne? ina matar gidan take.”? Ya juyo da wata iriyar fuska mara dad’in kallo yace.”Na saketa.”!!! Kalmar ta dinga yiwa Khalifa amsa kuwwa! a kunnansa, ya bude bakinsa na sar’kewa yace.”Ka saketa.”!? Girgiza kanshi yay yana so ya tabbatar masa! Khalifa ya dinga binshi da kallon mamaki kafin yace”Me ya faru! me yasa ka saketa!? me yasa ka yanke irin wannan hukuncin mara dad’i! duk da Allah ne ya hallatashi amma ba abune mai dad’in ji da fad’e a baki ba wallahi bakaji yanda naji a jikina ba fad’ar wannan kalma da kayi.”

Ba tare da ya cewa khalifa uffan ba ya wuce shi yaje ya nemi guri ya zauna! hade da rufe fuskarshi da tafukan hannayeshi! Khalifa ya zauna kusa dashi yana me dafa kafadarshi da fadin”Ka fad’a min abinda ke faruwa ni ka barni cikin duhu.”! Ya jima hannunsa rufe a fuskarsa kafin ya cire ya tsirawa khalifa ido tiryan tiryan ya shiga fad’a mishi abubuwan da suka faru ya kunna mishi rocouding muryar Wasila da As da irin tsare tsaren da sukeyi a kanshi, ya kuma tabbatar mishi da cewar ajiya Allah ne ya tsareshi dan a yanda ‘yan daban gidan gomnati suka zo mishi to babu shakka zasu iya kasheshi ko suyi masa rauni.’

Khalifa ya jima yana mamaki gami da jajanta al’amarin! hakika abinda wasila ta aikata babban abune wanda ya cancanta da ayi mata ko wane irin hukunci, to amma kuma baiji dadin hukuncin da ya yanke a kanta, da tayi shawara dashi da farko ba zai yarda ya saketa ba, zai fahintar dashi cewar sakin bashi ne sulotion, ya zauna da ita tinda yayi wa kawunta alkawari kuma yayi mata uziri! duba da cewar akwai kuruciya a tattare da ita in yaso yayi mata horon da za tagane abinda ta aikata babban abu ne, shawara ta karshe da zai bashi shine yayi aure yayi rayuwa da matarshi a cikin gidan tana kallo yasan dole za tayi hankali ta shiga taitayinta amma yaji zafin sakin da yay wa yarinyar mutune ya mai da ta karamar bazawara.

Ajiyar zuciya ya sauke yace.”A gaskiya banji dadin wannan abu ni da kayi shawara dani ba zan bari ka saketa ba, amma yanzu tinda har haka ta kasance please ka dauki niyya ka kuma ‘kudirta a ranka kan cewar ka mayar da ita ni da kaina zanje na dawo maka da ita, sai shawara ta biyu shine kayi gaggawar yin aure domun ta gane kuranta.

Ya kalleshi yana ya mutse fuskarsa yace.”Kafi kowa sanin idan na bar abu na barshi har abadah! a yanzu idan da wacce na tsana a duniya to wannan yarinyar ce na natseta wallahi, bani kaunar ganinta, saboda haka maganar ma in da

wo da ita bata taso ba, aure kuma sai na huta zanyi.”

Khalifa yace.”Kar kayiwa mai allo haka Ahamdu! ka duba daraja da furfurar dattijon! ka duba amanar da ya baka! aure baifi sati hudu ba har anyi an gama! wannan wace irin rayuwa ce.”! Kai ya shiga girgizawa yana wani irin mirmishi na takaici yace.”Komai abinka ba zan dawo da yarinyar nan ba taje kawai! shi kuma mai allo da kaina zanje nai mishi bayanin komai.” Khalifa ya dinga kallonshi yana girgiza kanshi tabbas yasan halin abokin nashi! da zuciya da kuma ramuwar gayya ba tun yau ba! Yasan bai da hakuri ko kad’an! mutukar kayi mishi abu bai rama ba to shine yaga dama.


Ta kira wayar Camas! ta kai sau ashirin bata dauka ba, sai abu ya shiga bata mamaki! taje wayar tayi tana fadin”Ko bata kusa da wayar ne bari anjima na sake kiranta……Ita kuwa Camas! a lokacin suna tare da As yana shaida mata abinda ya faru dashi itama tana shaida masa irin hukucin da Wasila ta yanke kan cewa ta bar harkar Siyasa kuma ta tabbatar masa da cewar Ahamdu ya saketa yanzu haka tana gidanta.
As yaji dad’in labarin Camas! sai dai kuma baiji dadin furucin da tayi ba na cewa ta bar harkar siyasa hakika ta zama wani jigo a tafiyar tasu, dole ya shirya yaje gidan domin ya rarrasheta ta dawo kawai su cigaba da fafatawa,

Camas! na fita daga gest house din As kira ya sake shigowa wayarta koda ta duba taga Numbar Rashida ce sai ta kashe tana jan tsaki tasan dai zancen gizo baya wuce na ‘koki! Tana kokarin shiga motarta text ya shigo ta bude tana dubawa.

Camas! kina ina ne? inata kiran wayarki baki dauka ba dan Allah kizo gidana yanzu zamuje banki zan cire kudi yanzu ina jiranki

Tsaki taja mai tsayi lokacin da tagama karanta text din ta bude mota ta shiga tana fad’in”Shashasha kawai ai kud’in nan sun shiga accont dina kenan! ke kin tsira da gida ni na tsira da kudi a tafiyar nan! babu abinda baki mallaka ba dan’kareran gida iyayen kudi gwala gwalai, ni kuwa fa in banda wannnan fankon motar babu abinda na tsira dashi, saboda haka na cinye kudi wallahi komai za’ayi sai dai ayi.” Tuka motarta tayi ta bar gurin hankalinta a kwance.

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
51

Wasila tayi ta tsammanin amsar Camas! taji shiru har wajejen karfe goma na dare bata daina kiran Camas! a waya ba, gashi dai tana shiga amma kuma taki dauka……Uwani tace”Wai kiran me kike mata ne? ni nasan da wuya Camas! ta dawo gidanan dan baki ga irin zagin da rashida tayi mata ba.” Tace.”Uwani ba wannan matsalar bace, kin san na fad’a miki jiya Ahmdu yace zai min bincike cikin accont dina sai na yanke shawarar kwashe kudina dake ciki na mayar accont din camas! kudin suna da yawa fa kusan miliyan biyar ne zuwa shida, a jiya na ciro dubu hamsin to jakar tawa na motarshi, ban dauko ba, wannan dubu dayan ma da nayi kudin mota gurin zuwa nan na siyi kati Allah ne ya taimakeni na tsinta cikin jakar dana zo da ita, kinga yanzu duka sau dari biyar a hannuna gashi ina ta kiran Camas a waya taki dauka.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button