NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Alhamdullhi an d’aura auran Uwani da malam a gidan Kawunta dake Tudun maliki, bayan daurin aurane sai suka kuma nufi can pataskum din domin gaisuwa sannan kuma da dauko amarya, malam sai washe baki yake yana baza babbar riga Shi kuwa Amadu kunya ce take kamashi wai daurin auran Uwar matarshi ake sai dai kawai ya girgiza kansa yana murmushi.

Uwani tayi ado dai-dai gwargwado kuruciyarta ta sake fitowa tamkar bata haifi Wasila ba wani cewa zaiyi yayarsu ce anyi mata kitso da jan lalle tana sanye da sabuwar atamfa ‘yar ingila jama’a sun cika gidan Kawu Madu sai hidima ake Kuluwa sai washe baki takeyi tana karbar baki, Kuluwa yanzu ta dan rage kazanta dan Kawu Madu ya soma dawowa hayyacinsa asirin da tayi masa ya karye dan da ya farga da irin kazantar da takeyi yace.”Wallahi ta kuka da

kanta idan ya tashi aure zai aure mace mai tsabta ‘yar gayu tunda shi ba kazami bane.”
Aikuwa Kuluwa ta tsorata sai ta dage da wanka da wani had’e da kitso akai akai kuma garin Allah yana wayewa zata sa brush ta wanke bakinta tun yana futar da jini har ya daina, amma duk da wannan abun da takeyi Kawu Madu bai saduda ba yana nan da bazawarsa ‘yar ‘kwalisa har sun tsayar da ranar daurin auransu, Kuluwan bata sani ba sai dai jama’a da yawa sun sani shuru kawai akayi mata ana jiran ranar da amarya zata zo aga me zai faru.

Amadu kasa shiga gidan yay sai ya zauna cikin motar…..Kunyar hada ido yake da mahaifiyar matar tashi, to itama Uwanin tunda taji jama’a nata surutu da amabatar sunan mijin ‘yar tata sai ta kasa fitowa tsakar gida ta zauna cikin daki abinta
Kawu Madu da kansa ya fita har bakin motar da yake ciki suka gaisa cikin mutuncin da karamci sannan fa mutane suka farga dashi sai suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa, ganin hakan kamar bai dace ba yasa ya fito daga motar yana gaisawa da jama’a cikin sakin fuska da dattako.

Karfe shida sun iso gidan……Lokacin Rashida da Wasila sun saka turare mai kamshi a dakin mahaifiyar tasu wanda ya sha jere mai kyau kuma na zamani, katon gado ne da katifa mai kyau sai katuwar sif mai murfi shida akwatinanta akai sai mudubi da drowars guda biyu koran kafet ne malale a dakin labule koraye da net dinsu, dakin yayi kyau sosai.
Su Kuluwa da Ina Tabawa da Ita mai waina suka rako Uwani dakinta Bitan ta karbesu hannu bibbiyu aka gaisa cikin mutunci da mutuntawa…………Wasila bata samu sun ke’be da mahaifiyarta ba ya dinga kiranta a waya ta fito su tafi saboda dare ya soma yi….Uwani tace”Ki shige ku tafi daga baya sai ki dawo ina laifi ma da ya barki kikayi kwanaki biyu, Babu yanda ta iya haka tasa yara suka dauki jakar kayanta Rashida kam fujirewa tayi wai tunda babu makaranta ba zata bisu ba sai jarrabawarsu ta fito, Uwani kam bata ce mata komai ba itama zata fiso ta zauna a gabanta…..Wasila ta fito tana sallama da jama’ar dake gidan duk zuciyarta babu dad’i Inna hajara tasa yara suka fitar mata da kayayyakinta wajan motar……Ita Kuluwa fad’i take “Kice ina gaisheshi.” Wasila ko kallonta batayi ba ta fice daga gidan, sukayi karo da malam zai shigo sai ta zube a kas tana kuka, Yace.”meyasa kike kuka Wasila. Tace”Wallahi Kawu bana so na tafiya yau.” Yace.”Kiyi hakuri kibi umarin mijinki Allah yay miki albarka.” Ta amsa da amin tana mikewa, Yace.”Ina Rashidar.”? Tace”Wai anan zata zauna sai sanda jarrabawarmu ta fito.” Malam yace.”Zancan banza zancen hofi! jirani anan na fito da ita.”Ya shiga gidan yana baza babbar rigarsa, Rashida na dakin Uwani malam ya shiga gidan yana fadin”Ina Rashida. tace.”Gani Kawu.” Yace.”Maza ki fito ku tafi ni bana son shashanci.” Tace.”Kawu Uwani ce tace.”Na zauna.” Sai ya daga labulen dakin yana fad’in “Uwani anya hukuncin nan yayi dai-dai kuwa.”?
Ta dago kai ta kalleshi tace” Malam ai ba cewa nayi ta zauna gabadaya ba idan jarrabawarsu ta fito zata tafi.”
Yace.”To! to ai babu komai Allah ya kaimu.” Labulan dakin ya saki Ya nufi dakin Bitan! lokacin ita kuma tana kicin tana ta kokarin raba abinci dan su Kuluwa suna nan basu tafi ba sai gobe tukkuna.

Dama tuntuni Garba ya shigar mata da kayanta cikin motar daga ita sai baby zahra da jakarta ta nufi motar, wanda yana hangota ya bude motar yana kallonta har ta ‘karaso ta shiga tana kumbura fuska, baice mata komai ba ya mayar da murfin motar ya rufe, Garba ya shiga da sauri yaja motar suka dauki hanya.
Baby zahra ya kar’ba daga hannunta yana mata wasa sai kyalkyala dariya takeyi,
Yace.”Momyna nayi missing dinki da yawa amma na lura ke da momynki baku damu dani ba, kunyi ki’ba kunyi lafiya kwana biyu.”
Kallonsa tayi tana dan sassauta murya tace”Allah Habibi ka yanke min jin dadina ina tare da ‘yan uwana kawai sai kace lallai sai mun tafi.”
Yace.”Akwai wani jin dadi wanda ya wuce ace kina tare dani.”?
Shuru tayi masa tana gyara fuskarta, Yace.”Ina Rashida.”? A hankali tace”Wai ba zata dawoba sai jarrabawa ta fito.” Yace.”To karatun isilamiyyarmu fa.” Ajiyar zuciya ta sauke tace.”Ni na ma

nta ma wallahi sabida bana cikin nutsuwa kuma dai Uwani ce tace dole sai ta zauna.”
Yace.”To tunda Momy ce ta yanke wannan hukuncin bani da magana amma dai naso ta dawo yanzu domin mu had’a izifi talatin d’inmu da ita.”
Tace.”Itace ta jawowa kanta, idan ta dawo na koya mata inda aka wuceta.” Yace.”To malama.” Shuru motar tayi na minti biyar ya dan kalleta yana kashe ido yace.”Wane tanadi kikayi min.” ? A hankali yay maganar saboda Garba. Fari tayi da ido tace” Kabari muje zaka gani.”
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana Allah Allah su sauka gida yayi masifar d’okanta da kasantuwa a tare da ita.

A daran ranar sunyi soyayya sosai wacce ta sanya su zubar da hawaye dukaninsu suka tabbatar wa da kansu cewar idan babu d’ayansu a cikin rayuwarsu to babu shakka rayuwarsu tana cikin kalubale mai girma.

Bayan dawowarta da kwana uku Hafsa ta haihu d’a namiji ta haifa A ranar data haihu sukaje ganin jinjiri Hafsa ta ‘karewa Wasila tanadi sosai tace”Wallahi kinji kunya ace wai wannan zuwan da kikayi shine na farko gidana ai ina sane dake shiyasa nima bana zuwa inda kike koda yake laifin ba na kowa bane na governor ne gashinan ai yana jina.
Amadu da yaga Hafsa ta fusata tana sakin maganganu sai ya fara kokarin kare kanshi da cewar shifa ba laifinsa bane nata tunda yana cewa suzo sai tace tana da uziri.
Wasila ta dinga mamakinsa babba dashi da karya, Hafsa tace” Ai nasan kafad’a ne domun ka wanke kanka dama ina ciki da kai kaine ke hanata zuwa inda nake nagode.
Sai ya shiga bata hakuri Wasilan na tayashi da kyar Hafsa ta sako ta basu jaririn suka dauka……Afnan ta samu abokinyar wasa, baby zahra ta makale jikin Wasila wai lallai sai ta bita su dinga wasa da babynta.
Amadu yace.”Kome zakiyu ba zamu tafi dake ba ki hanamu kwanciyar hankali….Khalifa na dariya yace”Afnan fa tayi wayo yanzu ta daina kuka.” Yace.”Kome zaka fada kan Afnan ba zan yarda ba ai ni yarinyar ta shani na warke………..Amadu da Khalifa suka fita sabida bakin dake zuwa, Cikinsu harda Zeey da sauran ‘yan gidansu, Zeey tamkar ba gidan ‘yar uwarta tazo ba ta kasa sakin jikinta duk dan ganin Wasila a gidan wani irin kunyar yarinyar takeji sosai sai yanzu ta gane cewar abinda tayi itama bata kyauta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button