NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Da ‘kyar bacci ya dauketa saboda tsabar bakin ciki da takaici, ta tashi da safe cikin rashin walwala har Hajja ta shigo dakin suka gaisa ta shirya zahra har taso ta fahimci wani abu amma dai ba tace mata komai ba itama so take ta cika ar’bain ta tafi ai tayi abinda tayi, Hajja na fita da Zahra ita kuma ta shiga toilet domin yin nata wankan.
Kafin ta fara wankan sai da ta shiga cikin ruwan d’umi tayi minti goma sha biyar sannan ta fito tayi wankanta da sabulai masu kyau da kamshi ta fito daure da karamin towel iya cinyarta………Ashe yana zaune a dakin ya shigo tana toliet sai ya zauna zaman jiran fitowarta…….Ganin ta a haka fatar jikinta na wani irin she’ki da sul’bi ga santala santalan cinyoyinta a waje dik sai ya rasa nutsuwarsa ya dinga binta da wani mayen kallo har ta wuceshi ta nufi mirror tana zum’buro bakinta tare da sauya salon tafiyarta.
Kasa daurewa yay ya mi’ke ya nufi inda take……Tana sane ta bude towel din wai zata sake d’aurawa aikuwa ya hangota ta madubi hankali a tashe yaje ya ri’ke towel din yana kokarin fuzgewa daga hannunta.
Ta dan tureshi kadan ta bar masa gurin……Matseta yay jikin wardorbe yana rarraba idanunsa a jikinta……….Ta dinga ture kirjinsa tana son yin kuka amma dai ta daure saboda bata so ya dinga raina mata hankali…..”Wai dan Allah meye haka bafa girmanka bane hakan da kakeyi ka kyaleni ni nasa kayana, kuma gidan nan dole ne ma na barshi dan ba zan zauna a inda ba’a bukatar dangina ba.” A kausashe take maganar tana tuttureshi daga jikinta
Muryarshi ba sosai take fita ba yace.”Wace irin magana kikeyi ne waye baya kaunar dangin ki da har kike ikirarin barin gidan auranki.”
Sai ta fashe da kuka tana wani irin bubbuga ‘kafafunta ta tureshi da ‘karfi tana haki ta matsa gefe tana kallonshi tace”Eh dama zaka fad’i haka mana yau kwanan Inna Hajara nawa da tafiya ka ta’ba tambayata dalilin tafiyar ta!? Sannan yau kwanana nawa da haihuwa me yasa baka ta’ba tunani koda sau d’aya ne kace bari ka tura d’aya daga cikin yaranka domin yaje ya dauko mahaifiyata kan tazo taga abinda na haifa, na sani dama tuntuni na san da cewar baka dauki Uwata a matsayin komai ba dan da ka dauketa da daraja to da duk inda take kaje ka gaisheta da kanka kuma ka shaida mata na haihu da abinda na haifa…..To nagaji ni ba shashasha bace nasan kuma inda ke min ciwo zanyi tafiyata in yaso sai ka auro wacce kake ganin Iyayenta sune dai-dai da kai da kimarka.”
Tana gama maganarta ta bude wardorbe ta duba kayanta t

a dauki riga da sket na wani had’addan swiss less ta shirya jikinta duk yana tsaye kamar gunki yana kallonta da mamakin kalamanta, bude kofar dakin ce ta sanya shi dawowa hayyacinsa, yay gaggawar kallon bakin kofar sai ya hango ficewarta daga dakin tare da jan kofar da karfin gaske.

Littafin na kudi ne!
Idan kika futar min da book keda Allah! Idan kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
77
Ya jima a tsaye a tsakiyar d’akin yana mamakin irin maganganun da yarinyar ta watsa masa, ransa yayi masifar ‘baci sosai ashe raini har ya soma shiga tsakaninsu tunda har zata iya d’aga masa murya! gurin magana tana fad’a masa duk maganar da tazo bakinta tana d’aga masa harshe kamar zata zageshi Idan tana so ta nusar dashi abinda ke zuciyarta ai sai tayi masa bayani cikin fahimta ba da irin wannan sigar ba, dole ne ma ya dauki tsatstsauran mataki a kanta, idan dan wannan abun na jikinta take kokarin zaginsa to taje ta ri’ke kayanta zai nuna mata shi d’an halak ne.
Koda ya fito daga ‘dakin bai kalli inda suke zaune ba ya wuce bedroom dinsa ransa duk a jagule.

Wasila kuwa jin zuciyarta take wasai tunda ta samu ta fad’i abinda ke cikin ranta shikkenan itama ta dauki al’kwarin akan ba zata sake zama ya dinga raina ta ba ballanta har ya dinga d’aga wayar ‘yan matansa a gabanta sai ta nuna masa itama macace wacce tasan abinda takeyi.

A shirye ya fito da shirin fita, ya tsaya suna magana da Hajja, Hajja tace”Nima fa na kusa tafiya tunda dai Allah yasa ta haihu lafiya shikkenan zan koma gida.” Yace.”Kiyi hakuri kiyi zamanki tare damu.” Tace”A’a dai gwara na kuma gidana bana dinga zama cikin yara ba.” Yace.”Hajja ai zaman naki cikin Yara gyara kike ba ‘barna ba.” Wasila da kanta yake sunkuye tayi saurin dago kanta tana kallonsa, sai taga kamar magana yake fad’a mata kan Inna Hajara oh! wannan mutum baya barin takwana! wato Yana nufin Inna Hajara itake aikata ‘barna kenan……Mi’kewa tayi ta bar musu gurin ba tare da tayi kuskuran kallonshi ba, Hajja ce ta bita da kallo sosai ta fuskanci akwai matsala a tsakaninsu amma kuma ba za tayi masu magana ba sai ranar da zata tafi tukkuna idan kuma sun dai-daita kansu shikkenan.

Yana fita Garba ya daukeshi a mota kafin ya ajeshi cikin ma’aikatarshi yake Umartarshi da cewar idan ya saukeshi ya nufi can garin su Uwani Patskum yaje ya sanar musu da cewar Wasilan ta haihu idan da me ra’ayi zuwa yaga abinda ta haifa sai ya dauko shi yazo dashi…..Hakan ce ta kasance Garba na saukeshi sai ya dauki hanya kamar yanda ya umarceshi.

Suna zaune a palo bayan azahar dan uku ma ta kusa Rashida ma ta dawo daga makaranta, kawai sai sukaji sallamarsu su Uwani da Kuluwa dasu Inna Tabawa……..Rashida ta mi’ke a guje taje ta bude musu kofar falon suka shigo ciki….Wasila ta mi’ke tsaye fuskarta cike da! walwala da farin ciki mara misaltuwa, Tabawa Iya mai waina da Uwani suka nemi guri suka zazzauna a nutse ita kuwa Kuluwa sai kalle kalle take tana ya’ke dafaffun ha’koranta da kyar ta zauna kan kujerar tana wani irin abu irin na marasa gaskiya……Hajja ta dinga fadin “Sannuku da zuwa kai masha Allah sannuku Wallahi ko jiya sai da mukayi zancenku ashe kuna tafe.” Inna Tabawa tace”Aikuwa dai munata sa rana sai yau Allah ya nufa yau din ma Ai maigidan nan ne ya tura a ka dauko mu…..Kuluwa tayi saurin kar’be maganar tace”Wallahi kuwa ai rashin kud’in mota duk shine yayi mana cikas da tuni munzo anyi hidimar suna damu ace yarinya ta haihu babu danginta ai da kunya gashi duk muna raye a duniyar.”
Wasila taji kamar ta kwada mata mari jin abinda take fad’a shashashar mace kawai daga zuwanta har ta soma sakin layi….Ita kuwa Hajja murmushi tayi kawai ta mi’ke tana kallon Rashida tace”Kije ki kawo musu abinci tunda Rabe ya fita.” Rashida ta mi’ke ta nufi kicin cike da takaicin Kuluwa da haukanta.

Kuluwa sai washe baki take tana kallon baby zahra dake hannunta tace”Yarinyar tubarakallah kyakykyawa gata da jikin girma kamar tayi wata uku kai masha Allah.” Uwani ta kalleta tana dan jan tsaki cikin ranta, shiyasa fa taki amincewa da zuwansu tuntuni saboda hauka da rashin kamun kai irin na kuluwan

Inna Tabawa ta kar’bi yar tana sanya mata albarka kana ta mi’kawa ‘Yar uwarta iya mai wani itama ta sanya mata albarka ta mi’kawa Uwani, kunya ta hana ta ‘karbar yarinyar sai dai tace”Allah ya rayata tafarkin addinin musulunci.” Ganin ta kasa kar’bar yarinyar yasa Kuluwa dashare baki tace”Uwani kunya ki keji ne ai dole jikar ‘yar fari hahahahaha.” ta karashe maganar tana dariya kamar sabuwa

r mahaukaciya sai wani mutsu mutsu takeyi……Uwani girgiza kanta tayi tayi mata banza ba tace mata komai ba haka su Inna Tabawa dama suma haushinta sukeji………Koda Rashida ta jere musu abinci kan daining Kuluwa kasa zama tayi kan kujerar sai kauyanci takeyi duk ta hargitsa musu guri…..Wasila tace”Rashida ki kwashe abincin daga dainnig din ki shirya musu shi kan daddumar can ta gefe sai sunfi jin dadin hakan.”
Da sauri Kuluwa tace”Aikam dan gaskiya zama kan wannan abun ba zaiyi dadin cin abinci ba gwara mutum ya zauna a ‘kas yanda abincin zaifi tsirga masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button