NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Hajja tace”Eh ‘kwarai kam amma kika sani ko wani abune ya dauke masa hankali tunda kinga kwana biyun nan abubuwa da yawa suna dauke masa hankali, yana da kyau ki sanar masa da zuwan nasu watakila ko mantawa yayi.” Tace”Shikkenan Hajja.” Daki ta nufa domun kiran wayarshi kamar yanda Hajjan ta umarceta sam bata so suyi ta jayayya da matar.

Suna tare d

a khalifa yaga kiran wayarta sai ya aje wayar suka cigaba da abinda sukeyi shi da Khalifan wanda har ya shiga mamakin ganin bai daga wayar ba ya sanya yace.”Da alama dai ‘yan mata da zawaran dake damunka ne tunda naga baka dauki wayar ba.” ba tare da ya bawa maganar mahimanci ba yace.”Wasila ce.” Khalifa ya kalleshi cike da mamaki yace.”Lefi tayi kenan ake hukuntata ta wannan hanyar.” Murmushin takaici yay mai tafe da bacin rai yace.”Khalifa na ta’ba ganin wanda ya samu damar da wannan yarinyar ta samu a kaina kuwa.”? Khalifa ya girgiza kansa yace.”Gaskiya ban ta’ba gani ba nima kana sonta sosai dan duk wasu alamu sun nuna.” Ya girgixa kanshi cikin takaici yace.”Nima nasan da haka khalifa wannan damar data samu ce ta sanya take takani yanda ranta yake so yarinya ‘kankanuwa ta dinga nuna ni da yatsa tana daga mun murya gurin magana tamkar zata zageni.”
Khalifa yace.”Subahanallahi! me ya janyo hakan.” ?Tsaki yaja yace.”Saboda kawai na nemi hakkina shikkenan cibi ya zama ‘kari.”
Khalifa yace.”Ban gane ba.”? A nutse ya kalleshi ya dan gyara zamansa ya soma warware masa abinda yake faruwa tsakaninsu.”
Khalifa yace.”Kai nifa shiyasa sam bana son wannan zaman jegon wallahi duk daga wannan zaman ake lalata maka mata , yanzu ita wannan matar abinda tayi shine dai-dai da girmanta da komai ta dinga d’ora yarinya kan turba mara kyau, idan bata sauke maka bukatarka ba gurin wa zakaje tunda kai ba manemin mata bane.”
Ya sauke ajiyar zuciya ransa a ‘bace yace.”Allah Khalifa yarinyar nan tayi wasa sai na ‘kara aure bana son hauka da da’ki’kanci wallahi kuma zata gane bata da wayo.” Khalifa yace.”A’a kayi hakuri dai ka cigaba da rarrashinta kasan yarinya ce.”Tsaki yaja yace.”Allah ya sawa’ke khalifa bazan kuma zuwa gunta sa wata bukata ba taje ra rike kayanta nima na rike nawa zan kuma fara neman aure.”
Khalifa yace”Yanzu ka sauka daga kan ra’ayinka kenan.”?
Yace.”Duk wani abu da zanyi itace ta jawowa kanta ni babu ruwana.” Khalifa yace.”To Allah ya za’ba abinda yafi alkairi.” Ya amsa sa ameen.” Lokacin kiran ta ya sake shigowa wayar tashi yana ganin sunanta ya kashe wayar yana jan tsaki.

Cike da takaici da mugun ba’kin ciki ta fito daga d’akin murya na rawa Tace”Hajja bai dauki wayar ba watakila ko baya kusa da wayar ne.” Hajja tace”E to hakan na iya kasancewa.” Mikewa tayi ta shiga daki tana fad’in “Ku dan jirani na fito.”
Uwani dasu Inna Tabawa suka mike Wasila ta jagorace su suka fita Ita Kuluwa zama tayi har sai da Hajja ta fito daga daki ta mi’ka mata karuwar ledar dake hannunta tace”Gashinan turaman atamfofine da mayafai da sabulai sai ku kasafta a tsakaninku.” Kuluwa ta kar’be da sauri jikinta na kyarma sai washe bakinta take tana ta zabga godiya, Hajja tace.”Babu komai Kuluwa ku gaida gida mungode.”

Suna can parking spece Kuluwa takaraso hammatar ta ma’kale da ledar kayan da Hajja ta basu sai murna takeyi tace”To Wasila da Rashida mu mun tafi sai mun sake zuwa ke Wasila idan maigadan nawa ya dawo to ki mi’ka gaisuwata gurinsa tunda dai rowarsa kike mana.” Wasila tana daure fuska tace”Zai ji ku gaida gida ku gaishe da Kawu Madu.” Suka dinga amsawa da “ameen.” Duk suka shiga cikin motar Garba yaja suka fita daga cikin gidan……Wasila da Rashida suka juya jikinsu a sanyaye suka koma ciki To itama Uwanin dai daurewa kawai takeyi amma zuciyarta babu dad’i sam! tana bala’in ‘kaunar ‘yayanta kamar yanda suke ‘kaunarta.

Littafin na kudi ne……!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
78

Sa’ko na mussaman zuwa gareka Amadu ‘kawayen Wasila irin su Mumy Farhan, Bomis Zainab kankara Mrs Aliyu Nafisa Buhari Hauwa Chindo, Sakina Ummee da dai sauransu, sunce kayi hakuri dan Allah karkayiwa Wasila kishiya kayi mata uziri saboda yarinya ce, idan kuma ka kuskura ka ‘kara aure to zaka gane baka da wayo dan duk wacce zaka aura ba zata kama ‘kafar Wasila ba, zaka dawo inda kake salati kana kiran sunan Allah???????? babu ruwana Sistar Sakina ce tafad’a???????? sannan Sistar Jamila tace duk wacce zaka aura sunanta salamatu salam dan ba zata iya da jarabarka ba???? babu ruwana! Jamila da Ummee ne suka fad’a ni dai ‘yar aike ce……Momyna tace kayi auranka dan ba Wasila ce kadai mace ba, takwara Fatima Yakubu ma haka tafad’a Sai sistar Hadiza Shall itama haka tace ka more rayuwarka, Shafa’a S Yari da Bilba sunce kayi aure ka more rayuwarka???????????? ni dai na isar da sa’kona Amadu sai ka yanke shawarar da zata fishe ka, nima nace ba Wasila ce kad’ai autar mat…….????????

Cikin sanyin jiki suka koma cikin gidan Hajja ta gansu duk babu kuzari a tare dasu tace”Ai kam ni kaina naso su zauna su danyi kwana biyu ku samu sakewa da mahaifiyarku amma ace daga zuwa sai su tafi wallahi banji dadin hakan ba sai kace wad’anda ake kora.”
Rashida ta goge hawaye tace”Nima naso su zauna wallahi yanzu anti Wasila yaushe zamuje to.” Wasila ta kalleta ranta duk babu dad’i tace.”Sai an d’an kwana biyu baby tayi ‘kwari zamuje insha Allahu.” Hajja tace”Kwarai kuwa hakan yana da kyau, Allah ya kaimu ya bamu lafiya mai amfani.” Duk suka amsa da “ameen.”

To har dai kusan goma da wajan rabi bai shigo gidan ba Hajja na kokarin shiga daki ta kwanta ya shigo da sallama a bakinsa……Dukaninsu suka amsa suna masa sannu da zuwa.
Ya kalli Hajja yace.”Ashe baki kwanta ba hajja ko kema kallon kike.”? Tace”Oh!oh kai nake ta jira ka dawo ai.” Yace.”To Allah yasa lafiya.”Ganin yana ‘kokarin zama ya sanya ta mi’ke a hankali ta bar gurin, Rashida ma ganin ‘yar uwarta ta tashi sai itama tayi yun’kurin mi’kewa yace.”Rashida koma kiyi zamanki ya kina kallo zaki tashi kuma.”
Cike da kunya da jin nauyi ta koma ta zauna ta maida hankalinta kan tv…..Hajja tace” Dazu munyi ba’ki a gidanan na sanya Wasila tayi kiranka a waya kazo ku gaisa duk da nasan da cewar kasan da zuwan nasu, bai kamata ace suzo har su tafi baka zo kun gaisa da juna ba.”
Ya d’an dafe kansa yana girgixa kai ya kai minti uku a haka kafin ya d’ago kansa yana kallon Hajjan yace.”Wallahi Hajja na manta shaf! ni da kaina na sanya Garba yaje ya daukosu amma kuma banyi tsammanin yau zasu koma ba shiyasa kwata kwata ban mai da hankalina gurin dawowa gida da wuri ba.”
Hajja tace”Aikuwa ko awanni uku basu cika ba suka tafi dan babu yanda banyi dasu su zauna su kwana biyu ba suka ki.”
Yace.”Ashsha! nima ban so hakan ba naso mu gaisa dasu wallahi amma babu damuwa Insha Allahu zamu shirya muje idan momy tayi kwari.”
Hajja tace”To yawwa yanzu naji kayi magana dan haka naji ita Wasilan ma ta fad’a to dan Allah ka mai da hankali kada ka shiririce ka kai yaran nan su kwana biyu tare da mahaifiyarsu.”
Yace.”Insha Allah Hajja.” Mikewa yay yace.”Bari na shiga nayi wanka.” Hajja tace”To sai da safe dan nima shiga zanyi na kwanta.”
Yace.”Hajja Allah ya tashemu lafiya.” Hajja ta mike ta nufi daki shima ya nufi dakinsa. suka var Rashida ita kadai tana kallo.
Wanka yay ya fito yana mamakin zuwan bakin da kuma tafiyarsu a gaggauce baiji dad’i ba gaskiya sai kace wad’anda ake kora ai sa bari su kwana tukkuna sai su koma gida, zuciyarsa ta shiga wasi-wasi kan Wasila yana tunanin kamar itace za tace su tafi tunda gashi tana fad’awa Hajja zasuje idan ankwana to kuwa idan hakane nufinta babu inda za taje duk wanda ke son ganinta daga can garin sai da yazo koda kuwa mahaifiyarta ce yana da inda zai sauketa, amma babu inda zataje masa da yarinya suje suyi kwana da kwanaki a wani guri.
Cikin jallabiya ruwan madara ya fito palon….Shuru dan Rashida ma bacci yaci karfinta ta kashe kayan kallo taje ta kwanta…..Daning ya zauna yana kokarin zuba abinci, wai kamar mara mace shike hidima da kanshi illar auran ‘

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button