NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

As ya dinga shawagi a dakin, Yana fad’in”,Ahamdu Ahamdu!! Wannan mutumin shu’umi ne! Ni dama nasan wannan plan din naku ba zai yuwu ba saboda nasan mutumin nan da bin diddigin tsiya, ya iya cin mutunci, kuma jikina na bani ba zai saki Wasila ba dan amsar da yasa ta bani a dazu ta dameni, Hakan ya hawo kawai na yanke shawarar wani abu guda a kanshi, ke kanki kin san irin yanda nake sha’awa da kulafucin kawarki ko? nayi mata hidima da kudina da jikina duk dan ta mallaka min kanta, sai da aski yazo gaban goshi sannan lokaci guda zai ce zai yanke min jin dadi, ba zan yarda ba mutukar a kan ‘Yar gaske ne, zamu zuba ni dashi, mulki kuwa sai dai yaga anayi komai nacin sa.

Camas! tace”Yanzu As wane mataki kake ganin zamu dauka kan guy nan nifa ba zan yarda wannan tozarcin da yayi min ya tashi a banza ba, sai na rama amma kuma hanyar da zan bi na rama ce din ban sani ba, kana gani duk hikima da dubara irin na wasila ta kasa kubta daga tarkonsa.”

Yace.”Idan Yar gaske zata yarda da shawarar dana yanke to duk abun zai zoma na da sauki sosai zamu ci riba biyu a kanshi, yanzu abinda zamuyi shine! mu bari a kwana biyu sai mu sake tun’tubar ita ‘Yar gasken a waya amma maganar zuwa gidanshi ta ‘kare zamu bullo masa ta bayan gida.

Camas! tace”Shikkeen to Yanzu dai ka kaini asibiti tukkuna dan wallahi duk jikina yayi tsami! yau naga tujara da wulakancin da tunda uwata ta haifeni ban gani ba.

As yayi murmushin takaici yace.”Idan wannan mutumin ne to baki gama ganin komai ba a kan halayyarsa…..Key dinshi na mota ya dauka yace.”Tashi muje ki kyale matsiyaci ‘karyarsa ta kusa ‘karewa.” Camas! ta mike tana ya mutse fuska, tabi bayansa suka fita daga dakin.


Sosai Wasila ta kwanta jinya, dan har sai da wannan karon tasha ruwa leda uku, kwana biyu a tsakani duk ta fyad’e! tayi wata rama sai haske da ta’kara sam! bata cin abinci sai yayi da gaske sannan take ci tanayi tana kuka, yanzu kwata kwata ya daina sakar mata fuska, kullum fuskarshi a daure tam! shiyasa daga yace tayi abu ko bata so takeyi sai bayan ya fita sannan ne take cin kukanta ta ‘koshi.

Tana zaune gefan bed dinta sanye da wata riga mai karamin hannu ta dan kamata kadai sai dogon wando na jins a jikinta, daurin da tayiwa gashinta duk ya tuje, dan bata dade da tashi daga bacci ba, saboda yanayin magungunan da take sha ya sanya cikin nata budewa bini bini cin abinci yanzu ma robar yohgt ce a hannunta tana sha tana goge hawaye, wannan masifa ta isheta kullum kana gida a kulle an kulleka, saboda tsabar mutun yana ta’kama da kudi da iko, wannan lamari na mugun bata mata rai, duk tunani da basirar ta ya toshe kan lamarin kawai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido……. yana Sanye da wani farin yadi irin kashimir d’in nan wanda akayi masa dinkin zaman gida (‘Yar shara) idanunsa sakaye da farin glass ya tura kofar dakin ya shiga da sallama a ciki ciki a bakinsa.

Ba tare data d’ago kanta ba itama ta amsa a ciki! Ya karaso gabanta ya tsaya, kamshin turaran sa ya isheta, amma dai bata dago kanta ba sam yanzu bata so ta hada ido dashi tunda dai shi ya kasance azzalimin mutum ne!

‘”Ya jikin naki.”? Yafada yana bin jikinta da kallo mussaman kirjinta, da yaga ya sake wani kumbari dake sam breziyya bata dameta ba sautari haka take saka riga ko vest babu shiyasa in tasaka karama irin me mannewa a jiki sai su sake wani tudu shatin nipples din su fito radau! cikin rigar yanzu ma hakane ya kasance! Yayi saurin kauda kansa, yana dan sauke numfashi, kwana biyu kacal da yayi ba tare da ya ra’bi jikinta yana jin wata irin kasala da damuwa, daurewa kawai yakeyi a kanta, ace lafiyarta lau, babu abinda zai hanashi biyan bukatarshi kawai dai ya bari ne taji kwarin jikinta.

Sai da ya sake wata maganar sannan tace.”Naji sau’ki.”! Ya dan tsirawa karamin bakinta ido yana kallo, kafin yadan shafa sajenshi yace.”Alhmdullahi haka ake so dama Sai ki tashi kije parlor kina da ba’ki.”

Tayi gaggawar dago kanta aikuwa idanunsu ya sar’ke guri guda, tayi saurin sunkuyar da kanga kasa gabanta na faduwa……Yace.”Hajja babbah ce da kanwarta suka zo dubaki dama kuma suna ta sa rana zasu su ganki basu samu dama ba sai yau .” Tayi shiru tana sauraransa, tasan Hajjah babbah a baki amma bata ta’ba ganinta ido da ido ba, sautari wani lokacin gabanta yake kiran ta a waya su gaisa kuma ta lura yana masifar ganin girmanta tunda dai ita tasan ba itace ta haifeshi ba a tarihin rayuwarsa amma ta gane tana da mahimanci a rayuwarsa…….A hankali ta mike tsaye, jikinta sam! babu kwari ta nufi wardrobe domin dauki hijab!! Yabi bayanta da kallo yana lumshe idonsa, yana masifar kaunar hips din ta, kamar itace ta dasa abinta ya zauna ram! kuma ta iya sarrafashi gurin tafiya.

Tana jiyowa yayi gaggawar dauke kanshi, wata irin sha’awa na yunkuro masa anya kuwa yau! ba zai rage wa kansa wahala ba, shifa idan masifar sa ta ciwo shi kawai yayi shine samun kwanciyar hankalinsa.

Gaba yayi tabi shi a baya salau-salau!

Hajjah babba tare da Aunty Kubura da Salimat Suhairat suna zaune a parlo suna hira katon teble din dake gabansu cike da kayan marmari da lemuka masu sanyin gaske!

Salimat kaf hankalinta na kan ‘kofar dakin tun bayan shigar Ahamdu dakin takasa nutsuwa wani irin masifaffan kishi ne ke cin zuciyarta, idanunta sunyi wani irin ja! so takeyi kawai taga macan da tasha gaban mata tayiwa mata zarra! da har ta samu nasarar auran Ahamdu cikin sauki…….. suna fitowa dik suka bisu da kallo Hajjan babba sai washe baki takeyi ita kuwa aunty Kubura kadaran kadahan! take, Suhairat sai l’eka bayan Ahamdu take tana so ta hango Wasila, ya dan kauce kadan yana fad’in”Kuyi hakuri fa Hajjah tana toilet ne shiyasa ba mu fito da wuri ba.” Kafin hajja tace wani abu Suhairat ta mike tsaye da sauri! tana nuna Wasila tace”Ke! ‘Yar Gaske! dama kece matar Yayanmu.”! Wasila ta d’ago kanta da sauri tana kallon Suhairat! sai taga tamkar ta san fuskarta a wani guri…..Kallon junansu suka shiga yi kafin ‘kankanin lokaci naga Wasila tayi wani bala’in shan kunu! tana watsawa Suhairat din kallon banza………….!

Littafin nan na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta kema baki biyani hakkina ba keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[12/08, 7:55 pm] Farida Books: ‘Yr Bngr Sys
42
Salimat ma dake zaune tayi masifar mamakin al’amarin, Wasila yarinyar da tayi ‘kaurin suna a jahar kano yarinyar dake harkar bangar Siyasa da maza! marasa d’abi’a da kamun kai! Yarinyar da duniya da mutanan cikin ta keyi mata kallon banza, Yarinyar da idan taje makaranta bata aikin komai sai shashanci da guje guje da kula kulan maza, Suhairat da Salimat sunyiwa Wasila farin sani a lokacin suna karamar makaranta pramary skull, ta ‘Dandago Lokacin babu wanda bai san Wasila ba a cikin makarantar saboda rashin mutuncin ta da kuma yanda ta raina malamai, sam ba karatu ke kaita ba kayan tallah take tafiya kamarsu alawar madara da gullisuwa kantin gana aya ji’kakkiya da sauransu, haka zata ciko jakarta dasu, daga an futa break ta fito ta baza kayan sana’arta tayi ta cini ki……Ita da Camas! halinsi yazo daya sosai shiyasa suke kawance ita Camas! d’an malale take dafowa ta zubo a karamar kulla itama idan an fita break tayi ta siyarwa, sam! basa gane komai na karatu, ta wani bangaran gwara Wasila kan Camas, Wasila tana iya rubutawa ta karanta, Camas! kuwa ko sunanta bata iya rubutawa, Malamai sun sha korar su daga aji saboda surutu sai su fita suna dariya da murna da fadin dama haka suke so, sai su sami gindin bishiya suyi zamansu suna cin gyada da shewa babu abinda ya damesu su dama suna zuwa makarantar ne domin su kasa su siyar su samu kwabo da dari……Lokacin da headmaster ya gaji da abunda sukeyi a makaranta, dan har sun soma lalatawa wasu dali’ban da d’abi’un su, sai kawai ya koresu daga makarantar yace ko wacce tazo da iyayenta, Rashida ta dinga kuka ganin an kori yayyanta, su kuwa bakin ciki duk ya ishesu suka dinga d’urawa Headmaster din ashar! suna ganin kamar yana musu bakin ciki ne da kudin da suke samu su sam! ba karatu sukaje ba, Uwani tace”Ai kuwa wallahi gobe da kaina zan yafa mayafi naje na samu shugaban makarantaer ai wannan wulakanci ne kawai muna samun abin bukata zai cuce mu, zan fada masa ke marainiya ce ubanki ya mutu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button