NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Tsaki yaja Yace.” Khalifa nayi abu yazo yana damuna kwata kwata yanzu na dawo ina dana sani da auran wannan yarinyar da nayi tsakanin jiya da yau ta zame min masifa da kyar nayi bacci n dare da sassafe muka tashi da masifa abincin kirki ta hanani naci…..Babban abunda ya ‘bata min rai da ita shine na bata waya ta ta kira gidansu, ta kira min wani shege wai ni zata rainawa hankali naji muryar namiji take cewa dani kanwarta ce a take na sumar da ita kasan dai halina in raina ya ‘baci.”!

Khalifa yace.”Subahanallahi! gaskiya Wasila bata kyauta ba! Magana da wani namiji bayan tana da auren wani a kanta……”Za tayi abinda yafi haka ma tunda jahila ce shiyasa na tsaurara matakan tsaro a kanta.” Khalifa yace.”Kaima matakin da ka dauka yayi tsauri gaskiya ya kamata ka zaunar da ita ka fada mata yanda al’amura suka kasance a tsakaninku nasan halinka da isa da jin kai! Dole ta shiga rudani da tashin hankali tunda katsaham! taji labarin auran kome zata iya yi a wannan lokacin.”
“Khalifa yarinyar fa babu irin rarrashin da banyi mata ba ta’kiji saboda tsabar rashin mutunci dazu ni tayiwa Allah ya isa.”! Khalifa yace.”A kan me? Shiru yayi nauyin fada masa abunda yasa yake….Yace.” Dole ne fa kayi hakuri da duk abunda za tayi maka gaskiyar magana kenan kuma kai kanka kasan duk yawancin abokananta maza ne abokan hurd’arta do ka fuskanci wannan matsalar.”

“Khalifa kasan Allah kasan Annabi Ba zan lamunci wannan iskanci ba, Zan iya raunatata nayi mata illah mai muni mutukar naga da aurena a kanta tana mu’amula da wani namijin a waje, shine dalilin da ya sanya ma duka na kwace wayoyinta na cire sim car din ciki na karairaya su….Domin nasan tilas mutsiyatan nan ba zasu rabu da ita ba tunda sun san tana musu amfani, Sam kar kayi tunanin ko sonta nakeyi kawai ina kishin aure na ne banda haka babu abunda ya shafeni da duk wata rayuwa da zata jefa kanta a ciki.”

Khalifa yace.” Kai ma kuma kayi gaskiya nan, Amma dai duk da haka ina mai baka shawarar karka tsawwala mata da yawa ka tausaya mata.” Yace.”Idan ta tausayawa kanta shikkenan idan bata tausayawa kanta ba ita ta jiyo.”

Sosai ya sissiya mata kayan sawa masu tsada da dinki irin na ‘yan burni shaddodi da lesuna sunfi yawa a cikin kayan kwata kwata atamfa hudu ce sai material uku sai dakakkun shaddodi da lesuna wanda aka zuba musu dinkuna masu kyau….Manya manyan ledoji hudu aka cika da kayan….Yaran dake aiki a shagon suka kai kayan mota Ahamdu ya fito da kudi ya biyasu suka fito daga gurin……Sai da ya koma gidan Khalifa ya dauki motarshi kana sukayi sallama da juna ya wuce gida.

Su Uwani da Rashi Da Camas! har magariba suna bakin gate din gidan Ahamdu kamar wasu Mayu sai naci sukewa masu gadi su bude musu sun’ki Daga karshe ma da suka takura musu bulala suka fito da ita sukace idan basu bar gurun ba sai sun zanesu, babu shiri suka bar gurun ransu idan yayi dubu ya ‘baci!

Tun bayan futarsa a dakin take kwance a gurun tana tsiyayar da hawaye sai wata iriyar makyayata takeyi tana zabura sanyi sai ratsa jikinta ya keyi ‘kashushuwan jikinta tana jinsu tamkar ana kwankwasa su da duste takure jikinta tayi guri guda jikinta sai d’ari yake yi yana mazari!!! Kafin kice kwabo ta soma ficewa daga hayyacinta.

Littafin na kudi ne……!
Kika futar min da book Ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema Ke da Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
26
Yana tura kofar dakin ya ganta a kwance inda iya ajiyeta tun safe zuwa wannan lokacin ta riga ta gama fucewa daga hayyacinta domin idanunta sun juye sunyi fari tas ya tsun hannuwanta duk sun tankware sun tsaya cak! babu abinda yake aiki a jikinta a lokacin sai saman idonta dake dan harbawa kadan kadan Numfashi kuwa da kar take jawo shi yana kufcewa…..Da mugun sauri ya dire ledojin dake hannunsa ya nufi inda take, hannu yasa ya tattaro ta jikinsa yana tatta’ba ta, Yayi gaggawar cusa hannunsa cikin rigarta wani mugun zafi yaji a jikinta ya cire hannunsa sauri ya kinkimeta ta mike sambal tamkar Matacciya kan bed ya kwantar da ita, juyawa yayi da azama! sai kuma ya dawo kanta ya tsaya duk ya rude kansa ya juye ya rasa ma wane taimako zai mata….da alama daf take da shekawa barxahu ganin yanda take jin jiki da jawo nufashi da kyar! A gaggauce ya nufi toilet dinshi ya ciko karamar roba da ruwa ya dauki karamin towel ya tsoma a cikin ruwan……Yana zuwa ya cire rigarshi ya janyota jikinsa ya zare mata jallabiyar jikinta, tayi tik da ita tamkar yanda uwarta ta haife, yarda ya kalli sassan jikinta ba dalili baya so wani abu ya darsu a zuciyarsa taimako zaiyi ba wani abu….manne ta yayi a jikinsa suka sauko kasan kafet, ya ware kafafunsa ya sanyata a tsakiyar shi, Ruwan ya shiga tsanowa da towel din yana goga mata a jikinta sa’ko da loko ko ina yake shafa mata yanayi yana korar shaidan tare da kau da kansa daga barin kallon muradan zuciyarsa, Ya jima yana matsa mata ruwa a jikinta ko gezau ba tayi ba, a lokacin yaji wata iriyar nadama ta kamashi yana tsoron kar yarinyar mutane ta mutu a hannunsa, Kwantar da ita yayi ya mike da sauri yaje ya dauko wayarshi…..Kai tsaye numbar dector din sa ya kira yace maza yazo gidanshi akwai mara lafiya Emagency…..Ya dawo inda take yana kallon saman idonta dake motsawa, tsuganawa yayi ya sanya hannu ya dan ta’ba gurin! Yaji ta sauke wata iriyar ajiyar zuciya!! Da sauri ya cire hannunsa ya rike tafin hannunta sai yaji tana motsawa, ya damke hannun cikin nasa yana kiran sunanta a hankali……..Hawaye sirara yaga suna zubowa daga idanunta gasu a rufe….Hamdala yayi ga Allah tabbas tunda yaga hawaye na fita daga idanunta ta dawo….Ya ciccibeta ya dora kan bed ya zauna kusa da ita hannunsa na rike da nata ya tsurawa fuskarta ido…….So yake kawai ta bude ido amma babu hali tsabar ciwon da kanta ke mata ya sanya idanunta sunyi nauyi sam ta kasa budewa jijiyon kanta sun tashi rad’a-rada hatta saman idanunta sai da jijiyo suka bayyana……Karaf! idanunsa suka sauke kan tsayayyun nonowanta da suke kallon rufin dakin….Yayi axamar dauke kansa yana sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya, ji yayi gabanshi na wani irin zillo! yana so ya sake kallonsu yana jin tsoron abunda ka iya zuwa ya dawo, sai ya mike hannunsa ba tare da kalleta ba ya janyo bargo ya rufe mata jikinta still hannunsa na makale da nashi.

Jin saukar bargo a jikinta ya sanya tayi wata iriyar zabura!! Idanunta ta bude suka sauka a kanshi! tayi saurin mayar da idanunta ta rufe tana jin wata iriyar tsanarsa cikin ranta da tana da yanda zatayi a kansa da sai tayi ta kassara shi bashi da imani bashi da tausayi nema yake yaga bayanta a duniya bata da babban makiyi da ya wuce shi…….Jin d’umin hannunaa cikin nata ya sanya ta tattaro ragowar karfin da take dashi ta fizge hannunta…..Ya dan kalleta, ta mayar da idanunta ta rufe hawaye na sake zuba….Mikewa yayi ya fita daga dakin ba….Yana fita dector Nasir ya shigo, suka gaisa kana yace dashi yana zuwa,Dakin ya koma tana kwance amma ta sake takure jikinta…..”Tashi ki dan sa riga Dr zai shigo ya dubaki.” Cikin taushin murya yayi maganar. Tana jinsa tayi masa shiru ya sake maimaita maganarsa nan ma kamar da dutse yake magana, bai sake cewa Uffan ba ya nufi inda ledojin kayanta suke ya dauko wata dakarkariyar shadda wacce akayi wa dingin doguwar riga ya nufe ta da rigar a hannunshi…..Jin tayi ya yaye bargon jikinta, tayi saurin bude idonta, Zabura tayi da mugun sauri! ta fuzge bargon hannunsa tana kare jikinta dashi wata lafiyayyar harara take! watsa masa, bai damu ba ya mika mata rigar a sar’ke yace.”Karbi kisa a jikinki.”! Kin ‘karba tayi tana ji tamkar taje ta shakeshi tabbas ita dai tasan akwai kayan a jikinta jallabiyarsa da ya bata to ya akayi kuma ko dai shine ya cire mata to waye kuwa in bashi ba, sai ta shiga motsa kafafunta taji wai ko yayi mata wani abun, ba taji wani sauyi ba a jikinta ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta tabarshi da tsaye da riga a hannu…..Hawa bed din yayi ya janye bargon tayi azamar mikewa zaune kallon juna sukayi ita dashi Yace.”Bana son taurin kai kar’bi suttura kisa baki da lafiya likita zai shigo ya duba ki.” Fuzgar rigar tayi daga hannunsa ba da son ranta sai dai kawai dan bata son katsalandan din da yake mata sai wani bude mata jiki yake….A gabanshi ta zura rigar tana gyarawa yana taimaka mata, mikewa yayi yaje ya dauki ledar pant cikin kayan da ya siyo mata ya farke ya ciri guda ya mika mata! Karba tayi tana kauda kai, Yace.”Yi azama kisa Yana tsaye yana jiranki.” Kin sawa tayi saboda nauyi yayi tsaye a kanta saboda rashin kwarin jiki sai ta koma ta kwanta tana takure jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button