NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Can bakin gate kuwa, Uwani da Rashida sun gaji da jira Garba nacan cikin ‘Yan uwanshi Rashida taje tace masa dan Allah ya sake gwada kiran wayar tashi ko ya tashi daga baccin….Garba ya fito da wayarshi yana sake traying din numbar tashi……Wayar nata ringing bai d’auka ba dan bayan fitowarsa daga toilet duk ya kunna wayoyin ya ajesu kusa dashi, ya dinga kokarin daukar wayar ya kasa kawai sai ya share wayar yanaji tana ta ringing ‘kararta har tsakar kanshi

Garba Ya kalli Rashida data zuba mishi ido tana kallonsa yace.”Kinga wayar na shiga amma bai dauka ba mybe yana wani uzirin ne bari zuwa anjima sai a sake kira.” Rashida ta koma ta zauna kusa da Uwani jikinsu duk yay sanyi sun gaji da zaman jiran tsammani.

Kimanin rabin awa da kiran wayar tashi Garba ya sake kira……Wannan karon ya d’aga wayar amma sam! garban baya jin abinda yake fad’a! Da kyar dai Garban yaji yana fad’in.”Ko ma su waye ka shaida musu cewar bana jin dad’i gobe su dawo in, Allah y kaimu.” Garba ya kashe wayar yana kallon rashida da jikinta yay bala’in sanyi…..Yace.”Kuyi hakuri bai da lafiya amma yace ku dawo gobe.”Uwani taji kamar ta zundumawa Garba zagi! sai dai ta daure tana jan tsaki ‘kasa-‘kasa tace”Rashida muje.” Gaba sukayi Garba ya bisu da kallo yana tunanin abinda ke faruwa har yanzu su basu san abinda ya faru tsakanin ogan nasu da matar tashi ba.

Sai da suka fita babban titi kana suka tuna da cewar fa basu da ko kwabo dan Wasila tayi tafiyarta da jakarta ‘bacin rai ya sanya dukaninsu basu tunanin hakan ba…..Babur din a dai-dai tasu su tsayar suka nemi alfarmar ya kaisu har kofar gida sai su bashi kudinshi….Mai babur ganin sun matsu yasa ya zuga musu kudi wai dubu daya da dari biyar zasu bayar….Uwani tace”Muje indai zaka kaimu gida zamu baka.” Suka shiga suka zauna shi kuma yaja babur din yayi gaba.

Ya jima yana mur’kukusu da kiran sunan Allah kafin ya samu sassauci a tare dashi ya dan mi’ka hannunshi a hankali ya dauki babbar wayarshi ya kunna! Ma’adanar hotunanshi ya bud’e hannunsa na kyarma ya lalube folder dake dauke da pictures dinsu da sukayi tare……Ya tsirawa fuskarta ido yana wata irin makyarkyata, wayar ya kai kan fuskarshi ya sumbaci dai-dai bakinta tana dariya lokacin da yake musu selpie ranar da zasu rabu!! Hakoranta reras! farare tas dasu, tsantsar kyawunta ya bayyana kanshi……Ya tsirawa kirjinta ido dake mayafin da tasa mai shara shara ne a ranar kuma d’inki mai saukakkiyar kafad’a ne ya dinga kallon brest dinta yana sauke ajiyar xuciya! Ji yake tamkar ya fasa wayar ya fito da ita ta biya mishi bukatarshi yarinya fitinanniya ta mai dashi fitinannan karfi da yaji, mugun da ya sani yake da shigarta rayuwarsa da yana zaune lafiyar Allah tazo ta mai dasho jarababbe mai kulafucun tsiya…….Wayar ya dora a kan kirjinsa ya rintse idanunnusa yana kiran sunan Allah.
A hankali a hankali ya soma jin jijiyar tashi na kwanciya tana risina ya dinga murna sosai yana ajiyar zuciya…..mi’kewar da zaiyi yaji danshi a jikinshi matse matsin cinyarshi to mazi ne ko kuma me gabad’aya, shi dai ya sani! babu cikkaken kuzari a jikinsa yaje ya sake wanka ya fito yana dan jin sassauci a tare dashi.


Wasila na kwance ‘kasan ties taji shigowarsu, sai ta mike zaune tana dan ya mutse fuskarta….Uwani tace”Bani duba daya da dari biyar in sallami mai babur din can! kina sane kika tawo kika barmu ba kudin mota.”

Tace”Uwani duka fa kudin nan saura dubu goma sha biyar ciki zamuyi kudin mota kana abinda yay saura a kudin mu siya musu tsaraba kin san dai ba zamu kwashi jiki muje musu gari hannu rabbana ba.” Uwani tace”Ni dai bani kudi bana son wata magana.” Mikewa tayi taje ta dauko mata ta bata Uwani ta mikawa rashida da fad’in”Kai masa kudinshi ai yayi mana mutuncin ma.” Rashida ta kar’bi kudin da sauri ta fita.

Uwani ta zauna tana zauna kan kujera tana jan tsaki tare da cire mayafinta tace”Banta’ba ganin mara kirki da mutunci irin wannan mutumin nan ba wallahi, Duk wannan xaman da mukayi muna jiranshi ‘karshe cewa yay ba zai fito ba sai dai mu dawo gobe saboda tsabar shi bashi da mutunci.” Wasila ta dan bude idonta tana kallon mahaifiyarta ta ta mayar da idonta ta rufe tace”Sai fa dana fad’a miki kingani dai ai da idonki munyi asarar kudin mota a banxa.” Uwani tace”Aikam gobe sai mun sake komawa dan baza fa mu tafi ba bai san da cewar kina tare da cikinsa ba.

Cikin jin haushi tace”Wai dan Allah Uwani dole sai ya sani ? dik ranar da ya kamata ya sani zai sani ni bana son haka wallahi na fad’a miki wahala kawai zaki sha da asarar kudin mota ba samun ganinshi zakiyi ba dan mugun dan wulakanci ne in bai sa kansa yin abuba babu me sa shi yayi dan haka kawai ki hakura idan kuma kince dole sai kin sake zuwa to ni bani da kudin motar da zan baki.”

Uwani jikinta yay sanyi tace”Ai shikkenan tunda kin’ki cikin a jikinki yake kuma kece kike wahala dashi yau da lafiya gobe babu lafiya, saboda kulafuci kin’ki bari a zubar dashi! kuma kin’ki bari a sanar da meshi ni ina ganin idan an fad’a masa kina da ciki zaiyi wani abu akai dole ne ya bayar da kudin rainon ciki in da zaki masa kinga ai zasu taimaka mana ko.”

”Uwani kyaleshi kawai dan Allah insha Allahu Allah bazai hana ni abinda zanci ba duk ranar dana haihu da kaina zan kai mishi d’anshi amma ba zamu dinga zuwa gidanshi muna zama cikin rana ba sai kace masu neman gafara.”

Uwani tace”Ai shikkenan tunda haka kika ce.” Rashida ta shigo tana fad’in”Wallahi wata masifaffiyar yunwa nakeji sosai bari na dora mana taliya tafi sauri.” Da sauri ta shiga kicin din….Uwani kuma ta mike ta nufi daki tana surutai….Yayin da Wasila ta rufe idanunta tana jin dama Allah bai hallice ba ta Astagafirullah! sautari bawa yakan fad’i wannan kalmar a yayin da ya shiga cikin wani yanayi mara dad’i sai ya dinga ji dama ya mutu ko kuma dama Allah bai halliceshi ba, Wa’iyazubillahi! Ai cikakken mumini baya zama haka kawai ba tare da Allah ya jarrabeshi ba, mutukar kaga a’lamuran ka na tayi dai-dai a duniya to ka binciki kanka, Ubangiji naso ya jarrabi bawanshi shi kuma bawan ya kar’bi jarrabawar hannu biyu tare da ya’ki da tawakkali kan cewar Allah ne yayi masa ba wani ba, Cikar mutum shine yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau! babu kyau dan Allah ya jarrabeka ka dinga jin kamar ko baya sonka ne A’a sone ya jawo haka dan ba kowa yakewa abinda yayi maka ba, idan ka kar’bi kaddara da jarrabawar da yayi maka shi kuma sai yayi maka tagomashi me kyau! Allah kasa mu dace


Bayan sati uku al’amura da dama sun faru ta ‘bangaran Ahamdu da Wasila ko wane bangare babu dad’i bangaran Ahamdu na cikin tsananin takura da masifaffiyar sha’awa dan har jiyya ya kwanta sai da Dr Nasir ya dorashi kan magani tukkuna ya dan samu sa’ida amma dai duk da haka duk daran duniya sai yayi hauka a dakinshi lokaci ‘kankani ya zabge! kullum cikin ‘bacin rai yake har khalifa yaso ya fahimci damuwa a tare dashi amma bai tambayeshi saboda ya soma zargin ko Allah ya soma ta’ba shi shima ai dama ba zai sha ba sai ya fuskanci kalubale tukkuna.

‘Bangaran Wasila kuma Al’amura sun tsanantaa domin wani irin ciwon ciki takeyi sosai da sosai wanda ya sanya ta yanke shawarar zuwa babban asibitin murtala dake cikin gari a duba……Ana ya gobe zasu tafi Pataskum suka shirya ita da Rashida suka nufi asibitin murtala Muhammad da tsakiyar birin kano.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button