NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

As yace.”Kar ki damu Sweetie yanzu Mada! yayi min waya cewar kan idanunshi kuka shiga gurin, yanzu abinda za’ayi shine! Mada da Kwage Lauje da sauran ‘yan uwansu, zasu tare hanyar da kuka bi idan kin samu kin fito daga motar ki tsallaka titi ki bi hanyar ki ta dama zakiga motana a pake kawai sai na daukeki mu wuce.” Murmushi tayi tace”Hakan yayi kyau Ogana naji dad’in hakan insha Allahu muke da nasara a kanshi.” murmushi ya saki cike da samun nasara yace.”Kada ki damu Swetie komai nayi miki banfadi ba.” Tace”Allah ya bar kau…..Jin ana ta’ba motar ya sanya ta zabura! da sauri ta kashe wayar! Ya bude motar ya shigo yana dan kallonta tana rike da wayarshi tayi fi’ki fi’ki! alamun rashin gaskiya, Yace.”Kirana akayi ne.”? Girgiza kanta tayi tana kokarin goge numbar As d’in…..Tace”Ina duba pictures dinmu ne.” Murmushi yayi ya mika mata wata leda mai she’ki da tambarin Dan sulaika jiki yace.” kar’ba.” Da sauri ta sanya hannu ta karba tana duba tamfatsa tamfatsan wayoyi ne guda biyu masu tsadar gaske ko wacce na cikin kwallinta, kwalayen wayar ta shiga budewa, tana murmushi a hankali tace”Nagode.” Baice komai ba ya mi’ka mata wata ‘yar ‘karamar cover layin mtn ne da glo yace.”Gashinan ko wanne nada rigstar akai sai ki sanya ko Allah ya sanya alkairi amma ki sani mutukar naga abinda ba shikkenan ba zan kwace wayoyina kamar yanda na kwace na baya.” Shiru tayi mishi kokarinta ta bude wayar tasa layinkan ya karba ya sa mata, kana ya jona mata guda a charge Tace”Idan tayi ka tura min pictures din.”…..Dan kallonta yayi yace.”Sai mun koma gida Okey.”
‘Kasa tayi da kanta bata so hakaba amma dole ta hakura, motar ya kunna ya tuka suka fita daga gurin.

Can gidanta na Tishama suka nufa, sosai yayi mamakin lamarin, Governor Lawan Rabo mugu ne azzalimi yana kwashe kudin talakawa yana kyauta da bajinta dasu, Yarinya ‘kankanuwa ya dauki Uban gida irin wannan ya mallaka mata Tishima Unguwace ta masu kudi kuma ginaginan dake GRA din manya ne da wuya kaga karamin gida a guraran, Ya silala motar tashi cikin gate din gidan ya samu guri yayi parking kana ya juyo yana kallonta ita kuma sai kokarin bude mota take…..Yace.”Ki daina wahalar da kanki shin kin manta na kulle kofar.”? Shaf ta manta ya kulle zumudi take kawai taga fita.

Yace.”Juyo ki kalleni.” Kallonsa tayi tana dan gyara fuskarta. Babu wasa a fuskarshi da maganarshi Yace.”Shin wannan gidan da kike ciki waye ya mallaka miki shi kuma kina da takardar shaidar mallaka.”? Shiru ta danyi tana kallonshi, itafa bata son neman fitina ina ruwansa da gidanta tunda ba kwabonshi ne ya siya mata ba.” Zai sake magana tayi saurin cewa”Gomnati ce ta mallaka min kuma takardun gidan banki.” Hararata yayi yace.” Ba cewa nayi ki fada min gomnati ce ta mallaka miki gida ba cewa nayi cikin manyan ‘yan siyasan da kike mu’amula dasu waye cikinsu ya siya miki gidan.”? Kai tsaye tace”Mai girma governor ne.” Ya sake watsa mata harara! yana naxarin maganarta dama dai sai shi d’in gaskiya magana gidan zaifi miliyan hamsin, wannan ai haukane da jahilci yanzu zarginsa ya soma tabbata kan governor lawan rabo kwakwalarshi ta lalace shiyasa yake hauka a siyasan ce ya rasa akin yi da dukiyoyin jama’a yazo yana siyan manya manyan gidaje yana ajiye wai shi me wayo idan ya sauka a mulki su zame masa kadara, aikuwa ya dauki alwashin mutukar Allah ya bashi mulki a hannunsa sai ya had’ashi da hukumar Efcc sun binkiceshi duk wasu kud’ad’e da ya sata sai ya fito dasu, idan bai fito dasu ba sai yasha d’auri!

Ya kalleta sai wani ‘kif!kif take da ido irin na marasa Yace.”Wane banki kike amfani dashi.”!? Da sauri ta kalleshi shin wai me yasa yake cin dunduniyar ta ne? me yasa dole sai ya san sirrinta.”? Ganin ya zuba mata ido babu walwala a tare dashi yasa tace.”Union bank ne.” Gyada kanshi yayi yace.”Zamuje tare dake domin kar’bar takardar gidanan sannan ina so nayi bunkice cikin asusunki.”! bata san sanda tace”Kai!!!!!!!! da mamaki tafad’i maganar.

Girarshi guda ya d’aga mata yana sakar mata wani killer smile kafin yace.”Ina so in kubtar dakene! dan bana so kisha wuya a gaba, ina me tabbatar miki da cewar ni Ahmadu mutukar Allah ya bani wannan jagorancin to duk wani ‘barawo! mugu! mazanbaci! macuci! dake fad’in jahar nan sai nasa an kamo min shi na tuhume shi, kan zalincin da yayiwa jama’a cikin wadanda zan d’aure har dake mutukar kikayi min gardama kan abinda na umarce ki, zanyi mulki ne tsakanina da Allah babu sani babu saboda zaki futo da dukanin kud’ad’an da kika ‘barnatar ba tare da bin ‘kaida ba.”! Gabanta ya dinga faduwa tana ta kallonsa lebenta na rawa, wai shin shi wann guy ba zai kyaleta ta sarara bane? ashe tsugune bata kare mata ba koda sun rabu ita dashi zai cigaba da bibiyarta da dukanin abinda takeyi…..Tsoro ne ya kamata lokacin data tuno da cewar har yanzu fa Pose dinta na hannunsa kuma muhiman abubuwanta na ciki ciki kuwa har Atm dinta, amma kuma dole tayi gaggawar zuwa banki domin ta rufe dik wata kafa da zata tona mata asirinta gurin shi……Ganin duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita ne yasa yace.”Kije ku gaisa ina nan ki fito mu koma gida.” Sai abun yazo mata biyu! lallaima wato shi da yana nufin ta shiga su gaisa yanzu ta fito su koma gida, Wallahi ba zai yuwuba! Kuka tasa kariris! ‘bakin ciki biyu ya had’e mata, Tace”Ni wallahi bazan koma ba sai dare! kwana nawa rabona da mahaifiyata da ‘yar uwata sannan kuma kace na fito yanzu.” Ta dinga kuka tana shashsheka! Zuba mata idonsa yayi yana kallo, to meye abin kuka anan kuma? Kawai tace yay hakuri sai dare yazo ya dauketa sai ta hau kuka mtsss! sangarta da shagwaba na damunta…….”Ya isa.” Yafada cikin sanyin murya….Shiru tayi tana kallonshi, Ya ciro hankicinshi mai kamshi ya shiga goge mata fuska, yace.”Shikkenan na bari sai dare okey karfe! bakwai ko shirya ana idar da sallahr isha’i zan shigo mu tafi.” Daga kai tayi! Yace.”Ki gaishe min da momyn tamu.” Kallonsa tayi Wai Uwani yake kira da momynsa, ai ita gani take ma ya girmeta ko kunya wai momyn tamu! Tace”To.” Za taji.” Bude mata motar yayi yace.”Shikkenan.”? Daga kai tayi tayi gaggawar ficewa.” Kawai sai taga Uwani da Rashida a tsaitsaye idanunsu kan motar ashe tun bayan shigowar motar tasu cikin gidan sukayo waje suka tsaitsaya suna jiran ta fito…..Shima da ya juya motar ya gansu sai dai su ba zasu ganshi ba kasancewar motar mai duhun gilashi ce (tintac) baiyi tsammanin da Uwani a cikinsu ba dan ya dauka ko ‘kawayenta ko dai wasu daban! Saboda idan ka kalli Uwani a yanzu ko kusa ko alama ba zakace itace ta haifi su Wasila ba, saboda Allah yayi mata kyawun jiki sosai dan kusan ita Wasilan ta gado, zaka fi tunanin ko yayarsu ce ita….. da gudu taje suka rungume juna suna murna kana suka wuce cikin gidan cike da farin ciki haduwa da junansu.

Uwani sai kallon ‘yar tata takeyi bayan shigarsu palon suka zazzauna kan kujera Wasila ta gaisheta tana tambayarsu bayan rabuwa, Rashida kuwa kallonta takeyi sosai tana mamakin yanda ta kara cika da kwarjini ta kara haske fatarta tayi luwai, abin sha’awa, ashe ba ita kadai ba har ita Uwanin mamakin sauyawar yar tata take cikin sati biyu kacal wasila ta zama wata hamsha’kiya komai na jikinta abin kallone hutu da jin dadi ya bayyana a tare da ita……….Uwani tace”Bayan rabuwa sai alkairi Wasila munanan kewa da damuwa sun dame mu amma ke kina can hankalinki a kwance kin hada ‘kiba abinki ijin dai ba ciki kika bari kika dauka ba dan ni na soma zargin wannan sauyawar da kikayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button