NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ya aje hular dake hannunshi a gefe yana fuskantar mai allon sosai, Yace.”Shine babban damuwar dama, akwai kuruciya da rashin sanin ciwon kai a tare da ita shiyasa take aikata komai yanzu daba dan Allah ya takaita ba da mummunar faduwa za tayi.” Mai allo yace.”Allah dai ya kikeye.” Mikewa yay hannunshi rike da rubutun ya nufi dakin……Binsa yay da kallo yana ji kamar yabi bayanshi sai dai kallon da Hajjah tayi mishi a d’azu yake tunawa.

Mai allo ya tsaya bakin ‘kofar dakin yana mikawa Bitan rubutun hannunshi da fad’in “Bata tasha kana kuma ki shafe mata jikinta dashi, za taji sassauci rashin jin magana ne irin na mutan yau, takalma zan daukesu yanzu in fita dasu idan ya kasance ta shiga bandakin babu takalmi sai ta shiga haka ai lalurace tunda shi takalmin na baraxana da lafiyarta” Hajjah babah tace”Kwarai kuwa malam ka kwashe takalman a fita dasu tunda suna neman cutar da ita kuma mutukar tana ganinsu to ba zata daina sakawa ba.”

Mai allo ya sunkuya bakin kofar ya kwashe sabbin takalman ‘yan madina ya samu leda ya zuba a ciki ya daure ya rataye jikin wata kusa dake bangon gidan yana fad’in “Anjima idan zan fita zan fita dasu in bawa yara sayi amfani dashi.”

Yana zaune yana kallon mai allon duk ya rasa abinda ke damunshi hankalinshi na cikin dakin burinshi ya sake tozali da ita da cikin jikinta, jikinsa ne yay sanyi ganin babu wata sakewa irin tada a tare da mai allon yasan dai sun gaisa cikin girma da mutunci amma duk wannan rawar jikin da mai allon keyi masa ya daina magana ma ba sosai sukeyi ba……Hajjah babbah da Bitan suka fito daga dakin, Hajja na fad’in “Ciki fari dama ai kyaga wauta iri iri Allah dai ya rabasu lafiya.” Duk suka amsa da ” ameen.” Har dashi gogan da yabi ya zubawa hajja ido yana so yayi magana sai dai yayi shiru ya sunkuyar da kanshi ‘kasa, tunda khalifa baya gurin to yanzu hajja itace garkuwa a gurinshi amma shi kanshi yanzu ya gane ya tafka babban kuskure sosai mugun kunyar mai allon ne ma ya rufeshi yanzu da wane ido xai kalleshi yayi mishi bayani dangane da abinda yake tafe dashi.

Hajjah ta gyara zamanta a nutse tace”Malam gurinka nazo domin magana mai muhimanci nake tafe da ita.” mai allo ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace.”Hajiya ina sauraranki.” Hajja tace”Malam da farko dai ina me baka hakuri a bisa abinda ya faru, nasan dole rayukan ku su ‘baci saboda duk mutumin da akece an saki d’anshi dole ne ranshi ya ‘baci mussaman idan anyi bunkice an duba anga babu ‘kwakkwaran dalilin da ya sanya aka aikata sakin kamar dai yanda al’amarin nan faru, yarinyar nan wasila an saketa ba tare da wani dalili me karfi ba, tabbas an shiga hakkinta mutuka!! kuma irin wannan sakin shine ubangji baya so…..To amma nasan dai kai mai ilimi ne kuma kasan kaddara dai- dai gwargwado kasan cewar duk abinda Allah ya kaddara sai ya faru a kan bawanshi to sai ya faru, saboda haka ina so dukaninmu mu dauki wannan abun a matsayin kaddara wacce ta riga fata……Kuma hakika naji dad’i sosai da ya kasance cewa sakin an aikata irin wanda musulunci yake so, akwai sauran dama a halin yanzu, dan haka muke ro’ko ayi hakuri yarinyar nan ta koma d’akinta.”

Mai allo ya sauke ajiyar zuciya mai ‘karfi! yana kallon matar…..Hakika matar nada mutunci da kima da kuma sanin ya kamata ko ga yanayin kalamanta, baya jin zai iya wani ja’inja kan maganarta mutukar shi Ahmadu da yarjewarsa take masa bikon matarshi, zai amince da maganarta, sam baya so a zo ayi abu irin na baya ma’ana a koma gidan jiya, Ahamdu ne me aure ba Hajjah ba kuma shi ake so ya furta da bakinshi kan cewar ni wane na janye sakin da nayi wa mata wance na mayar da ita dakinta yanzu tana matsayin matata kamar yanda addinin musulunci ya tanada, to mutukar yaji wad’annan kalmomi daga bakinshi, bashi da tace addini ya riga ya halasta masa matarshi tunda dama ba tayi iddah ba.” Yace.”To masha Allah Hajiya, ai dukanin abinda kikaga ya faru dama da sanin Allah duniya babu wanda ya isa ya tsarawa kanshi rayuwa face wacce Allah ya tsara masa, auran Ahamdu da Wasila ya ‘kare a lokacin da Allah yake so, kuma a sanda yake so zai iya sanyawa su koma su cigaba da zama mutukar rabo bai ‘kare a tsakaninsu ba, Ni bani da tacewa anan gurin hakanan itama yarinya bata da magana, tunda a yanzu addinin musulunci ya bashi dama a hannunshi, zai iya yankewa kanshi hukunci, ina nufin ya d’auki aniya a zuciyarshi kancewa ya mayar da matarshi ko kuma akasin hakan duk wannan damar yanzu a hannunsa take, Yanzu ni shi nake jira ya furta min da bakinshi cewar ya amince yarinyar nan ta cigaba da zama matarshi ko A’a.”? Mai allo ya ‘kare maganarshi hankalinshi a kwance.

Hajjah babba tace”Eh gaskiya ne malam maganar ka na kan hanya a yanxu magana na bakinsa dani da kai duka ‘yan fatan alkairi ne domin dukaninmu ba zamu haramanta abinda ya halasta ba saboda haka magana yanzu tana gurunka kai muke sauraro.” Hajja ta’kare maganarta tana me zuba masa idanunta………A nutse ya d’ago kanshi zaiyi magana kenan, Ta fito daga dakinsu, sai duk suka zuba mata ido har ta tattako a hankali ta ‘karaso inda suke zaune! gaban mai allo ta dur’kusa tana hawaye da rike masa hannuwa tace”Kawu kaine fa kace ba zaka sake takurani ba! Kawu ashe ka manta al’kawarin da kayi min ranar da muka zo garinan kace ba zaka sake yi min tilas ba, zaka barni da kaina na za’bi miji wanda yayi dai-dai da rayuwata na aura.” Da sauri! ya d’ago kanshi yana kallonta jin abinda take fad’a! da cikinsa za take tunanin yin aure? Kafin ya gama tunani ya juyo muryarta na shashshe’ka tana fad’in “Kawu ni daina bana son na koma gidanshi, sabida ba zan iya rayuwar da nayi dashi a baya ba, Zargina yakeyi Kawu nasan kasan aure da zargi a musulunci ya haramta ni kawai a kyaleni na haifu lafiya sai a bashi d’anshi.” Cikin kuka da yanayi na damuwa take maganar gashi ta ruk’e hannun Kawunta katamau!

Dukaninsu suka bita da kallo mussaman gogon da duk jikinsa yayi sanyi ya dinga kallonta yana hango tsabagen ‘kiyaysrshi a cikin kwayar idanunta……Sai yaji wani irin ba’kin ciki da takaici ya turnu’keshi! wato har wani kuka take tana nadama da fad’in ba zata koma gidanshi ba, to me yake mata da za tace ba zata koma gidanshi ta cigaba da yin rayuwar da tayi a baya ba? shin tun da suke yaushe yayi zarginta? shine zai fad’awa kowa cewa ita d’in kamila ce kuma nitsatstsiya tunda ta kawo mishi burducinta! bai ta’ba zarginta ba sai sanda wannan al’amarin ya faru!!!! ‘Kwafa yay cikin ranshi, ai magana a hannunshi take ba’a hannun wani ba, malam mai allo na shirin yayi magana, Ya rigashi da gyaran murya kafin yace.”Ai maganar saki tuntuni na janyeta malam yarinyar yanzu haka a matsayin matata take, wannan dalilin ne ma ya sanya ni dauko Hajja domin tazo ta baka hakuri a bisa abinda ya faru tsautsayi ne da kaddara amma insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba.” Mai allo ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace.”To madallah Alhaji naji dad’in wannan kalmar taka kuma Wasila zata koma gidanka insha Allahu amma ina so in baka shawara ko kuma in tunasar dakai duk da cewar ka sani, Allah da kanshi ya hallata saki amma kuma baya so a akaita shi, kayi kuskure a lokacin daka yanke hukunci, bance yarinyar ba tayi maka laifi ba tabbas tayi laifi wanda ya dace ka dauki ko wane irin mataki a kanta, amma banda saki, ni a ganina ba tayi abinda za’a saketa ba, saboda ita mace komai girmanta da shekarunta abar tausayi ce ballanta yarinya ‘karama irin wannan!? Ka saketa tana da ciki, abinda ba’aso sannan ta amshi laifinta ta nemi afuwarka ka koreta daga gidanka, bazan ‘boye maka Alhaji yarinyar nan ta wuya da wannan cikin na jiki kafin su zo nan kenan, sai bayan zuwansu, dana tsananta gurin yi mata tofi da rubutu sannan ta samu lafiya har kazo ka ganta haka, ina fad’a maka da can kwanakin baya kazo da sai ka tausaya mata mutuka dan abincin kirki bata iyaci sai yame yame irin nasu, to Alhamdullhi yanzu lafiya ta samu tana iya cin komai ta zauna lafiya, saboda haka nake baka shawara da kuma tunasarwa kan cewar duk wani abu da matarka za tayi maka na kuskure to ka dinga sanya hankali da nutsuwa kafin ka yanke hukunci akai dan saurin saki bashi ne hukunci ba, wallahi Alhaji da kazo bayan yarinyar nan ta haihu to banga dalilin da zai sanya in tilas ta mata cewar sai ta cigaba da zama da kai ba, zan dai baka dama ka shiga cikin zawarawanta idan har kana da muradin hakan.”
Ya dinga kallon mai allo cike da d’umbin mamaki! wato shine ma zaibi layin zawarawa sai kace wani shashasha! tsaki yaja cikin ranshi mai allo bai ta’ba ‘bata masa rai ba irin yau! amma sai ya shanye ya dake! ya hakura tunda dai magana ta’kare ai shikkenan……..A nutse yace.”Arrama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa dukanin abinda ka fad’a gaskiya ne tsautsayi da ‘kaddara basa wuce kan kowa, saboda haka insha Allahu magana ta wuce a gurina zan rike yarinyar nan tsakani da Allah da manzonsa, Saboda haka yanzu sai su shirya kayansu ita da ‘yar uwar tata mu tafi in yaso sai ta dinga d’an d’ebe mata kewa har Allah ya sauketa lafiya”……………Da jin maganar dake fitowa daga bakinshi yasa ta mike da sauri ta shige d’akinsu tana wani irin kuka mai cin rai!!? Ta sanya hannuwanta duka ta dunga dukan katifar dake shimfid’e a tsakar d’akin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button