NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Hajja tace”Subahanallahi Wasila daina irin wad’an nan maganganun sam basu dace ba, kiyi hakuri kinji ko ansan ba’a kyauta miki ba amma komai a sannu ake binsa dama ni tuntuni na fuskanci matsala a tartare daku dama kuma naso in zauna daku din gobe idan Allah ya kaimu kiyi hakuri kinji ko duk da kince anyi miki laifi amma ina so kiyi hakuri dan duk wacce kika gani a gidan mijinta hakuri takeyi, maganar saki ki daina yi tunda har Allah yasa kun fara haihuwa ke dashi ai babu maganar rabuwa shi kuma aure lokaci gareshi idan Allah ya ‘kaddara mijinki zai ‘kara wani auran babu wanda ya isa ya hanashi abinda kikeyi bai dace ba kin san bashi da lafiya amma a maimakon ki kwantar masa da hankali sai kuma tashin hankali haba Wasila.” Hajja ta kare maganarta cikin damuwa da kuma tausasa harshe.

Wani irin bala’in shaushin matar ya turnu’keta! hakan da tayi yana nuna mata cewar tana goyan bayansa kenan! A fusace! ta shige dakinta ta bugo kofar dakin da karfi!!!!! Hajja da rashida suka bita da kallo cikin mamaki, dama Amadu shi tuntuni ya shigewarsa dakinshi tsabar takaici bai tsaya ya saurari sharrin da take shirya masa gurin Hajja ba abinda bata sani ba kuwa Hajja ko kad’an bata son abinda zai ‘bata masa rai!

Wannan abinda tayi yay masifar ‘batawa Rashida rai! bata ta’ba yin turrr! da halin ‘yar uwartata ba sai yau, kamar ta fashe da kuka tace” Dan Allah Hajja kiyi hakuri.”! Hajja tayi murmushi a hankali tace”Ai babu komai Rashida Wasila na cikin ‘bacin rai a yanzu komai zata iyayi kishi ne ke damunta.”
Rashida ta girgiza kanta rai a ‘bace! tace”To Hajja kishi hauka ne ni wallahi banji dad’in abinda takeyi ba.”
Hajja tayi hanyar daki tana fad’in” Rashida kenan wani idan kishinsa ya tashi mancewa yake da komai da kowa kada ki damu nayi mata uziri.”

Rashida ta girgiza kanta ta nufi dakin Wasilan…..Zaune ta tarar da ita had’a tagumi! hannu bibbiyu tana zubda hawaye duk ta wani firgice!.

Rashida tace”Yanzu anti Wasila wannan abin da kikayi shine dai-dai? nifa dole na fada miki gaskiya saboda in kika kashe wannan auran ba kanki kawai kika cutar ba har damu! Ashe har kin manta da al’kawarin da kika d’aukawar su Mai allo, shin wai me mutumin nan yake miki? meye bai miki ba na jin dadin rayuwa? ina ruwanki da auransa! ya auri mata dubu mana kin san dai ba zaki ta’ba hana abinda Allah ya halasta ba, to duk wannan tashin hankalin da damuwa

r da kikeyi na banza ne wallahi, wai har Hajja zaki zum’burawa baki ki buga mata kofa kawai saboda tana fad’a miki gaskiya meye laifinta dan tace ki bawa mijinki hakuri tana jin tsoro kada ki kwana cikin fushin Ubangiji duk macan da take furta kalmar saki ga mijinta Allah na fushi da ita! ni wallahi anti Wasila wani lokacin idan kina wani abun har mamaki kike bani.”
Murya na rawa rashida ta karashe maganar.

Maganganun ne suka sanya ta dawo hayyacinta nutsuwa ta shigeta sai ta dinga tunanin abubuwan da suka faru ita dashi a baya, gabanta ya buga da mugun karfi! kada fa yayi zuciya ya kara sakina irin na baya! abinda ta ayyana kenan cikin ranta….. Ta goge hawayen fuskarta tana kallon babynta dake bacci, Rashin kunyar da tayi masa ta tuna, jikina yay sanyi duk taji tsoro ya shigeta tasan halinshi baya barin takwana idan anyi misho sai ya rama kuma ta lura ranshi ya baci sosai, tsoranta Allah tsoranta Annabi kada ya saketa da jego! gashi ta daukarwa su Mai allo alkawarin zama dashi har abada.
Ta kalli rashida jiki duk a sanyaye tace”Rashida Wallahi raina ne ya ‘baci shiyasa kuma nasan ko ke akewa irin haka ba zakiji dad’i ba, amma nima nagane ban kyautaba.”
Rashida tace”Nifa a ganina duk wannan abinda ke faruwa tsakaninku rashin bashi kulawa ne da tun farko da ya nemi agajinki kina agaza masa kina rarrashinsa da lallabashi da biya masa bukatunsa to da duk haka bata faru ba, wallahi laifin ba na kowa bane naki ne.”!
Murya na rawa tace”Rashida kema laifina kike gani ko.”? Rashida tace” Wallahi laifinki ne kan me yasa ba zaki kwantarwa da mijinki hankali ba tunda dai kin san baida hakuri ta wannan ‘bangaran.”
Hawaye ta goge murya na rawa tace”Kina so na mi’ka masa jikinta ya lalatani.”
Rashida tace”Nifa ba haka nace ba, kiyi masa dabaru ma ki biya masa bukata, kuma ni banga wani abu ba banda kin sanyawa ranki kinje asibiti an tabbatar miki da cewar gurin nan ya warke to kuma zaman me kikeyi ki bawa me hakki hakkinsa kawai kin tsaya wani abu wallahi kece mai babban laifi.”
Wasila tayi shuru tana sauraran ‘kanwartata, tace”Naji shikkenan jeki dan Allah ni nagaji da wannan maganar na hakura idan na mika masa jikina ya fatattakani ya watsar dani shikkenan tunda haka kuke bukata.” Rashida ta juya ta fita daga dakin ranta a ‘bace!

Wasila ta jima zaune tana sa’ke-sa’ke yanda za’ayi ta gyara kwa’bar da tayi dan jikinta yay bala’in mutuwa sosai tana jin tsoro kada gari ya waye ya shigo mata da takardar saki irin na farko……..Jikinta a sanyaye ta dauki babynta ta nufi dakin nashi……A hankali ta tura kofar dakin ta shiga ta mai da kofa ta rufe, da haske kadan a dakin shima na karamar wayarshi ne ya kunna.
Yana kwance cikin bargo zazzabin gaske ne ya rufeshi a d’azu dai zazzabi ‘karya ya ‘kir’kirarwa kansa amma yanzu tsabar tension d’in Wasila ya zuba masa zazzabi me zafin gaske.

Jin zamanta kusa dashi ya sanya ya bude idanunsa da sukayi masa bala’in nauyi sunyi jawur yana haska fuskarta da hasken wayarshi
Marairaice fuska takeyi tana kalato hawaye…..Ya ‘bara rai mutuka yace”Tashi ki fitar min a d’aki.”
Hannunsa ta ri’ke murya na rawa jiki na rawa tace”Kayi hakuri.”!!!!! Ya janye hannunsa yace.”Kin shigo nan ma ki zageni ke ga mara kunya ko.”? Girgiza kanta tayi tace”Ba haka bane wallahi nayi kuskure raina ne ya ‘baci! dan Allah kayi hakuri bazan sake ba.”
Yace.” Zaki hanani aure ne.”? Shuru tayi gabanta na fad’uwa.
Ya sake maimaita magabarshi, girgiza kanta tayi alamun a’a hawaye na sauka a kumatunta, yace.”To cewa nayi ki d’aga waya ta ko kuma cewa nayi ki kashe.”?
“Cewa kayi na kashe.” Yace.” To me yasa kika d’aga min waya.”? ”Babu komai.” tafada tana dan matse hannunta da nashi dake game! Yace.”Zeey ba sa’arki bace ta girmeki nesa ba kusa ba kuma da zan aureta da tun kafin na aureki na aureta bana son rashin arziki da rashin mutunci wallahi duk sanda wani ko wata ya sake kirana a waya kika d’auka kika zageshi sai na sa’ba miki kuma idan kikayi wasa sai nayi aure domin nagaji da wannan rashin hankalin naki.”
Hannunsa ta rungume a kirjinta tana shashshe’kar kuka tace”Dan Allah kayi hakuri na daina kada kayi min kishiya

Allah bazan iya had’aka da ko wace mace ba ina sonka ina kishinka duk sanda naga kuna waya da Zeey ji nake kamar na mutu saboda bakin ciki da takaici.”
Yace.”Kina yi min irin wannan d’abi’un zan zauna dake ke kad’ai ki sanja hali idan kina bukatar hakan.” Tana sake matsowa jikinsa sosai tace”Na daina wallahi Yanzu kome kake bukata zanyi maka dama dan dai na haihu ne amma yanzu idan ka shirya nima a shirye nake………Ya watsa mata wani irin kallo yace.”Ban shirya ba tukkuna kije ki huta ba yanzu ba.” Sai ta sake rungume hannunsa sosai a kirjinta tana marairace masa fuska…….

Namiji tamkar yaro ‘karami yake duk ta inda kika tafiyar dashi zai tafi kuma ba zaki sha wuya dashi ba Namiji ba’ayi masa kutse! ba’ayi masa dole ba’a nuna masa iko idan kikace zakiyiwa mijinki wad’annan da’bi’un zakiyi masifar shan wahala………Wasila itace babbar mai laifi dangane da wannan rikicin da sukeyi Team din Wasila Afuwa Amadu nada masifar sau’kin kai kuma yana son Wasila ni banga laifinsa ba idan ma yana da laifi bai ka nata ba, yanzu gashi lokaci ‘kankani ta shawo kansa duk da rashin mutuncin da take masa amma tasirin son da yake mata ya hanashi daukar mataki a kanta ko yayi niyya ma baya iyawa saboda yana sonta dan haka Wasila kiyi kokarin ganin kin rike mijinki da kyau idan ba haka ba na kawo mishi santaleliyar mace wacce tafi ki komai da komai da kike ta’kama dashi????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button