YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Rashida kwanciya tayi kan kujera jikinta duk a sanyaye ita kuma Wasila cikin dakinta ta shiga tana goge hawaye, wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya jikinta sosai tayi kwalliya cikin wani irin boyal me ruwan zuma d’inki irin buba akayi masa da wani uban sirfani a wuyan rigar da yaji stons sai sheki takeyi tayi amfani da gold dinta na fitar sunan Zahra ado taci tamkar wata amarya ta baza turarruka masu kamshi a jikinta, ta shirya Zahra suka fito palo, Rashida ta dinga kwarzanta kyawun da tayi tana fad’in kamata yay kafin kowa ya fara ganin kwalliyar nan Abban Zahra ne zai fara gani.
Wasila ta wani d’ora ka’fa daya kan d’aya Rashida na daukarta a hoto da wayarta.
Sai da sukayi pictures sama da ashirin wasu ita kadai wasu ita da Rashidan da baby zahra wani kuma ita da babynta sunyi kyau har sun gaji.
Har wajen karfe hud’u da rabi na yamma bai dawo ba, tun bayan da ya tafi kai Hajja gida, kwalliyar da tayi duk ta tsufa! bayan ta idar da sal
lah ta yanke shawarar kiransa a waya.
Suna tare da Khalifa a guest house dinsa kiran wayarta ya shigo ba kasafai yake son amsa mata waya a ko’ina saboda tsaro dan ba Khalifan ne kawai a gurun ba su kusan hudu ne, sai kawai ya kashe wayar,
Ranta taji ya ‘baci jikinta yay sanyi tace”Kodai bai hakura bane? Whsap ta shiga dama numbarshi ce kadai da ita, tana dubashi sai ganshi a online! abinda bata sani ba shine Amadu datar sa sai tayi kwana da kwanaki a bude saboda ba sosai yake shiga whasap din ba ko ya shiga baya dadewa yake sauka, sai kawai ta shiga tuttura masa pictures dinsu ita da baby zahra tana gama turawa ta kashe datar ta mike ta fita daga dakin.
Kicin ta nufa ta dauko had’inta na ni’ima cikin fridge ta zauna tana sha sai da tasha sosai ta mayar ta tsiyayi ruwan kaninfarin ta daya tsumu! har wani ja yayi tasha tana rinste ido saboda yaji da gafinsa da ya game mata baki, cup din ta ajiye ta fita daga kicin din.
Ya d’an dauki wayar yana duba lokaci kawai yaga sa’kkoni na shigo masa ta whasap kuma da numbar ta, da sauri ya shiga yana dubawa, Pictures din yake kallon yana sakin murmushi gabakid’aya hankalinsa nakan hotonan wanda sukayi masifar kyau da dauke masa hankali…….Khalifa yace.”Wai me kake dubawa cikin waya ne sai murmushi kake.”? Alhaji Nura yace.”Da’alama dai bazawararsa ce tayi masa text mai daukar hankali.”
Kashe wayar yay yana kallonsu da murmushi a fuskarsa yace.”Ni zan koma gida dama kai Khalifa nace maka bana jin dadi dan jiya da zazzabi na yini na kwana, komai za’ayi ayi idan da yuwuwar A bawa Alhaji Munzali rance kud’in nan a bashi amma dai a tabbatar da cewar akwai shaidu sannan kuma kowa ya sanya hannu.” Khalifa yace.”Kafin ka tafi sai kasa hannu tunda kaina zaka bada kudin in yaso sai musa namu daga baya.”
A gaggauce ya ‘karbi takardar ya saka hannu ya mika masa yana gyara babbar rigarsa ya mikawa Alhaji Nura Hannu yana fad’in “Alhaji Saduwar alkairi.” Alhaji Nura yace.”Mutumina da alama dai madam ce tayi kira irin wannan sauri haka.”
Khalifa na sane yace.”Kasan yarinya ‘karama ya aura shiyasa yake wannan rawar jikin.” Alhaji Nura yasa dariya yana fad’in “Nima daf nake da na auri ‘yar ‘kankanuwar yarinya domun in more yanda ya kamata.”
Gabad’aya dariya suka saka, suna mi’kewa tare da yin musabaha ga junansu, suka sauka da bene kowanne yana baza babbar riga Garba yay gaggawar bude masa mota ya shiga ya zauna yana dagawa Khalifa hannu wanda shima ya shiga motarshi tare da direbansa,
Kusan tare motocin suka fita daga gurin kafin ko wace mota ta dauki hanyarta.
Cikin ‘kananun kaya ta shirya jikinta ta matse sosai ta saki dogon gashinta ya kwanta a bayanta le’bunanta sun sha jan janbaki tayi kyau sosai
Cike da wasa Rashida tace”Lallai yau anti Wasila amarci ake ci bari na koma daki kafin Abban Zahra ya shigo naji kunya.” Wasila ta harareta tana kai mata duka, rashida ta kauce tana ‘yar dariya tace”Ni wallahi wannan soyyayar taku mamaki take bani ayi fad’a a shirya humm! Murmushi tayi tace”Baby zahra a gurinki zata kwana yau tunda kin daure min gindi na mi’ka kaina gurin dadynta yau zamu kwana muna abu daya.”
Rashida tasa hannunta ta rufe bakinta tana dariya cike da kunyar yayar tata tace”A’a anti Wasila ni ban daure miki gindi ba dan Allah ki sassautawa Abban baby kada ya zauce! baby zahra kuma na amince zan rike miki ita har gari ya waye amma dan Allah ki sasaautawa abbanta.” Wasila tasa dariya tace”Shi zaki fad’awa kice ya sassauta min amma bani ba.” Rashida ta dinga dariya tana fad’in “Anti Wasila shifa salihi ne ke kam ai babu sauki! Allah ma yasa Zahra ta samu k’ani.”
Wasila ta kai mata duka tana ‘bata rai tace”Ciki yanzu Allah ya kiyaye min rashida har yanzu ban manta wuyar dana shaba.”
Tana rufe bakinta ya shigo palon, idanunsu suka sarke guri guda wani irin kallo suke jifan junansu dashi.
Rashida tayi masa barka da zuwa ya amsa yana me kauda idonsa daga kan Wasila, baby zahra ya kar’ba daga hannunta yana mata wasa.
Cikin wata irin murya tace”Sannu da zuwa.” Ya amsa da “Yawwa.”! yana kokarin shiga dakinshi da baby zahra a hannunsa……Mi’kewa tay tabi bayanshi tana wata irin t
afiya sasaan jikinta na wani irin rawa.
Agogon hannunsa yake kokarin cirewa ta ‘karasa da sauri tana karba tana cire masa, ya tsira mata ido bako kiftawa, murmushi tayi tace” Dazu nayi ta kiran wayarka baka dauka ba.” Anutse yace.”Ina tare da jama’a ne duk sanda kika kira waya kikaga ban daga ba ina wani uziri ne.
Ta ajiye agogon kan drowar ta fara kokarin cire masa babbar rigar jikinsa, ta ajiye kan bed tana ‘balle masa botiran rigar cikin, ya zauna da dogon wando da singlet a jikinsa,
Tace.”Ko na had’a maka ruwan wanka.”?
Yace.”Bari naci abinci tukkuna.”
Tace.”Tom bari na kawo maka.” Juyawa tayi da niyyar futa daga dakin ya bita da kallo har ta fice ya sauke wawar ajiyar zuciya yana me lumshe idanuwansa.
Da kanta ta bashi abincin yaci ya koshi tana masa hira sosai yake mamakinta, yana adduar Allah yasa zamansu ya dore a haka.
Tun da ya gama cin abincin jikinsa ya mutu murus! bacci bacci wani irin feeling mara dadi ne yake taso masa,
sai kawai yay kwance kan chanis carfet din dake gefan bed din, Ta shigo dakin taga yana kokarin yin bacci, zama tayi kusa dashi kamshin jikinta ya bugeshi, da sauri ya bude idonsa yana kallonta, hannunta ta dora a kirjinsa tace”Ko jikin ne ya dawo kada kayi bacci da yamma Annabi ya hana.” Yaji kamar ya daure sai dai ya kasa! janyota yay ta fad’a saman ‘kirjinsa ya rungumeta ‘kam! yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya.
Littafin na kudi ne…!
Kika futar min da book keda Allah! kika karana baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
BINTA UMAR ABBALE
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
83
Kwanciya tayi saman kirjinsa tana jin yanda yake shashshafa sassan jikinta yana sakar mata wasu zafafan kesses wanda ya sanya a take ita jikinta ya mutu ta langwabe a jikinsa tana so ta biye masa, gashi magariba ta gabato, sun jima a haka har sai da yaji ya dan samu sassauci a tare dashi kana ya cireta daga jikinsa ya mike ya nufi toilet domun daura alwala,
Sai da yayi wanka sannan ya daura alwala ya fito har yanzu tana nan takure a kasan kafet, ya dan kalleta yana nazarinta
ganin ta d’ago kanta sun hada ido ya sanya ya fahimci halin da take ciki, Yace.”Lokacin sallah yayi ko bakyajin kiran sallah ne.”?
A sanyaye tace”Yanzu zan tashi nayi alwala.” bai ce komai ba ya fita daga dakin.
Ta jima zaune tana so ta dawo dai-dai abin ya faskara muguwar sha’awa ce ke damunta. Da kyar taje ta dauro alwala ta fito, ta tada sallah, tana idarwa, ta fita parlo lokacin Rabe har ya shirya musu daining Rashida na daki ita kadai kunyar zama take a palon gudun kada masu gidan suyi abin kunya a gabanta.
Dakin ta shiga ta tarar da ita tana kallo da plate din abinci a gabanta tana ci.
Tace”Rashida yau babu kallo kenan.”?
Rashida tace”Anti Wasila yau nan zan zauna nayi kallona ina kewar Hajja Wallahi da tuni muna tare.
Wasila tace.”Bake kadai ba nima kewarta nake! wallahi matar nada kirki……juyawa tayi da niyyar futa daga dakin Rashida tace”Sai da safe Anti Wasila.”
Tace”Allah ya tashemu lafiya.”
Amadu be shigo gidan ba sai bayan sallahr isha’i, lokacin tayi wanka ta sauya kaya wannan karon ma kananu ne wanda suka matse mata jiki gashi tayi amfani da turarrika masu kamshin gaske duk inda ta gifta kamshi ne ke tashi, Da kyar ya daure ya iya zaman cin abincin, a daddafe suka nufi bedroom ita dashi, duk sun d’okanta da junansu. wata iriyar rayuwa sukayi a ranar wacce ba zasu ta’ba mantawa da ita ba, sun mori kansu da kansu kuma dukaninsu sun biya wa junansu bukata, sukayi wanka tare kamar yanda suka saba kana suka kwanta rungume da junansu.
Koda asuba tayi yaje masjid ya dawo sai da suka sake komawa ruwa basu saurarawa kansu ba sai da gari yay haske sosai san suka sarara sukayi wanka suka shirya tsaf! Wasila ta shirya babynta ya karbeta suka fito palo a tare sai wani kyallin goshi yakeyi….Rashida data gaji da zaman jiran fitowarsu gurin karatu sai kawai ta bar gurin ta koma kan kujera ta zauna tana duba wani littafin addini.
Sai da ya ganta da littafi a hannu sannan ya tuna da karatu, suka gaisa a nutse yace.”Yau bamuyi karatu ba ko.”? dan mirmushi tayi tace”Ai baka jin dad’i.”
Yace.”Lefin yayarki ne da bata tasheni a bacci ba.” Wasila taji karshen maganarsa lokacin ta fito daga daki ta dan harareshi irin na soyyaya tace” Ni babu ruwana wane irin tashi ne ban maka ba mybe maganin daka sha ne ya sanya maka bacci.” Da sauri yace.”Nima nafi tunanin haka.”
Dainnig ta nufa ya bita da kallo cikin sha’awa shi dai ba zai ta’ba gajiya da ita ba a rayuwarsa, Rashida ta kar’be baby zahra dake hannunshi Shi kuma ya wuce dainig domin karyawa
Ko a gurin break din ma sai da sukayi wassanin su iya son ransu sannan sukayi break din cike da farin ciki gami da annushuwa, da kwata kwata baiyi niyyar fita ba yaso ya zauna gida ya yini tare da iyalinsa to dole ne ya fita saboda akwai babban abinda zai sanya ya fita din, harda kuka da zai fita tana ta shagwaba da dire diren kafafu shi kuma sai biye mata yake yi, da kyar dai ta barshi ya fita daga gidan.



