YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wani wawan burki! yaci a gabanta! Tsabar wuya da galabaita ya sanya ta zubewa a gurin tana mai da nuffashi!! Ya bude mota ya fito rai a ‘bace! sai ta yunkura cikin zafin nama zata sake arcewa da azama! ya sanya mata kafarsa guda a tsakanin tata sai tayo kanshi zata fad’a! yayi saurin matsawa ta kirjinta ya daki jikin motar….Ta dago kafadunta tare da juyo da ita ba tare da ‘bata lokaci ba ya kife ta da wani wawan mari! wanda sai da taga gilmawar taurari ta dinga jin dum!! dum!! a kunnenta….Luuuu!! tayi zata sake kifawa a jikinsa ya kauce! ta sake dukan motar a zabure!! ta bude idonta ta dinga ganin zatinsa dishi dishi a cikin idonta…..Kawai sai wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska…..Motar ya bude ya tankad’ata ciki ya mayar da murfin ya rufe kana ya zagaya mazauninsa ya shiga yaja motar,
Su Garba kuwa dama tuni sun juya……….Gate din a bude yake dan haka kawai sai ya shiga da motar duk suna tsaye ciro cirko ya tsai da motar ya tsaya yana musu fada da gargadi kan duk wanda yayi kuskuran sake barin ta ta futa daga gidan to a bakin aikinsa.” Dukaninsu suka shiga bashi hakuri tsabar haushi bai ma tsaya ya sauraresu ba ya fuzgi motar a guje ya wuce.
Yanayin parking ya fito hade da bude kofar da take tana kwance ruf da ciki kan site gashinta ya wargaje yayi buyaya lifayar ma ta cire dan saura kadan ta rabu da jikinta, Tsawa ya buga mata kan ta fito masa daga mota! shiru yayi ya sake kwatsa mata wata tsawar yaji shiru, sai da yayi magana sau biyar ba ta amsa ba, ya zura jikinsa cikin motar ya burkitota fuskarta ya tsirawa ido yana kallo….Idanunta a rufe ruf! dai-dai da gashin idon baya motsi! yaji faduwar gaba kadan ta kamashi Hannunsa ya dora a kirjinta minti biyu ya dauke! da sauri! ya kara hannunsa saitin hancinta nan ma yayi minti biyu babu alamun nuffashi a tare da ita….Babu shiri ya tattaro ta jikinsa ya taraiyaye ta daukar jarirai yayi mata ko motar bai rufe ba ya nufi cikin gidan da ita, hankalinsa a tashe.
TO JAMA’A NAN NA KAWO ‘KARSHEN FREE PEGE NA WANNAN LITTAFIN GA DUK MAI BUKATAR CIGABA DA KARANTAWA SAI YA DUBA BAYANAN DA NAYI A SAMA KAZO KA BIYA KUDINKA KA KARANTA DOMIN KAR AYI BABU KAI WANNAN LABARI DAI YANZU MA AKA FARA AKWAI TAFIYA A GABA WANNAN D’ANDANAN GISHIRI NE……….HAR KULLUM INA FAD’A CEWA KUD’IN KARATU KIKA BIYA BA NA MALLAKA BA IDAN KIN YARDA KIZO KI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI YARDA DA WANNAN TSARIN BA TO DAN ALLAH KAR KIZO KI BIYA KI FUTAR MIN DA BOOK KI RUSA NI KIYI ZAMANKI NAGODE SANNAN DUK MAI BUKATAR KARANTA NOVLS DINA AKWAI COMPLETED KAN FARASHI MAI SAU’KI KAR KU MANTA DAI HAUSAWA NACEWA SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA
‘WADANNAN SUNE LITTAFAN NAWA
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
BABBAN YARO
LADIDI KWADAGA
MASHAHURI
SADAUKI OMAR
RUWAN DARE
NI DA YAYA SADAM
‘YAR BANGAR SIYASA
Kar ku manta da cewar ni Binta Umar Abbale nice mamalakiyar wad’annan novels din…..Saboda haka ga duk wani mai bukatar ya karanta completed dinsu sai ya nemi numbar ta ya biya ya karanta hankali kwance, Ina kara tunasar daku cewar kada kuje ku biya wani ko wata kudin wannan novels din dana jera muku ‘karya yake ‘karya take zasu siyar muku da hakkin da bana su ba kumai ba zama lallai su baku complete ba shikkenan sunci kudinku a banza, hanya mafi sauki anan ita ce ku tuntu’be ta wannan numbars din nawa
08089965176
07084653262
Masha Allah masoya sai naji ku????????♀️
[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr bngr Sys.
21
Kan makeken bed dinshi ya shimfidata a gaggauce ya bude ma dai-dai cin firjin dake gefan bed din ya dauko goran ruwa mai sanyi ya bude murfin ya tsiyaya a hannushi ya soma yarfa ma a fuska, sai da yayi haka sau uku tukkuna ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya numfashinta ya dawo amma kuma idanunta a rufe ruf sai dai gashin idanunta dake motsi…..Tsayuwa yayi a kanta yana me ‘karewa fuskarta kallo, Tunda yake da yarinyar bai ta’ba tsayuwa ya kare mata kallo ba irin yau! tana da masifar kyau! wanda sai ka dade kana kallonta zaka fahimta babu abunda yafi tafiya da hankalinsa irin karamin bakinta mai dan tudun le’be dai-dai sumba, bai san sanda ya tsotsi leb’anshi ba ya dan lumshe idonsa tare da sake budesu a kanta, karaf! suka hada ido lokacin ta bude nata idon yayin saurin dauke kansa yana dan ja baya daga kusa da ita…..Cikinta ta rike da hannuwanta tana rintse ido hawaye ya soma shatata! “Wayyo cikina wayyo cikina! wayyo cikina.”!!!! Abunda take ta fad’a kenan tana matagugu kan bed din……Sai ya tsinci kanshi da kid’imewa ya zauna kusa da ita yana kokarin rike hannunta ta fuzge! da ‘karfi! tana cigaba da murkususu da kiran cikinta…..Hayewa yayi bed din ba tare da ya sani ba ya rirrike ta jikinsa sai kyarma! yake ” Menene! ina ne yake miki ciwo sannu daina kuka ko kin bugu ne.”? Duka ya jero mata wannan tambayar lokaci guda…..Shiru tayi masa ta sane ta dinga kwanciya a jikinsa tana mutsika masa jikinta anashi tana kuka da kiran cikinta……Bai san sanda ya zura hannunsa cikin rigarta ba yana shafa kasan mararta muryarshi sanyi kalau! yake magana “Sannu daina kuka bari na duba miki magani ina kin buga gurin da jikin mota dole yayi miki ciwo mybe ma yunwa kikeji ko.”? Ba tace komai ba sai aukin tureshi da takeyi daga jikinta yana sake rirriketa shi duk a tunaninsa da gaske take cikinta ciwo yake…..Ya mike da sauri yans fad’in” Bari na duba miki magani dare yayi yanzu da na kaiki an duba ki.”’ Yana fita taja tsaki ta mike da azama! taje ta rufe kofar dakin tabar key din a jiki…..Komawa tayi ta kwanta tana sa’ka wacce zata fisheta.
Ya dawo dakin hannunsa rike da maganin ciwon ciki duk ya had’a uban gumi yana jan kofar yaji a kulle gam! gam!! Turus yayi da maganin a hannunsa yana tunani Babu shakka yarinyar nan yaudararsa tayi…..handle din ya sake murdawa yaji a rufe gam! gashi bedroom dinshi ne duk wasu abubuwan bukatunsa na ciki…..Wato tana so yayi mata magiya ta bude kofar shi kuma ya dauki alkawari kan sai dai ta gaji dan karan kanta ta bude tunda ya gane manufarta…..Wani bedroom din ya nufa ranshi a ‘bace! amma yarinyar ta shammace shi gashi wayoyinsa na dakin hade da sauran makullan gidan…..Idanunsa suka sauka kan key din dake jikin kofar dakin da yake ciki….Da sauri ya mike ya isa gurin ya zare key din ya nufi dakin….Koda ya zura key din sai yaki shiga yayi yayi nan ya fahimci tabar key din a jiki. Ya juyo yana girgiza kai agogon bango ya kalla karfe daya na dare har da wani abu yarinyar nan ta hanashi bacci…..Idanunsa ne suka sauka kan pose dinta dake can bakin kofa yayi saurin isa inda take ya dauka tare da zama kan kujera yana budewa…..Wayarta babba da karama ce a ciki sai turaranta da wani zobe na gold a cikin gidanshi sai ‘yan kudinta wanda basu wuce dubu takwas ba zuwa goma….Ya kunna wayar yana dube dube a ciki.
Tana kwance ta ‘kurawa cilling ido tana tunanin yanda za’ayi ta kubutar da kanta daga hannun Ahamdu, ta mike zaune da sauri tana dube dube! sai yanzu ta tuna da pose dinta….Tsaye ta mike lifayar jikinta na hard’e tayi gaggawar cireta ta jefar a gurin babu ruwanta da yanayin kayan dake jikinta ta durfafi kofar futa…..Har ta murda kofar zata futa sai kuma ta fasa tsoro takeji kar ya ritsata ta k sanya kunnanta jikin kofar wai ko za taji alamun motsi taji tsit! a hankali ta murza key din ta ja kofar ta bude…….Yana zaune kasan kafet tsakanin kujeru shine dalilin da ya sanya ba ta ganshi ba sai ta fara dube dube a palon….Ya zuba mata idanunsa yana kallonta tar cikin jan ‘kwan dake palon mai hasken tsiya…..Can yaga ta nufi bakin kofar futa domin anan take tunanin ta yar da Pose din nata….Ya mike a hankali ya iske inda take hannunsa rike da pose din nata….Tana juyowa suka buga karo goshinta ne ya daki kirjinsa……Tayi masifar razana!!! da sauri tayi nufi guduwa ya tare ta tare da matseta a jikin labule…….” ‘Kas tayi da kanta kunya ta isheta sai yanzu ta fahimci a yanda ta fito tama manta shaf da kananun kayane a jikinta.