YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

“Kallonta kawai yake yi ya ma rasa abunda zai ce mata sai bin sasan jikinta yake da kallo yana ayyana abubuwa da dama a kanta.
Pose din dake hannunshi ta zubawa ido….Ya dage mata gira tare da fad’in” Kin bude kofa ne sabida kizo ki dauki jakarki ko.”? Tayi shiru yace.”Kin yaudareni da ciwon ciki kin kulle min daki….Daga taimako sai sharri ya biyo baya kinga dake bani da alhaki a kanki da kanki kin bude kofar wai ke me wayo ko? Okey jakarki gata a hannunta zan baki abarka amma zan dauki abu biyu a ciki.”
Hannu ta kai da sauri zata fuzge! yayi sama da jakar yana kallonta sai d’age! takeyi Yace.”Ki daina wani wahalar da kanki Ba komai zan dauka ba a ciki illah wayoyinki dukaninsu babu ke babu amfani da waya sai kinyi hankali.”
Ido ta zare! hannunta na kyarma sai rirrike hannunsa takeyi tana so ta fuzgo pose din….Dariya ta bashi ganin yand ta dage tana d’age! ‘kafafu Ya d’an ture ta daga jikinsa yana matsawa, Biyo shi tayi muryarta na rawa “Allah sai ka bani waya ta.” Abunda take fada kenan tana rirrike masa riga….Ya ‘bata fuska da fad’in”Idan ba ki daina tatta’ba min jiki ba sai na ‘bata miki ” Wallahi kinji na rantse ke da wayar nan har abadah sai nayi niyya nan gaba na yarda da hankalin ki sannan zan yarda ki rike waya.”
Dajin wannan magana tashi sai ta fashe da kuka” Wallahi ban yarda ba haka kawai zaka takura min ka shiga rayuwa ta kace ba zan rike waya ba, Idan ka cuzguwa rayuwata nima sai na cuzguna maka kuma na fada maka wannan auran dashi da babu duk daya suke a gurina Gwara kawai ka sallame ni naje na cigaba da harkokina.”
Ko kallonta baiyi ba ya cire mata agogonta da turaranta ya ajiye mata kan kujera ya nufu bedroom dinshi yana fadin”Wahala ce bata isheki ba yarinya sai kiyi tayi ke kadai, Ahamdu bashi da lokacin ki.” Yana shiga dakin ya murza key ta tsaya jikin kofar tana bugawa ya share ta kawai ya kwanta bed din shi tare da rufe ido bacci yake ji sosai bayan haka kuma ga gajiya ta dabaibaye shi……Tun yana jin bugun kofarta sama-sama har ya daina ji bacci yaci karfinsa…….Itama da ta gaji da dukan kofar sai ta silale kofar dakin tana kuka da kiran sunan Allah shiru palon tsoro da farga duk ya isheta haka dai tayi kwance bakin kofar dakin ga sanyi Ac yayi yawa a palon tsoro ya hanata taje ta rage, Yanda taga rana haka taga dare domin a kunnanta aka soma kiran assalatu.
Kika futa da book din nan na barki da Allah kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr bngr Sys
22
Yana fitowa da shirin zuwa masalaci yaci tuntube da ita a bakin ‘kofa yayi saurin matsawa yana dan haske ta da wayarshi, ta bude idanunta da suka ci kuka suka ‘koshi ta zuba a kanshi….Wani irin mugun haushinsa da tsanarsa ne ya kamata haka kawai ya daukota ya rufe a gida yana azabtar da ita, Da sauri ta mike tsaye! yayi saurin kaucewa ya bata hanya ya dauka dakin zata shige sai yaga tayi kansa ta cikwokwiye shi tana kuka.” Ka dauke ni ka mayar dani inda ka dauko ni ba zan iya wannan rayuwar ba bana sonka kan me yasa zakaje ka sanya a daura maka aure dani ai wannan zalinci ne, Wallahi gwara na kashe kaina kan in zauna da kai na tsaneka.” kuka take hai’kan! tana sake rike masa riga sai shigewa jikinsa takeyi gashi ya dauro alwala.
Yanda take gunjin kuka ya nuna masa da gaske takeyi abunda take fada har cikin ranta yake……Sai yaji rashin dadin hakan ranshi a bace ya ture ta daga jikinshi ya bar gurin da sauri! ta kuma mikewa a guje ta cimma sa ta baya ta rikeshi tam ta zagaye ‘kugunsa da hannuwanta kirjinta na gogan bayanshi…..A zabure! ya juyo ya hankade ta hade da kifa mata mari! da hannu ya nuna ta “Kika sake kika ‘kara ta’bani sai ranki ya ‘baci! wallahi ba zan sake ki ba za kiyi ta zama a cikin kunci da bacin rai! ke da kin dauka nima sonki ne? Allah ya sawake na fada miki domin na karya alkadarinki yasa na aure ki shashasha kawai.”! Juyawa yayi ya shige dakin….A gurguje ya sake sabuwar alwala yana jan tsaki ko yaya ta ra’bi jikinsa sai yaji sauyi a tare dashi abinda bai taba faruwa ba dashi…..Tana durkushe tsakiyar palon ya fito ko kallonta baiyi ba ya fice! yaji masifar haushin cewar da tayi bata sonsa yanzu ya soma zama da ita duk dan ya kuntatawa rayuwarta.
Can gidan kuwa Uwani da Rashida na ganin sha biyu na dare ta wuce sai suka hakura da jiran ta suka kwanta ba tare da wata damuwa ba saboda sun san dama ta saba irin wannan tafiyar wani sa’in ta kwana wani sa’in kuma ta dawo…….Gashi Rashida ta kira wayarta tana shiga bata dauka ba sai tayi zargin ko tana tare da mutane ne dalili kenan da ya sanya suka kwanta ba tare da sunsa wata fargaba ba a cikin ransu.
Bai jima da futa ba ta mike da azama! ta shiga dakin nasa nan idanunta suka sauka kan wayoyinta dake zube kan bed kusa da inda ya kwanta taga har da babbar wayarshi ma….Da sauri ta dauki babbar wayar ta tana duba contec numbar As take nema…..Sai taga ba kwata kwata babu sim card a wayar tayi saurin budewa wayar tana dubawa wai ko gocewa yayi taga duk babu, hannu na rawa ta dauki karamar ma taga itama ya cire sim card din gashi duka kan wayoyin babu numbar kowa ziro take……..Hankali a tashe ta zube kan gadon tana rike kai! Wannan guy ya kassara ni! Innalilihi wa’ina ilahi raji’un! abunda take iya fada kenan jikinta na kyarma! babbar wayarshi ta kaiwa raruma hannu na rawa ta bud’e duka ta zare sim card din dake ciki ta zura cikin birziyarta rufe wayar tayi ta nemi guri ta zauna kan stoll tana jiran shigowarsa kwata kwata tunaninta ma baya kan ibadah burinta ta kubutar da kanta.
Tananan zaune ya shigo dakin…Kallo guda yayi mata ya ga alamun ba tayi alwala ba ballanta tayi sallah! Ya sha kunu tare da fad’in”Tashi kije kiyi sallah.”! Ba tayi masa musu ba ta mike yabi bayanta da kallo tana muskuta d’uwawu cikin damammen wandonta da sauri ya kauda kai yana fadin”Mara kunyar ‘karya.” Sarai taji shi girgiza kai tayi tace”Wallahi kome za’ayi ba zan bayar da sim card din nan ba nima sai an bani nawa.
Sabon bursh ta bude ta matsa man goge baki a kai ta wanke bakinta tas ta dauro alwala ta fito…..Lifayar ta ta hango can karshen gadonshi ta haura kan bed din yana kwance yayi saurin gyarawa ganin kamar zata fado kansa, ba tare da ta damu ba ta dauko ta nad’a a jikinta ta nemi gefen kafet ta tada sallah! Yana kwance yana kallonta har ta tayar da sallahr.
Hannu ya kai ya dauki wayarshi yana dan dubawa sai yaga babu sim card ya bude wayar yaga babu ajiye ta yayi ya dauki karamar ita ya bude yaga ta cire! Murmushi yayi…….”Ke! waye ya baki izinin daukar min waya kiyi min bunkice.”? Kai tsaye tace”Nima waye yace ka cire min sim card din waya ta ina ruwanka da kaya dukanin sirrina yana waya ta ka duba min ni banyi maka bunkice a waya ba kawai na cire sim card ne sai ka bani nawa sai na baka.”
Mikewa yayi zaune…sai ta zabura! ta matsa gefe da sauri! Hannu ya mika mata “bani Sim card dina tun muna shaida juna dake.”
“Allah sai ka bani nawa zan baka.” Tafada cikin dakewa da jajurcewa.”!
“Nayi bunkice jiya a wayarki naga komai a ciki da irin mutanan da kike mu’amula dasu dalili kenan da ya sanya na cire sim card din, da da yanzu ba daya bane kina da aure yanzu ba kowa ya kamata kiyi mu’amula dasu ba sanna duk mutanan da naga numbarsu a wayarki basu da kirki babu wanda ban sani ba a cikinsu, ga yanayin yanda kika dauki wannan auran da rashin kima kina iya cigaba da mu’amula dasu dalili kenan da ya sanya na zare sim card din wayoyinki……Su kansu wayoyin anjima kadan zan bada kyautarsu ga mabu’kata.” Ya kare maganarshi cike da rashin wasa.