NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Littafin nan na kudi ne! Idan kika futa da book din nan Ke da Allah! Ki ka karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
25

Ransa a ‘bace ya fita ya iske Garba da Hadi a bakin mota suna jiranshi tun kafin ya karaso Garba ya bude masa mota ya shiga kana kallon yanayin yanda ya fito kasan babu wasa, su kansu su Garban sun sha jinin jikinsu, sukan kwana biyu ba suga irin wannan fuskar shanun daga gurun ogan nasu ba, duk ranar da yayi irin wannan ‘bata ran to babu shakka akwai abunda ya faru…..Da wuya kaga fushin Ahamdu dalili kenan da yasa idan anyi masa abu a take yake ramawa saboda shi bashi da ri’ko ko ‘kan’kani ! ko wane irin laifi zakayi masa ba zai gaba da kai amma wannan karon yarinyar nan ta kaishi bango dole ne ya nuna mata fushinsa mugun kishi ne dashi mussaman kan abunshi, idan yana da abu yasan halalinsa ne baya so kowa ya ra’beshi, yayi masifar jin ciwon wannan kalma da As ke kiran yarinyar dashi (my love) idan ya tuna ji yake kamar ya zai shake dan bakin ciki!………Maigadin gidan Khalifa ya bude gate din Hadi ya shiga da mota Khalifa na tsaye harabar gidan dama already Ya kirashi a waya ya sanar dashi gashinan kan hanya, da kanshi ya karasa inda motar take ya bude masa kofa ya fito yanayin yanda ya ganshi a hargitse ya sanya yasha jinin jikinsa babu shakka akwai abunda ke faruwa…..Tare suka jera suna tafiya har zuwa cikin gidan…Ya samu kujerar dake daura da kofar fita ya zaune hade da cire hularsa, Khalifa ya tsaya kanshi tare da fad’in” Akwai damuwa a tare da kai dama tunda naji kace ga nan nasha jinin jikina Allah yasa dai lafiya.” Kafin yace wani abu Hafsa ta fito daga daki taci kwalliya cikin boyal mai ruwan zuma tace”Lallai ango ne a gidan da muna cewa zamu zo gashi har na shirya sai kawai ka kira waya kace kaganan.” Ya dan saki fuska kadan yace.”Zuwana ba zai hanaki zuwa ba tunda kin san gidan sai kiyi tafiyarki.” Tace”Ai amarya bata sanni ba mun bari dai sai ranar da kake gida sai muje Ga Zeey ma tazo yau kwananta biyu har ita muka shirya zamuje muga amarya sai kuma kayi mana bukulu.”

Cikin ‘kosawa yace.”Wai ke dole sao da mijinki zakije gidan ne? nifa bana son gulma irin taku idan yawo ne ya kama watarana ma bakya tambayarsa kike tafiya to tunda kin samu abokiyar tafiya ba sai kuje ba, muma mafi jin dadin sakewa a gidan dan idan kinanan kin dinga zurga zurga kenan kina hanashi fahimtar magana.” Dariya tasa tace” A’a dai gwara muje tare da mijina in yaso sai ka gabatar damu tare a gurinta amma yanzu idan munje nida zeey bamu san abunda zamu ce mata ba tunda ba saninmu tayi ba.”

Khalifa yace.”Ke da Zeey din ai gulma ce zata kaiku ba wani abu ba.” Yar dariya tayi tace “Lallai Abban Afnan Wai gulma ni da nake so ma amaryar ta zama ‘kawata sai kuma naje gulma.” Yace.”To meye na gayyato zeey dole sai anje da ita.” Hafsa ta diririce! “Abban Afnan meye haka? Wallahi katari akayi Zeey tazo kai kanka ka san Zeey bata san Governor yayi aure ba, sai da tazo taji labari to meye a ciki dan taje gidan ai matar mutum kabarinsa wani baya auran matar wani hakanan wani baya auran mijin wani.” Ahamdu Yace.”Kinji mijinki naso ya tona miki asiri duk kin diririce to ai nagane komai.” Rantsuwa ta soma yi tana so ta fahimtar dashi ba haka bane….Zeey ta fito daga dakinta, Siririyar mace ce fara mai fadin fuska da manya manyan ido da hanci mai fad’i sai bakinta mai dan tudu dai-dai misali bata da wata cikakkiyar ‘kira ta matantaka! amma kuma kallo daya kayi mata zaka gane cewar wayayyar macece mai tarin ilimi da kagani kuma tana da shekaru ko kusa ko alama ba zaka hada shekarunta dana Wasila ba ta girme ta da kusan shekaru bakwai Wasila yanzu tana matakin shekaru 18 Yayin da Zeey ke da 26 Fuska a sake ta zauna kujerar dake fuskantarsa tana fadin”Ango ashe ana ganinku gaskiya Yallabai kayi wuyar gani ko a waya ba’a gaisawa.

Akwai kyakkyawar fahimtar juna a tsakaninsa da Zeey dan haka sai ya saki fuska kadan yana fad’in”Kece mai laifi ai da baki kirana a waya kin san al’amura da yawa sun sha kaina sai hakuri.”

Murmushi tayi tana mamakin maganarshi wai fadi yake bata kiran wayarshi abunda a rana sai ta kira sau goma yaki dauka gajiya tayi da wulakanci ta kama kanta amma saboda ya kare kanshi yake kokarin dora mata laifi….Cikin bagarar da maganarsa tace”Kawai dai ka fad’i hakane domin kaji dadin bakin ka amma sau nawa zan kira wayarka kayi dauka gashi zahiri tana shiga babu amsa..

Kare kansa ya hauyi tace”Governor kenan ashe kayi aure babu labari.”? Ya dan sosa kanshi still da murmushi kadan! wata iriyar kunyar ta ce ta kamashi amma dake namijin gaske ne sai ya basar yace.”Wallahi kuwa lokaci yayi kisan kuma dama haka lamarin aure yake idan Allah ya kawo shi bagatatan sai ayi.” Tace”Hakane to Ubangiji Allah ya sanya alkairi.” Yace.”Ameen nagode kwarai yanzu ki bani numbar ki sai nayi seving ko.” Ta kalleshi da mamaki tace”Au! kace ma baka da no dina.”

A wayance yace.”Kwanaki na bawa Garba Wayar ya rage min numbars na jama’a sunyi yawa ashe ya had’a da taki dalili kenan da ya sanya duk sanda kika kira bakya samun amsa akan lokaci.” Yafadi hakane dan ya kare kansa amma tun ranar da sukayi musayar numbar ita dashi yana futa ya goge numbarta a ganinsa sam bai ga amfanin ajiye numbar mace a wayarsa ba.

Zeey kuwa ta yarda da maganarsa dan haka da sauri ta soma fad’o masa numbar yana sanyawa a wayarsa yayi serving tare da fadin'” Kinga ma dunga gaisawa lokaci zuwa lokaci.” Zeey tace”Aikuwa dai kam.” Hafsa dake shirya abinci a dining tace”Governor yau fa mutuminka nayi ban sani ba ko zaka ci ko da yake amarya nasan kafin ka fito ta cika mata ciki da girkinta na amare.

Hararata yayi yace.”Wai kina nufin Towo ko me.”? Tasa dariya da fadin “d’ayan ne.” Yace.”Alkubus.”? Eh tafada tana murmushi….Yace.”Ai ko d’awisu ta bani sai naci ko da cikina zai fashe.” Duka suka kwashe masa da dariya Khalifa yace.” Ai na sani ko ka koshi sai kaci wannan abu ni ban san me kake ji a cikinsa ba fulawa kayan basir.” Mikewa yayi yana fad’in”Ballanta na ma ban koshi ba dan har yanzu ‘bacin rai ya hanani cin wani abincin kirki.” Sai da ya fadi maganar kuma ya dawo yana da ya sani ganin dukaninsu sun sha jinin jikinsu…..To dai babu wanda ya sake tado da maganar suka zauna a danning Hasfa ta zubawa kowa nashi….Ahamdu ya riga kowa cinyewa Ya sake zuba wani da kanshi Hasfa sai tsokanarsa take da fadin”Allah yasa santi yasa ya manta hularsa.

Sai bayan sun kammala cin abincin ne ya kalli Hafsa a nutse yace.”Wane guri ake miki d’inkunanki.”? Ta kalli Khalifa dake goge bakinsa da tissue! Khalifa yace.”Kana so ayi wa amarya kenan.”? Ina so dai in siya mata d’inkakku a gurin nasan ba za’a rasa ba.’ Khalifa yace.” Bari nayi wanka nazo muje Yakasai Gidan Murtala.” Yace.”Kayi da sauri yamma tayi.” Khalifa ya mike ya nufi daki Hafsa tabi bayansa domin hada masa ruwan wanka…..Ahamdu da Zeey suka shiga hira abunda ya shafi harkokin Siyasa da yanda talakawa me faman shan wuya a wannan gomnantin.

Khalifa ne yake draving shi kuma yana zaune a gefansa suna hira Khalifa yace.”Yanayin yanda ka shigo dazu ya sanya hankalina ya tashi to amma ganin ka sake kana hira dasu Hafsa yasa hankalina ya kwanta da har nayi tunanin ko kai da mutanan ne.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button